Idan miji ya sha nono matarsa ya matsayin aurensu?

    Duk namijin da ya tsotsi nonon matarsa har ruwa ya fito yasha wannan ruwan nonon, ko tana shayarwa ko ba ta shayarwa tananan a matsayin matarsa.

     A indai aure yake haramta a tsakani shi ne, idan mace ɗaya ta shayar da shi yana jariri a lokacin daba ya buƙatar wani abinci sai nono,ba ya iya cin komai sai nono, to idan ya zama matar data shayar da shi ita ce ta shayar da matarsa, to anan aure ya haramta a tsakaninsu.

     Amma mutuƙar ya girma yana cin abinci, yana yin komai da kansa, yana yawo a gari, to anan duk nonon matar da yasha a wannan hali '‘yarta ta halatta ya aure ta, amma indai yana jariri ne ta shayar dashi, to anan ne take haramta a gareshi.

     Don haka duk wanda yake kan fahimtar cewa ai idan miji yasha ruwan nonon matarsa babu aure a tsakaninsu, wannan ba gaskiya ba ne.

    ALLAH TA'ALAH kasa mudace.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.