Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora: Siyasa ta dawo Gwamna Alu zai tuta yam.
Yara: Cali siyasa ta dawo,
Gwamna Alu zai tuta yam.
Jagora: Siyasa ta dawo
Gwamna Alu zai tuta yam.
Yara: Cali siyasa ta dawo,
Gwamna Alu zai tuta yam.
Jagora: Ya Allah Sarki
Allah,
Ya Allah kama ma Alu,
Yara: Shehu kaso ba musu
ba.
Jagora: Ya Allah Sarki
Allah,
Ya Allah kama ma Alu,
Yara: Shehu kaso ba musu
ba.
Jagora: Ina yin kiran
jama’ar birni,
Ina yin kiran jama’arƙ ƙauye,
Gwamna Alu zai tuta yam.
Jagora: Ina yin kiran
jama’ar birni,
Ina yin kiran jama’arƙ ƙauye,
Gwamna Alu zai tuta yam.
Yara: Shehu ka zakka ko
yaushe.
Jagora: Idam Buzu bai gwamna
Yara: Sai ya tsaya kallosh
shayi.
Jagora: Idam Buzu bai gwamna
Yara: Sai ya tsaya kallosh
shayi.
Jagora: Alu bai gasar kyan
aiki,
Ɗan Barade na jikan
Umar,
Ya ɗamara Baban,
Yara: Baban Bello.
Jagora: Alu bai gasar kyan
aiki,
Ɗan Barade na jikan
Umaru.
Yara: Yo ɗamara baban Bello.
Jagora: ‘Yan ta ɓare sun yo kunya,
Wai an ce sun ɗau boka,
Dun gurinsu a ka da Alu,
Yara: Ba su iyawa wa su
nan.
Jagora: ‘Yan ta ɓare sun yo kunya,
Wai an ce sun ɗau boka,
Dun gurinsu a ka da Alu,
Yara: Ba su iyawa wa su
nan.
Jagora: Boka da ɗan bori,
Wannan bai iya ka da Alu.
Yara: Sai da nufin yardar
Allah.
Jagora: Boka da ɗan bori,
Wannan bai iya ka da Alu.
Yara: Sai da nufin yardar
Allah.
Jagora: Ummaru Ɗan Ama na Alu,
Ya ba ni gida ya bani kuɗɗi,
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Ummaru Ɗan Ama na Alu,
Ya ba ni gida ya bani kuɗɗi,
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Ummaru Ɗan Ama na Alu,
Ya ba ni gida ya bani kuɗɗi,
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Salihu Barade babban
sarki na,
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Salihu Barade babban
sarki na,
Sannu masoyin gwamna Alu.
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Salihu Barade babban
sarki na,
Sannu masoyin gwamna Alu.
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Ahamed Barade ubana
na,
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Ahamed Barade ubana
na,
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Ina kai kai,
Yara: Cali siyasa ta dawo
gwamna Alu zai tuta yam.
Jagora: Ahamed Barade ubana
na,
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Mamman ɗan Cadi sadauki na.
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Shi ko ciyaman ne
Sabon Birni Ɗan Cadi nai min alheri.
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Sarkin baƙi Yawale ya kyauta.
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Sarkin baƙi Yawale ya kyauta.
Yara: Yanda yake mana ya
kyauta.
Jagora: Sardaunan Gobir
sanata,
Sannu masoyin gwamna Alu.
Jagora: Sardaunan Gobir
sanata,
Sannu masoyin gwamna Alu.
Jagora: Mu mun yi addu’a mun
kore gada,
Had da barewa -
Yara: mun harbe.
Jagora: Mu mun yi addu’a mun
kore gada,
Yara: Har da barewa mun
harbe.
Jagora: Ri ‘yan garda masu
abin kunya,
Na iske su gidan mata,
An sha giya an sha wiwi,
Yara: Har wasu na koyon
banjo.
Jagora: Ri ‘yan garda masu
abin kunya,
Na iske su gidan mata,
An sha giya an sha wiwi,
Yara: Har wasu na koyon
banjo.
Jagora: Alu bai gasar kyan
aiki,
Ɗan Barade na jikan
Umar.
Yara: Yo ɗamara Baban Bello.
Jagora: Angon Murja angon
Arziki,
Kai,
Yara: Yo ɗamara Baban Bello.
Jagora: Angon Arziki angon
Murja ne,
Yara: Yo ɗamara Baban Bello.
Jagora: Angon Arziki angon
Murja ne,
Yara: Yo ɗamara Baban Bello.
Jagora: Baban Hodiyo baban
Lamiɗi,
Kai,
Yara: Yo ɗamara baban Bello.
Jagora: Baban Hodiyo baban
Lamiɗi,
Kai,
Yara: Yo ɗamara baban Bello.
Jagora: Cali alƙawali na naɗ ɗauka,
Haƙ in dai gada zai
gwamna,
In dan fatin PDP,
Yara: Wanga karon da mun
bar shi.
Jagora: Cali alƙawali na naɗ ɗauka,
Haƙ in dai gada zai
gwamna,
In dan fatin PDP,
Yara: Wanga karon da mun
bar shi.
Jagora: ‘Yan ta-ɓare sun yo kunya,
Wai nan ce sun ɗau boka,
Don gurinsu a ka da Alu,
Yara: Ba su iyawa wa su
nan.
Jagora: Boka ko da ɗan bori,
Wannan bai iya ka da
Alu.
Yara: Sai da nufin yardar
Allah.
Jagora: Boka ko da ɗan bori,
Wannan bai iya ka da
Alu.
Yara: Sai da nufin yardar
Allah.
Jagora: Ummaru Ɗan Ama jigo,
Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.
Yara: Yanda yake min ya kyauta.
Jagora: Ummaru Ɗan Ama jigo,
Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.
Yara: Yanda yake min ya
kyauta.
Jagora: Salihu Barade babban
sarki na,
Sannu masoyin gwamna Alu.
Yara: Ya ba ni gida yab
ban kuɗɗi.
Jagora: Salihu Barade babban
sarki na,
Sannu masoyin gwamna Alu.
Yara: Ya ba ni gida yab
ban kuɗɗi.
Jagora: Na gode mai gida
haji Faruku,
Yara: Ya ba ni gida yab
ban kuɗɗi.
Jagora: Kwamishinan kuɗi nau dattijo Faruku
sannu,
Kai,
Yara: Ya ba ni gida yab
ban kuɗɗi.
Jagora: Kwamishinan kuɗi zaki Faruku yai min
alheri.
Yara: Ya ba ni gida yab
ban kuɗɗi.
Jagora: ‘Yan garda masu abin
kunya,
Na iske su gidan mata,
An sha giya an sha wiwi,
Yara: Ha wasu na koyon
banjo.
Canjin kiɗa da rauji
Jagora: Baba a bar maka yaƙi,
Aliyu sabon gwamna
Yara: Baba a bar maka yaƙi,
Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Baba a bar maka yaƙi,
Aliyu sabon gwamna
Yara: Baba a bar maka yaƙi,
Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Mu sabka Sakkwato
birni,
Saboda nau Ɗan Ama.
Yara: Tun da dai mun ka riƙe shi,
Ba mu kukan babu.
Jagora: Ga Cali ɗan Lajinge,
Cali ƙanin ɗan gwamna.
Yara: Mijin Zakiya Mamman,
A bar ka sarkin waƙa.
Jagora: Karen gida da ka ga
za ka far ma kurar daji,
Yara: Ka bar shi in sun ka
game ƙashin shi sai ya ɓazge.
Jagora: Mu sauka Sakkwato
birni,
Saboda nan Ɗan Ama.
Yara: Tun da dai mun ka riƙe shi,
Ba mu kukan babu.
Jagora: Baba masoyin gwamna,
Ummaru Ɗan Ama,
Kai,
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Madawakin jigo na
gwamna sarkin Yamma,
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Madawakin roƙo Umaru Ɗan Ama,
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Na ji ‘yan ta ɓare,
Wai a kan,
Sun ka ƙi noman rani,
Yara: Shekara ta tashi
Su sun riga sun watse.
Jagora: Na ji ‘yan ta ɓare,
Wai a kan a ba su muƙami,
Sun ka ƙi noman rani,
Yara: Shekara ta watse,
Su sun riga sun watse.
Jagora: Muna da ‘yan ga-aiki
cikinku nau ‘yan ta-ɓare,
Yara: Tun da ba a da
mulki,
A kama sabon izza.
Jagora: Na yaba maka giwa
Sahabi Isa Zaki.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Sakataren gwamnati
ne Sahabi ɗan Lattijo.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Na yaba maka fam sek
Aminu Dikko Sadauki.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Na yaba maka Bello,
Guiwa uban mai waƙa.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Sakkwatawa asuli ku
zo mu zaɓi Aliyu.
Yara: Ka bar su kowa ya
wuce,
Jagora: Mahassada su ji
habshi,
Aliyu shi ag gwamna.
Yara: Rabbana shi yac ce a
bar shi ko don dole.
Jagora: Baban Hodiyo zaki
Yara: Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Baban Hodiyo zaki
Yara: Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Baba uban Lamiɗo,
Yara: Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Baba uban Lamiɗo,
Yara: Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Angon Arziki jigo,
Yara: Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Baba angon Murja,
Yara: Aliyu sabon gwamna.
Jagora: Baba sabon sarki
Salihu ban ran mai ba.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Na yaba maka Walin
Gagi nau dattijo.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Na yaba maka Walin
Gagi nau dattijo.
Yara: Abin da yay ya kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Ga wasiƙa na yo a kai ma nau ɗan Ama,
Yara: Sai ya duba ta da
kyau,
Ya kai ta hannun gwamna.
Jagora: Ga wasiƙa na yo a kai ma nau ɗan Ama,
Yara: Sai ya duba ta da
kyau,
Ya kai ta hannun gwamna.
Jagora:Gwamna nai mishi
koke,
Tun da ba ni da mota,
Ban da kuɗɗin Mkka,
Yara: Ga gida da yawa a
gai da tsohon kwano.
Jagora: Sakatarenmu na kirki
Aminu Arɗo Sadauki,
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Sakatarenmu na
kirki,
Ibrahim nau Arɗo,
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Ibrahim ɗan Arɗo na zama na gaishe
ka,
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Gobirawa asuli ku zo
mu zaɓi Aliyu.
Yara: Ka bar su kowak
kauce wuya ta kai mai kaya.
Jagora: Ashe hukuma INEC ita ka yanke shari’a.
Yara: Sai ta yanke
hukunci,
Ta kore Arnan Togo.
Yara: Sai ta yanke
hukunci,
Ta kore Arnan Togo.
Jagora: Na ga masu adawa
wajen mu sun sha kaye.
Yara: Sun yi kwance ga
hanya kamat ɗiyar raƙumma.
Jagora: Na ga masu adawa
wajen mu sun sha kaye.
Yara: Sun yi kwance ga
hanya kamat ɗiyar raƙumma.
Jagora: Na yaba maka giwa
Faruƙu nau ɗan Yabo.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Na yaba maka giwa
Faruƙu nau ɗan Yabo.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Ɗan Cadi zo ka riƙe mu,
Ka gyara sabon birni.
Yara: Abin da kai mun ka
sani,
A bar ka sai ka kama.
Jagora: Mu sabka Sabon Birni,
Saboda Sarkin Baƙi.
Yara: Tun da dai mun ka riƙe shi,
Ba mu kukan babu.
Jagora: Shugaban PDP Yawale Sarkin Baƙi.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: ga sanata nan jigo
Sardauna mai,
Kai!
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Ga sana nan jigo,
Sardauna ban ran mar ba.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Na ga ‘yan ta-ɓare du wajenmu sun
sha kaye,
Yara: Sun yi kwance ga
hanya,
Kamar ɗiyar raƙumma.
Jagora: Shugaban ‘yan ta-ɓare,
Na ganai ya walga.
Yara:Mun ga yara ka jifan
shi,
Wai kare ya wubce.
Jagora: Shugaban mata ko,
Taƙar ƙashiya ta ɓare.
Yara: Wance ba a da kaya,
Duwai ga hilin Allah.
Jagora: Baba sabon sarki,
Salihu ban ran mai ba.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Baba Baraden Wamako,
Mai kgida kyauta,
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Baba Baraden Wamako,
Maigida na gode.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Arjika nau lattizo
Tireta,
Ban ran mai ba.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
Jagora: Arjika nau Lattizo
Tireta,
Nai mini rana.
Yara: Abin da yay ya
kyauta,
Saboda sabon gwamna.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.