Article Citation: Yankara, M. M. and Sifawa, H. S. (2018). Jigon Tarbiyya Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi. Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, 2 (1). Department of Nigerian Languages. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University. P 161-176.
Jigon Tarbiyya A Wasu Waƙoƙin
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi
DAGA
Muhammad
Musa Yankara
Department
of Registry,
Fedaral
University Dutsin-Ma, Katsina.
esemwaiy12@gmail.com
Da
Hadiza Salman Sifawa
Department
of Languages,
Shehu
Shagari College of Education, Sokoto.
dijeskk17@gmail.com
Tsakure
Tarbiyya
kyakkyawar hanyar rayuwa ce da ake gina mutum kanta tun yana yaro. Tun a
yarinta alamu ke fara bayyana na kyakkyawar tarbiyya ko akasin haka. Ita alama
cikin kowane abu tana da muhimmanci. Sai ta bayyana sannan haƙiƙanin
al’amari yake zuwa, Bunza (2016). Wannan maƙala za ta yi tsokaci
ne a kan yadda Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi ya yi amfani da hikima da basira
da kuma dabaru a cikin waqarsa domin, tarbiyyantar da al’umma a kan rayuwa ta ƙwarai
wadda kowa zai yi na’am da ita. Takardar za ta yi ƙoƙari ne
wajen zaƙulo dukkan ɓangarori na rayuwa da ya shafi tarbiyya wanda ya zo a
cikin waƙoƙin marubucin.
1.0
Gabatarwa
Waƙa muhimmin rukuni ne na adabi da ta cancanci a yi mata kirari da “Nagge daɗi goma”. Dalili kuwa shi ne, a kowane harshe na duniya waƙa ita ce kan gaba wajen
bunƙasa da ɗaukakar adabin wannan harshe, domin
ita ta nashe dukkan sassa na rayuwar al’ummar da ke magana da harshen. Waƙa takan yi ruwa da tsaki
kusan a kowane fanni na rayuwar al’umma. Ana iya gyara al’umma ta zama masu
kyawawan halaye da ita, ko kuma a gurɓata ta da ita; ana iya tunzura mutane ko a zuga su zuwa ga fusata ko kuma a
kwantar masu da hankali da ita; ana iya ba su ilimi cikin sauƙi har su gwanance ko
kuma a jawo hankalinsu zuwa ga muhimmin abu, a wayar musu da kai da ita; ana ƙwarzanta abu komin ƙanƙantarsa ko a ƙara masa gishiri ko a kushe shi a
wulaƙanta shi da ita. Waƙa tana da asirin tilasta a yarda ko a amince da abu komai muninsa da ƙazantarsa ko cutarwarsa,
kamar yadda take halasta a ƙyamaci abu duk kyawunsa da amfaninsa ko muhimmancinsa.
Dukkan waɗannan darajojin baiwa ce da Allah ya
hore wa mawaƙa domin bayar da gudummuwarsu ga al’umma tare da cin karensu ba babbaka
wajen sarrafa kalmomin harshensu da gwanancewarsu yadda suke so.
Bahaushe kamar yadda sauran mutane suke, tun tale-tale mutum ne da bai iya
zama sai da tarbiyya. Tarbiyyar nan kuwa ta jikinsa ce ko ta ruhinsa, wato
rayuwarsa. Saboda haka, ba zai taɓa zama lafiya ba sai da tarbiyya, ta ƙashin kansa da ta iyalinsa da kuma jama’ar da yake rayuwa
da su. Irin hakan ne ya sa tun kafin Bahaushe ya iya karatu da rubutu Allah ya
yi masa baiwar hikimomi da dabaru na yi wa kansa, da ‘ya’yansa da sauran
al’ummar da yake zama cikinta tarbiyya.
Daga cikin ire-iren waɗannan hanyoyi na tarbiyyar Bahaushe a gargajiyance, akwai tatsuniyoyi da waƙoƙin yara na mata da na maza. Lokacin
da ya samu ilimi, sai ya ƙara samun wasu dabaru na yin tarbiyya ta hanyar rubutu
wanda ya kai ga yana bayar da ita a litattafai, har ma aka samu rubutattun waƙoƙin Hausa su ma suka fara taka tasu
rawar a wannan fagen duk da cewa dai ba su yawaita ba.
Tsinkayar tarbiyya a irin waɗannan rubutattun waƙoƙin ne ya sa wannan takarda yin kutse cikin diwanin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi,
domin zaƙulo da fito da jigon don amfanuwar al’umma.
2.0
Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi
An haifi Alhaji Ɗahiru Musa Jahun, a
cikin shekarar 1942 a unguwar Jahun da ke cikin garin Bauchi. Bayan ya sauke Alƙur’ani da shekara
takwas a makarantar Allo ta Malam Maigari, sai babban yayansa Liman Muhammadu
Inuwa, wanda a hannunsa ya taso tun haihuwarsa kasancewar mahaifinsu ya rasu,
ya tura shi Gombe domin ƙaro ilimi da sanin Alƙur’ani sosai. Alhaji Ɗahiru ya karanci litattafan addinin Musulunci da suka haɗa da Iziyya da Risala da Alburda, da kuma Ishiriniya a
wajen Malam Aminu Murshidi a garin Gombe.
Sakamakon gidansu Alhaji Ɗahiru Musa Jahun duk malaman addini ne, sai ya zama bai
samu damar xanxanar zaƙin karatun boko ba, duk da sha’awa da ƙaunar da ya nuna gare shi domin
kuwa, sai da ya taɓa saka kansa a furamare, bayan da aka gane yana zuwa ne aka fitar da shi.
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya yi sana’o’i da dama bayan kammala karatunsa na addini
da ya haɗa da ɗinki, da gini, da kuma gyaran keke. Sannan a lokaci ɗaya kuma yana koyon rubutun Hausa ta hanyar yaƙi da jahilci wanda da
haka ya fara rubuta waƙoƙinsa.
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya fara rubuta waƙoƙi ne tun yana ɗan shekara sha uku, a in da samari da ‘yan mata ke taruwa shi kuma yana
rera masu suna saurare. Ya rubuta waƙoƙi masu tarin yawa a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma, kamar siyasa,
haɗin kai, bukukuwa, sarauta, da kuma
tarbiyya. Sai dai waƙoƙin da suka fi fito da shi, su ne waɗanda ya ke yi domin, tarbiyyantar da jama’a. Haka kuma ya samu lambar yabo
da jinjina a wurin mutane daban-daban, kamar irinsu Sarkin Bauchi Alhaji
Sulaimanu Adamu, da kuma lambar yabo ta qasa-da-qasa da aka ba shi lokacin
mulkin Shugaban Ƙasar Najeriya Olusegun Obasanjo.
Ya zuwa yanzu, Alhaji Ɗahiru Musa Jahun yana nan da rayuwarsa, zaune a Unguwar
Jahun Layin Liman Mai rasuwa Bauchi, da kimanin shekaru 75 a duniya, kuma yana
da mata 4 da ‘ya’ya 42 tare da jikoki masu yawa. Sannan har yanzu yana rubuta
waƙoƙin tarbiyya da kuma waɗanda suka shafi rayuwar jama’a ta fuskoki daban-daban.
3.0
Ma’anar
Tarbiyya
Kalmar tarbiyya abu ce wadda ta sha luguden ma’anoni daga bakunan masana da
manazarta. Daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar Kalmar akwai, Gusau
(1999) da yake kallon tarbiyya a matsayin “wata hanya ce ta kyautata rayuwar ɗan Adam da shigar da shi ya zuwa halaye da ɗabi’u masu kyau da nagarta. Ta yin haka zai sa ya tashi
da ƙima da ƙwarjini da ganin mutuncin abokan zamansa, sannan ya riƙa ba kowa haqqinsa daidai yadda ya
kamata gwargwadon hali.
Yahya (2001) cewa ya yi “tarbiya kalma ce wadda Bahaushe ya aro daga
Larabci kaitsaye watau kamar yadda take ba tare da wata sakayawa ba, wadda kuma
ta Hausa gangariya take da ma’anar ‘reno’, domin wanda ake yi wa shi samu
dukkan halaye da ɗabi’un da mai yin renon yake son
gani.
Bunza (2002) ya tafi a kan cewa ‘tarbiyya tana nufin samun kyakkyawan horo
ga mutum ya zama masanin kyawun abubuwa na ɗabi’un hulɗa da jama’a da ladabi, da biyayya, da kamun kai, da kasancewa mai jin kunya
da kyakkyawan maƙasudi.
Tarbiyya ita ce koyar da hali nagari (CNH 2006).
Shehu (2011) ya tafi a kan cewa tarbiyya na nufin “aza wani mutum bisa wata
hanya da zai koyi wani abu wanda zai amfane shi a rayuwarsa da ma sauran
jama’arsa baki ɗaya.
Tarbiya ta shafi gina mutum a bisa halayen da al’ummarsa ta aminta da su na
kunya da ƙwazo da ladabi da biyayya da girmama na gaba da kishin kai da riƙe iyali da taimakon juna
da haɗin kai da son aikata alheri da
nisantar kwaɗayi da rowa da sauransu (Bunza
2012).
Ita kuwa Bugaje (2013) cewa ta yi, “tarbiyya ta kasance ma’aunin gane
darajar mutum da al’ummar da ya fito domin, haka ana tarbiyya da nufin a sami
al’umma tagari, nagartatta.
Bunza (2016) ya ce “tarbiyya hanya ce ta gina yaro don kasancewarsa mutum
nagari a lokacin kammalar tunaninsa da hankalinsa. Wannan zai sa ya ja linzamin
rayuwarsa da na makusantansa a hanya madaidaiciya, ya amfani kansa a kuma
amfana da shi.
Ta la’akari da ma’anoni na tarbiyya da masana da manzarta suka kawo a sama,
nake ganin tarbiyya a matsayin dabarar gina rayuwa mai inganci don samun dukkan
halayen kamalar mutuntaka da ɗabi’un dattaku domin, kasancewa abin yabawa da sambarka.
3.1
Jigon Tarbiyya a Cikin Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun
Tarbiyya wani babban jigo ne ga rayuwar Bahaushe wanda idan babu tsarin
tarbiyya a rayuwa lallai mutum zai kasance tamkar dabba, kuma abin ƙyama wanda sauran jama’a
ba za su so yin mu’amala da shi cikin kowane sha’ani ba.
Kasancewar mutum mai kammalalliyar tarbiyya, dole ne ya zama mai kunya, da
gaskiya, da riƙon amana, da haƙuri, da tausayi, da kare mutuncin kai, da kishi, da neman ilimi, da abokai
nagari, da haɗin kai, da taimakon mabuƙata, da tsafta, da ƙana’a, da tawali’u da
kuma neman na kai da biyayya ko ɗa’a ga magabata da sauransu. Ire-iren waɗannan abubuwa kuwa, koyar da su ake yi domin, ganin an
samar da mutum nagari a cikin al’umma tun yana ƙarami har zuwa girma. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun gwani
ne wajen tsara waƙoƙin da suka shafi gina tarbiyya tsantsa, wanda waƙoƙin nasa suna tattare da ire-iren waɗannan halaye da ake buƙatar gani a wurin mutanen kirki
kamar yadda misalai za su nuna.
3.1.1
Gaskiya
Makaɗa Kassu Zurmi ya yi
wa gaskiya take da cewa, “Gaskiya mugunyar magana, ba a sonki sai kin tsufa”.
Abin da wannan makaɗi ke nufi bai wuce
zancen nan na masu hikima ba da suke cewa, “Gaskiya ɗaci gareta”. Wato ita gaskiya ba ta da daɗi a lokacin da aka ji ta sai bayan an aikata ta sai a ji daɗi.
Mustapha, (2003:56-7) ya zayyano ma’anar gaskiya daga bakin masana kamar
haka:
Yin abin da ya kamata ba tare da ƙari ko ragi ba, (Gusau 1984).
Gaskiya ita ce, aikata wani aiki ko furta wata magana da al’umma suka
aminta da kasancewarsa gaskiya. Haka kuma, wannan aiki ko maganar ya kasance
abu ne tabbatacce ga idon Bahaushe a ma’aunin al’adarsa, kuma ya zamo abu ne
mai ɗorewa ba mai gushewa ba, domin a daɗe ana yi sai gaskiya, (Bunza 2002).
Gaskiya shi ne faɗin daidai a cikin tunanin ɗan Adam da aikata daidai a cikin harkokinsa, tare da neman gano ko rarrabe
abin da ke tsakanin tunanin ɗan Adam da dabba, ko a da lokacin zaman gargajiya, ko a yanzu da addinin Musulunci
tare da sauyawar zamani ta zo, (Mu’azu (…..)).
Bisa lura da abin da masana suka ambata dangane da gaskiya, za a iya cewa;
Gaskiya shi ne faɗin abu yadda yake, ko ba da labari
bisa tabbaci da haƙiƙa ba tare da shakka ko kokwanto ba.
Yin gaskiya ta kowace hanya abu ne mai kyau da amfani ga mutane a tsarin
zamantakewa. Dangane da haka ne Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya duƙufa wajen ganin ya ɗora al’umma a kan turbar gaskiya, da faɗinta da kuma aikata ta komai ɗaci da wahalarta a tsarin rayuwa. Ga misalai a cikin wasu
waƙoƙinsa kamar haka:
‘Yan kasuwa a yi ƙoƙari,
A yi gaskiya a yi hanƙuri,
Kwana da wayunwan gari,
Wataran
buƙata zai biya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya
II)
Jama’a a bar yin maguɗi,
A yi
gaskiya a yi tarbiya.
Ku ɗalibai in gaya muku,
Ko ko in ƙara tuna muku,
Komai izan ya
matsa muku,
Ku faɗi ta hanyar gaskiya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya
III)
9. Gyara kayanka domin sanin haƙƙi,
Mai riƙon gaskiya bai shiga
kunya.
(Ɗahiru Jahun:Gyara
Kayanka Bakandamiya)
Misalan da wannan
marubuci ya kawo na koyar da tsayawa tsayin daka ne a kan gaskiya. Wato duk
abin da mutum zai yi, to ya yi ƙoƙarin ganin ya yi
gaskiya ya kiyayi maguɗi da mugunta a
cikinsa domin, mai gaskiya bai shan kunya. Haka kuma duk abin da mutum zai faɗa, to ya yi ƙoƙari a ji gaskiya ce ta fito daga bakinsa.
3.1.2
Riƙon
Amana
Ita dai kalmar amana asalinta daga harshen Larabci take. Hausawa suka aro
ta suna amfani da ita kamar yadda take a cikin harshen Larabci. Kalmar tana
nufin aminci, wato yarda. Yarda kuwa na iya kasancewa a kan kowace irin hulɗa da ake iya samu a tsakanin mutune. Wannan shi ya sa
mutumin da ba ya da riƙon amana wato ba yardadde ba, yake kasancewa abin ƙyama a cikin al’umma.
Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar amana a
Hausa, daga cikin waɗannan masana akwai Bargery (1934:27), wanda ya bayyana ma’anar amana a
matsayin kyakkyawar fahimta ko yarjewa mutum a kan wani abu. Haka kuma, ya ƙara da cewa amana na iya
ɗaukar ma’anar dogara da ban gaskiya
a kan abu.
Newman, (1997:289) an bayar da ma’anar amana da amincewa da yarda da mutum.
A cikin Ƙamusun Hausa (2006:15) an bayyana amana da ba mutum ajiyar kaya ko wani abu
yadda zai adana shi kamar nasa ba tare da wani abu ya salwanta ko wani abu ya
same shi ba.
A Hausance, Amana na nufin mutum ya kula da wani abu da aka damƙa masa kada ya bari ya
lalace ko ya salwanta, (Ibrahim, 2013:186). Idan ya kasance mutum mai amana ne
to al’amuransa sukan yi kyau. Idan aka ci amana kuma a sami akasi.
Buƙatuwar gina al’umma bisa tarbiyyar riƙon amana tasa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun a cikin waqoqinsa
ke cewa;
Kuma sai mu gaida
ma’aikata,
Wasu na shiga
wasu na fita
Dukkanku ƙwan ku da kwarkwata,
Ku riƙe
amanan gaskiya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya
II)
58. Gyara kayanka duk wanda ke aiki,
An fi
son mai amana da tarbiyya.
(Ɗahiru Jahun:Gyara
Kayanka Bakandamiya)
Waɗannan baitoci na
Alhaji Ɗahiru na nuna cewa a cikin al’umma ba wanda aka fi so
kamar mai riƙon amana, mai gaskiya. Don haka ya ke kiran mutane a kan
riƙon
amana cikin dukkan ayyukansu da suka sa gaba.
3.1.3
Kunya da Kawaici
Kunya kamar yadda
Yahya da wasu (1992:82) suka bayyana “ta ƙunshi hana harshe yin
munanan maganganu da ƙiya wa gaɓɓan jikin mutum aikata miyagun ayyuka.
A wata ma’anar kuma,
Balbasatu (2009:62) cewa ta yi, “Kunya na nufin jin nauyi da girmamawa ko
karamcin da ake yi wa wani na gaba da mutum ko masoyi ko ‘ya’ya ko surukai ko
baƙo.
Kunya na nufin halin ɗa’a da kawaici ko a aikace ko a magance. Kunya ɗabi’a ce kyakkyawa da kan jawo wa mai ita daraja da
girmamawa a cikin mutane, (Garba 2010:20).
Kunya tana matuƙar taka rawa wajen nuna zurfin kamala da halayen ƙwarai na mutum domin, siffa ce daga
cikin siffofin da ake gane mutum mai tarbiyya. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun a ƙoƙarinsa na tarbiyyantar da al’umma
yin kunya, ya kawo baitoci masu nuni da kyawun kunya ga mutum a cikin waƙoƙinsa kamar haka:
Suturar jikinki
ta yalwata,
Surar jikinmu ya ɗan ɓata,
Da wuya ace an
kunyata,
In an bi hanyar
gaskiya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya
II)
Tsiraici abu ne da
ake buƙatar ɓoyewa. Duk mutum mai hankali da
kunya ba zai so ya bayyanar da tsiraicinsa ba. Illar bayyanar da tsiraici ga
mata ne baitukan Sha’irin ke ƙoƙarin nunawa da cewa, duk mace mai kunya ba za ta bar jikinta a buɗe ba kamar moɗar randar bakin kasuwa. A cikin wani baitin kuwa cewa yake:
49. ‘Yan acaɓa ku inganta halinku,
Mai biɗar arziƙi bai rashin kunya.
51. Don waɗansunku kan sa a zarge ku,
Ga rashin hankali ga rashin kunya.
53. Masu tuƙi na mota waɗansun su,
Kan gwada ba
mutunci bare kunya.
85. Gyara kaya
tuni ne ga matanmu,
Kar a faɗa tafarkin rashin kunya.
(Ɗahiru Jahun: Gyara
kayanka: Bakandamiya)
Wato muddin ana son
inganta sana’a dole sai an haɗa da kunya domin, rashin kunya na jawo zargi da tsana a
wajen jama’a. Har ila yau marubucin ya sake bayyana yadda ake son mutum ya
kasance mai kunya a cikin sana’arsa a cikin baitin da ya ke cewa:
Amma gyaran da za
ku soma,
Farko ku rage
yawan zalama,
Ko buɗe ido da nuna tsama,
Tsiwa da tsuma da
nuna tsama,
Da tsageranci cikin
mutane.
(Ɗahiru Jahun: Sana’ar
Acaɓa).
3.1.4
Haƙuri
Hausawa na cewa “mai haƙuri yakan dafa dutse har ya sha romonsa”. Haƙuri kamar yadda Adamawa
(2007) ya bayyana, shi ne juriya ko shanye wani abu na ɓacin rai ko na rashin daɗi, wato haƙuri da ƙin maida martani don haifar da maslaha. Haƙuri yana yalwata zuciya
da janyo soyayyar mutane, kuma yana hana yin nadama. Shi yasa ma Hausawa suka
ce “Haƙuri maganin zaman duniya” domin, duk wanda ya laƙanci yin haƙuri to ya sami kyakkyawar shaida a
rayuwa. Masu haƙuri su ke tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a gida da gari da kuma al’umma
baki ɗaya.
Tarbiyya tana ingantuwa ne da haƙuri, wanda hakan yasa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya ke kwaɓar jama’a don tarbiyyantar da su haƙuri a cikin waƙoƙinsa kamar haka:
To dole sai mu yi yunƙuri,
Mu yi dauriya mu yi ƙoƙari,
Haɗa kanmu ƙauye ko gari,
Da nufin a maido tarbiyya.
To ‘yan uwa mu yi ƙoƙari,
Mu yi dauriya mu yi hanƙuri,
A ƙasarmu daji ko gari,
Kowa ya yarda da tarbiyya.
To ‘yan uwa mu yi ƙoƙari,
Mu yi dauriya mu yi hanƙuri,
Mu yi maganin
mutakabiri,
Daga nesa ba shi da tarbiyya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)
Haƙuri a kan dukkan wani abu da mutum yasa gaba na rayuwa shi Sha’irin ke ƙoƙarin nunawa a cikin waɗannan baitoci. Sha’irin na nuna komai mutum zai yi to
dole sai ya yi haƙuri a cikinsa matuƙar yana son cimma muradi. Haka kuma ya nuna ba a samun nasara a zamantakewa
sai da haƙuri.
3.1.5
Wadatar Zuci
Wadatar zuci shi ne
akasin kwaɗayi, rashin ƙwallafa rai kan samu
ko mallakar abin da wani ya mallaka na rayuwar duniya. Wato gamsuwa da abin da
ka mallaka komai ƙarancinsa, da rashin damuwa da abin da wasu suka mallaka
komai yawansa shi ne wadatar zuci.
Wadatar zuci wani
muhimmin makami ne na kyautata tarbiyyar al’umma. A duk lokacin da mutane suka
kasance masu wadatar zuci, to sai kishin kai ya shige su, su zama ba su
hassadar abin da ke hannun wani. Dukkan mutumin da Allah ya ba wadatar zuci, ya
yi dace domin zai zama mai natsuwa da kwanciyar rai a koyaushe. Haka a duk lokacin da wadatar zuci ya bazu a zukatan jama’a, to lumana da
zaman lafiya za su samu a tsakaninsu. Haka lalaci irin na sace-sace da ƙyashi da jiye wa juna za
su ragu sosai in har ma ba su gushe ba gaba ɗaya. (Bunza, 2012).
A koyaushe a cikin al’umma a kan samu wasu jama’a da ke yin iya ƙoƙarinsu domin faɗakar da mutane su zama masu wadatar zuci dangane da abin
da Allah ya hore musu domin kauce wa faɗawa a wata muguwar hanyar da za ta ɓata tarbiyyarsu, ta fitar da su daga gurbin mutane na gari.
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya ƙoƙarta wajen tarbiyyantar da al’umma wadatar zuci a cikin waƙoƙinsa, kamar yadda ya ke cewa:
Najeriyanmu ƙasa ɗaya,
Kuma ga mu
al’umma ɗaya,
Jama’a a bar son zuciya,
Ɗa’a ta samu da tarbiyya.
Jama’a a nai mana
gargaɗi,
Mu rage azabar son kuɗi,
Wasu na ta
haddasa maguɗi,
Sunansu ba su da tarbiya.
Ku saya ku saida halaliya,
Riba kaɗan mu yi godiya,
Duka sun ƙi gwamma haramiya,
Ba sa da ɗa’a tarbiya.
Ba wai ka mallaki naka ba,
Ka fito ka handami namu ba,
Baka san kana kashe kan ka ba,
Don
son gwanintan duniya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya
II)
Son zuciya kan haifar da maguɗi da hassada da handama da son duniya. Duba ga wannan da
hanin jama’a kan yin su shi ne Sha’irin ya ke kiran jama’a a kansu cikin
baitukan da suka gabata.
A cikin wata waƙar kuwa ga abin da yake cewa dangane da tallar da iyaye
ke ɗorawa yara domin neman abin duniya:
Wasu gun talla ɗa’a takan rushe,
Har su koyo ɗabi’un rashin kunya.
(Ɗahiru Jahun: Gyara
kayanka Bakandamiya).
Rashin
haƙurin
wasu iyaye kan jefa yara cikin miyagun ɗabi’un da ƙarshe za a zo ana
da-na-sani wanda da sun sami wadatar zuciya da hakan bai faru da ‘ya’yansu ba
kamar yadda baitocin waƙar ke nuni. Har wayau marubucin ya sake cewa:
7. shirin gyara kayanka ne ke faɗi,
Musamman a azure
na yin gargaɗi,
A taso a barci a
bar gyangyaɗi,
A yaƙi dukkan ayyukan maguɗi,
Na masu zalama da
yunwar kuɗi,
Misali ta manya
da ‘yan burbuɗi,
Na sa yara talla
farautar kuɗi,
Ka gansu a lungu
cikin turbuɗi,
Da ɗai ba karatu bare
tarbiyya.
(Ɗahiru Jahun: Ceton
‘yar talla)
Idan aka dubi waɗannan misalai za a ga
cewa babban saƙon da waqar take ƙarfafawa shi ne, mutum
ya zama mai wadatar zuci watau ƙana’a. Haƙuri da kaɗan shi ne babbar
nasara da nuna godiyar Allah, in kuwa aka ce sai an samu mai yawa to take-yanke
za a faɗa cikin haramiya da
kuma ɓarnar da ba ta da
makari.
3.1.6
Zumunta
Ƙoƙarin kusantar ‘yan
uwa da abokan arziƙi, da ziyartarsu a kai a kai, da riƙe dangi ba tare da zaɓunta ko son kai ba,
wannan ita ce zumunta. (Zarruƙ da wasu, 1988). Tarbiyyar Hausa tana
jaddada ziyarce-ziyarce tsakanin ‘yan uwa da abokan arziƙi. Har ma Hausawa
suna cewa “Zumunta a ƙafa take”. A cikin kowace irin
al’umma ana alfahari da mutum mai sa da zumunci. Wannan tasa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun domin ƙarfafar zumunta a waƙarsa ta Tarbiyya II ya
ke cewa:
Son ‘yan uwa shi ne
gaba,
Ka so shi ba zai ƙi ka ba,
Ba ka nuna ka so
kanka ba,
Zai sa a zauna lafiya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)
Wato dai abin da Sha’irin yake nuna wa mutane a wannan baiti shi ne, su yi ƙoƙari su riƙe ‘yan uwansu domin, shi ne gaba ga
komai da ke wanzar da zaman lafiya da son juna.
3.1.7
Kare mutumcin kai
‘Tsira da mutumci ya fi tsira da kaya’ inji masu hikimar zance. Sanin
darajar kai da tsare kai da kuma tsare mutuncin sauran mutane yana daga cikin
mutunci, musamman idan aka darajantasu saboda shekarunsu ko ilminsu ko kuma
saboda kasancewar su mutane na ƙwarai. Mutunci shi ne mutum ya ji kunyar aikata duk wani
abin da zai zubar masa da darajarsa. Mutunci shi ne mutum ya saba wa kansa da
kiyaye halaye mafiya kyau da cika. Wato kada ka aikata wulaƙantaccen abu. Kada ka
nuna halin ƙasƙanci wanda zai rage darajarka ka zama ba ka da girma wurin ‘ya’uwa
(Abubakar 1966:21).
Mutunci abu ne mai kyau da kusan kowane mutum yake maraba da shi domin,
yana taimaka wa zaman lafiya ya tabbata, tare da ɗaukaka darajar al’umma kamar yadda tufafi kan suturta
mutum, abinci kan kyautata lafiyar jiki a sami kuzari. Mutunci yakan ƙarfafi darajar mutum da
kuma al’umma baki ɗaya. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun yana faxakar da al’umma dangane da kare mutuncin kai da
sanin daraja da ƙima a cikin waƙoƙinsa. Misali
Dama mutunci ne
mutun,
In ba mutunci ba
mutun,
Mai hankali ka riƙe batun,
Ladabi da ɗa’a tarbiya.
Bari nuna kai ɗan wane ne,
Ko don ace kai wane ne,
Kowanmu ai ɗan wane ne,
Don
kar ka ja mana tankiya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya
II)
Har
wayau, a wani wuri Marubucin a cikin waqar Gyara Kayanka yana cewa;
12. Gyara kayanka domin gudun sharri,
Duniya
lahira kar a sha kunya.
22. Gyara kayanka kan malam ilmu,
Kar a
koya wa yara rashin kunya.
23. lakcaran
Jami’a ko mu ce tica,
Mun yi fatan a inganta tarbiyya.
24. Don sifofi ɗabi’un waɗansun ku,
Kan gwada ba su daidai
da tarbiyya.
25. Tun da yara
sukan ɗau sifar malam,
Bar fitowa da siffar rashin kunya.
(Ɗahiru Jahun: Gyara kayanka Bakandamiya)
Da jin waɗannan kalamai na cikin baitocin
wannan waqa za a fahimci cewa kashedi ne ake yi wa mutum ko hannunka mai sanda
game da irin yadda ake so duk abin da zai yi, to ya yi ƙoƙarin kare mutumcinsa. Kar ya aikata
abin da za a zarge shi domin, mutunci Hausawa sun ce “madara ne”. an kuwa yi
amanna cewa madara idan ta zube ƙasa to ba kwasuwa take yi ba.
3.1.8
Haɗin kai da Zama tare
Hausawa sukan ce, “Mutum na mutane ne”. watau mutum in dai mai lafiya ne,
to ya kamata a san shi tare da mutane, ba a ga yana janye jiki yana zama shi kaɗai ba. Da zarar aka samu jituwa a cikin al’amari, to za a
tarar da komai na tafiya salin-alin ba kace-nace a cikin al’umma. Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun suna tarbiyyantar
da jama’a muhimmancin haɗin kai, kamar yadda wasu misali za su nuna, in da marubucin ke cewa:
Ya ‘yan
ƙasan
nan ‘yan uwa,
Mu haɗe mu yarda da ‘yan uwa,
Mu zama muna son ‘yan uwa,
Mu haɗe mu gyara Najeriya.
Zancen ƙabilanci kuwa,
Mai yinta zai shiga damuwa,
Shi zai ci kansa ya sha ruwa,
Mun gane ba shi da
tarbiya.
Kai mai ƙabilanci bari,
Ko nuna bambancin gari,
Mu dai muna maka shawari,
Ka zama mutum mai
tarbiya.
Muddin ba mu haɗa kanmu ba,
Ba za mu kai burinmu ba,
Ra’ayinmu in ya rarraba,
Zai rarraba mana
tarbiya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)
Ta lura da lafazin wannan Sha’ira, za a ga cewa ba qaramin
fa’ida ke akwai ba na haxin kai. Don kuwa zaman lafiya ba zai tava wanzuwa ba
idan har akwai rashin jituwa tsakanin al’ummar da ke rayuwa a wuri xaya, kuma
ita kanta qasa ba yadda za ayi ta ci gaba, ballantana har jama’ar qasar su more
amfaninta matuqar babu haxin kai da zaman lafiya tsakaninsu.
3.1.9
Tsafta
Cikakkiyar kula ga jiki, da tufafi, da wurin
zama, da duk wani abin mu’amala mai alaƙa da mutum, ta hanyar
gyara shi, da inganta shi da tsaftace shi zuwa ga mafi dacewar kama ko yanayin
da ya fi ƙayatarwa da jan hankali, shi ne tsafta.
Ban da kasancewar
tsafta cikon addini, takan jawo farin jini da ƙauna ga jama’a.
Mutane kan yi na’am da maraba da mai tsafta, sannan takan sa masa farin jini da
duk wani abu da ya dangance shi. Hakan yasa masana da
manazarta suka duƙufa wajen tsawatarwa game da tarbiyyar tsafta. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun na sahun gaba wajen
ba da gudummuwarsa ta fuskar waƙa don kula da tsafta, kamar yadda misalan wasu daga cikin
baitocin waƙoƙinsa ke nunawa kamar haka;
73. Tsaftace zuciya tsaftace aiki,
Gyara kayanka inganta tarbiyya.
75. Gyara kayanka
tsafta cikin Ofis,
Har gidaje da gona da kan hanya.
(Ɗahiru Jahun: Gyara kayanka Bakandamiya)
Da farko ya nusar da mutane ne dangane da tsaftace niyya
a cikin kowane irin aiki da mutum zai yi. Ma-da-mar ba a samu kyakkyawar niyya
a cikin kowane irin aiki ba, to lallai za a iya fuskantar gajiyawa. Sannan kuma
sai kiyaye ko kula da tsaftar jiki, da abinci da muhalli.
6. ‘Yan karkara ƙauye ko birane,
Samun rashin tsafta
kuskure ne,
To gyara kayanka kar ka manta.
10. To gyara kayanka
sai a lura,
Tsaftar jiki ɗaki ko ta shara,
Sai masu Imani ke kula
ta.
12. To gyara kayanka
don kulawa,
Kan wanda ke tsafta sai daɗawa,
Domin rashin tsafta ba a son ta.
13. Tsaftar jiki ita
kam zahirun ne,
Farkon shirin tsafta
ya mutane,
Kowa ya ɗau tsafta can zukata.
39. Kowa da sunansa ya mutane,
To ko cikin ƙauye ko birane,
Sunan marar tsafta mai ƙazanta.
(Ɗahiru Jahun: Tsaftar Muhalli da Kewaye)
Wannan Sha’iri ya tavo wasu muhimman sassa da tsaftar xan Adam ya kamata ta
taka rawa a cikinsu, wanda ya haxa da jiki, da muhalli ko mazauni. Abin da
Sha’irin ke qoqarin nunawa shi ne, matuqar ana son lafiya ta wanzu a cikin al’umma
a daina cututtuka, to wajibi ne sai an kula da tsaftar jiki da kuma ta muhalli
domin, tsafta ita ke samar da lafiya a jikin mutane.
3.1.10
Ladabi da Biyayya
Kyautatawa ta fuskar daɗaɗawa da faranta rai ta hanyar biyayya
ga umurnin magabata ko hukuma, da aikata abin da suke so, wanda ya dace da
shari’a, shi ne biyayya.
Ladabi da biyayya manyan ƙusoshi ne a cikin tarbiyyar Hausa. Watau muhimman halaye
ne da Bahaushe yake so ya ga ana yi. Girmama na gaba
da kyautata wa na baya, su ne halayen da ake kira ladabi da biyayya (Zarruƙ da wasu 1988). Jigon
ladabi da biyayya ya fito a waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun in da ya ke nuni da yi wa hukuma da iyaye biyayya kamar
haka;
Dukkan hukumar gaskiya,
Tsarin mutan Najeriya,
Jama’a mu bi ta
da gaskiya,
Shi ne alamun tarbiya.
Tutan ƙasarmu mu girmama,
Taken ƙasarmu mu girmama,
Dokan ƙasarmu mu girmama,
Shi ne alamun
tarbiya.
Mulkin ƙasa dai dole ne,
Bin masu mulki dole ne,
Dokar ƙasa dokar mu ne,
Ta haɗe ƙasan nan bai ɗaya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya II)
Duk xa nagari ba zai qi yi wa iyayensa biyayya ba.
Biyayya ga umurnin na gaba kuwa alamun tarbiyya ce domin, Hausawa na cewa ‘Bin
na gaba, bin Allah’. Wataqila wannan ne ya sa Alhaji Xahiru Musa Jahun yake faxakar
da mutane muhimmancin yi wa Shugabanni da manya biyayya. Ba shakka a cikin waɗannan baituka akwai cusa tarbiyyar biyayya ga jama’a
dangane da bin doka da oda. Wato yi wa hukuma biyayya a kan dokokin da ta
shimfiɗa wa ƙasa don kiyaye lafiyarsu.
3.1.11
Taimako
Taimako shi ne agaji
ko tayawa (Bargery, 1993:976).
Haka kuma, taimaka
(taimako) ya ƙunshi taya aiki, ko taimakekeniya a harkokin rayuwa, ko
gudunmuwa ko kuma bayar da tallafi ko agaji ga mutum (Newman, 1997:123).
Taimako wani muhimmin
jigo ne da ke kyautata tarbiyyar rayuwa, kuma akan taimaki wanda suka sani da
waɗanda ba su sani ba.
Saboda muhimmancin taimako wajen ƙarfafa tarbiyya ne
tasa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun yake cewa,
Mu haɗe mu fidda kitse wuta,
Wani za a gyara
ko wata,
Don gyara dukkan
karkata,
Jama’a a maido tarbiya.
In za ka nuna
halin ƙwarai,
In ka ci nama ka ci ƙwai,
Wani bai da shi
maza taimakai,
In dukiyarka da
tarbiya.
(Ɗahiru Jahun:Tarbiyya
II)
Kowane mutum na duniya yana son a taimaka masa a duk
lokacin da ya shiga wani hali na tsanani. Irin hakan ne ke sa mutum ya kasa mantawa
da wannan wanda ya taimaka masa komai tsawon zamani. Shi kuwa taimako ba kowa
ke yin sa ba, sai mai tarbiyya. Wannan ne yasa Sha’irin ke nuna wa jama’a
muhimmanci da amfanin taimakon mabuqaci a cikin baitukan da suka gabata.
4.1
Kammalawa
Tarbiyya ita ce ruhin kafuwa da ɗorewar kowace
al’umma, wanda ya zama wajibi ga kowa ya mallaka, musamman yara a lokacin
samartaka domin, inganta rayuwa. Duk wani ‘yantaccen mutum da tarbiyya yake
bugun gaba. Ɗabi’ar mai tarbiya ba ta zama cuta domin, zai zamo abin
alfahari da soyuwa ga mutane.
Tarbiyya a idon Bahaushe ta ƙunshi dogara a kan
kyakkayawan ƙuduri da magana mai daɗi da kuma kyautata wa mutane, wadda takan
inganta zamantakewa har ta kai mutum ya zama ƙaƙƙarfan tubali na gina
al’umma ta gari. Abin da ake so shi ne mutum ya zama mai son ‘yan’uwansa mutane
da soyayya ta haƙiƙa, da gaskiya da riƙon amana, da gujewa
zargi da munanan halaye, da ƙana’a da taimako ta fuskar yi wa
al’umma kyauta, wato ba su wani abu da ya ragu daga abin hannunsa, bisa jin daɗi da yardar zuciya
Buƙatuwar al’umma su
tashi da waɗannan halaye ne ya sa
marubuta waƙoƙin Hausa suka yi ta amfani da alƙalumansu domin, kira
da ganin an raya wannan ɗabi’a, kamar yadda
wannan maƙala ta zaƙulo irin waɗannan jigogi, a cikin
wasu waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun.
MANAZARTA
Abubakar, A. (2001).
An Introductory Morphology. Nigeria: Faculty of Arts, University of Maiduguri.
Abubakar, S. M.
(1966). Hali Zanen Dutse. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.
Adamawa, A. (2007). Sirrin Kamalah. Bauchi:
Adamawa Media Link.
Bugaje, H. M. (2013). Tarbiyya da
Zamantakewar Hausawa: Jiya da Yau. Cikin Excerpts of International Conference
On (Taɓarɓarewar Al’adun
Hausawa) The Deterioration of Hausa Culture Organized by Katsina State History
and Culture Bureau in Collaboration with Umaru Musa ‘Yar’adua University,
Katsina.
Bunza, A.M. (2002). Yaƙi Da Rashin Tarbiya,
Lalaci, Cin Hanci Da Karɓar Rashawa Cikin Waƙoƙin Alhaji Muhammadu
Sambo Wali Basakkwace. Lagos: Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.
Bunza, U. A. (2013). Tarbiya a Cikin Adabin
Hausa: Tsokaci Daga Karin Magana. Cikin KADA Journal Of Liberal Arts Vol. 7 No.
1. Faculty Of Arts, Kaduna State University, Kaduna Nigeria.
Bunza, U. A. (2016). Matakan Kyautata Tarbiyya
A Cikin Ƙagaggun Labarai: Wata Matakala Ta Samun ‘Yan Ƙasa Nagari. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa na farko, Tsangayar Fasaha da
Nazarin Addinin Musulunci. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, U. A. (2016).
Alamomin Gurbatar Tarbiyya Yara: Nazari Daga Wasu Littattafan Ƙagaggun Labarai. Sashen
Koyar da Harsunan Najeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria:
Ahmadu Bello University Press.
Gusau, S. M. (1984).
Tarbiyya A Ƙasar Hausa Jiya Da Yau. Maƙalar Da Aka Gabatar A Taron Ƙaddamar Da Ƙungiyar Hausa, Jami’ar Sakkwato.
Kirk-Greene, da A. H. M. (1973). “Mutumin Kirki: The Concept of Good Man in
Hausa”. (Hans Wolf Memorial Lecture) Bloomington Indian. African Studies
Program.
Mustapha, S. (2003).
“Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”. M.A. Dessertation. Sokoto: Department of
Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University
Newman P. (2000). The
Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar. U.S.A.: Yale University
Press.
Newman, R. M. (1997).
An English-Hausa Dictionary. Nigeria: Longman Nigeria PLC.
Skinner, N. (1965). Ƙamus Na Turanci Da
Hausa. Zaria:
Northan Nigerian Publishing Company, Ltd.
Skinner, N. (1980).
An Anthology of Hausa Literature. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.
Umar, M. H. (1980).
Nuni Cikin Nishaɗi. Northern Nigerian
Publishing Company Ltd.
Yahya,
A. B. (2001). Dangantakar Waƙa Da Tarbiyar ‘Ya’yan Hausawa. Cikin
Mujallar Harsunan Najeriya, XIX. Centre For The Study Of Nigerian Languages,
Bayero University, Kano Nigeria.
Yahaya, I. Y. (1979).
‘Folklore As An Educational Tool’. In Harsunan Nijeriya IX. Center For The
Nigerian Languages, Kano: Bayero University.
Yahaya, I. Y. (2005).
Labarun Gargajiya 1. University Press PLC.
Zarruƙ, R. M. da Musa, I. U. da Alhassan,
H. (1988). Zaman Hausawa: Bugu Na Biyu. Lagos: Academy Press Ltd.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.