𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam barka da warhaka, wani bawan Allah ne yake azumin Litinin da Alhamis, ga shi yana shiga hakkin matarsa wani lokachin, tayimishi magana amma ya ce shi ba zai daina ba so yake ya saba da azumin, komai zaifaru sai dai ya faru, malam azumin ko sauke hakkin matarsa? Allah ya kara daukaka mlm na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu, Tabbas yana daga cikin haƙƙoƙi na wajibi na ma'aurata a kan junansu
sauke wa juna haƙƙin aure ta ɓangaren
saduwa, kuma rashin cika wannan haƙƙin na iya sa ɗaya daga cikin ma'aurata ya kusanci saɓon Allah ta hanyar zina
musamman idan aka samu raunin imani, ko kuma hakan ya haifar da mutuwar aure ma
baki ɗaya.
Shi kuma yin
azumin Litinin da Alhamis sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah ﷺ, saboda haka ya sauke
wajibin iyalinsa a kansa shi ne a gaba a kan yin azumin nafila, saboda katange
matarsa ga aikata abin da bai dace ba, kamar yadda yake faɗin komai zai faru ya faru, wannan
magana tasa kuskure ne.
Saboda rashin
gamsar da juna a tsakanin ma'aurata kaɗai
na iya haifar da faruwar fitinar da ba za a iya shawo kanta a tsakaninsu ba in
ba ta wannan hanyar gamsarwar ba. Saboda haka sai ya rage yin azumin a kai a
kai ko da ba zai daina ba gaba ɗaya
tun da yana son koyi da sunnah, kuma ita kanta gamsar da iyali akwai lada a
cikinta, kamar yadda azumin taɗawwu'i
yake da lada.
Idan kuma ya ƙi ji,
to ta yi haƙuri
da shi a kan hakan, saboda kada matsawarta a gare shi ya haifar da wata fitina
a tsakaninsu, matuƙar dai ba kusantarta ne ba ya yi baki ɗaya ba.
Allah ne mafi
sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.✍🏻
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.