Citation:
Hassan, H. and Yankara, M. M. (2021). Karin
Magana Mai Labari: Wani Shaƙo Daga Kare-Karen Maganar Hausa. FUDMA Journal of
Hausa Studies (FUDJOHAS), 1(1). Dutsin-Ma: Federal University
Dutsin-Ma. P70-81
Karin Magana Mai Labari: Wani Shaƙo Daga Kare-Karen Maganar Hausa
Hussaini Hassan, Ph.D
Sashen Hausa
Kwalejin Ilimi ta
Tarayya,
Pankshin, Jihar
Filato.
+234 703 9283 077
husssainihassan387@gmail.com
Da
Muhammad Musa Yankara
Sashen Hausa
Jami’ar Tarayya
Dutsin-ma,
Jihar Katsina.
+234 806 2367 496
esemwaiy12@gmail.com
Tsakure
Maƙasudin wannan takarda
shi ne fitar da wani ɗan tsalli daga cikin sassan adabin Bahaushe don bayar da
misalai ga ‘yan uwa ɗalibai domin ƙara faɗaɗa bincike da nazari.
Nazarin ya yi ƙoƙarin bayyana nau’in karin magana mai labari a matsayin
wani shaƙo daga cikin kare-karen magana na Hausa”. An tsara
binciken ta hanyar garkuwa da misalan karin magana guda ashirin da bakwai (27)
waɗanda
tushen su labarai ne ko dai ya faru da gaske, ko kuma kunne ya girmi kaka domin
a daddagi bagiren sosai da sosai, a cashe a fitar da tsaba da tsakuwa a ɗebe kokonto.
Sakamakon nazarin ya tabbatar da cewa karin magana tamkar wani kogi ne da
kowane mai nazari kan yi iya shiga ya ɗebo abin da yake so daidai buƙatarsa
ya yi amfani da shi, kuma ya bar shi a nan. A ƙarshe aka shawarci ɗalibai da su faɗaɗa bincike a kan
wannan nau’i na karin magana mai labari ta hanyar gwama na Hausa da na wasu
harsunan.
1.0 Gabatarwa
Tunanin mutane da suke sarrafawa a
fatar bakunansu wani yanayi ne da ke bayyanar da fasaha da hikimomin kimiyyar
rayuwarsu da yadda suke cin gajiyarta. A kowane sashe na adabi, ana samun
nazarce-nzarce masu tarin yawa, amma har yanzu haƙa ta ƙi cim ma ruwa na
ganin an kai ƙarshe. Koyaushe aka buɗe ido ana ganin sabon binciken ilimi wanda
masana da manazarta suke aiwatarwa da gudanarwa. Karin magana, magana ce mai
tsawo wadda aka dunƙule ta, ta zama gajera cikin hikima, da zalaƙa kuma ta ƙunshi ma’ana mai yawa
in za a tsaya a warware ta. Farfesa Abdullahi Bayero Yahya a wani darasin ajin
digiri na uku, shekarar 2017 shi ya bayyana kalmar shaƙo da cewa kamar mutum
ne ya yi nutso a kogi, to abin da ya ɗebo na daga ruwa a jikinsa shi ne shaƙo. A bisa hasashe ake
kallon karin magana mai labari a matsayin ɗan wani abu da akan shaƙo daga cikin kogin
karin magana na Hausa. Abin nufi dai, karin magana wani fanni ne mai faɗin gaske wanda yake
tamkar kogi ne ga mai son nazari, ta yadda duk iya kwalfa da ɗiba, sai dai a ɗebo wani abu a bar
saura. Don haka ne ma ɗaliban adabi ke ganin
karin magana wani babban rumbu ne na kimshe hikimomin al’ummar Hausawa da ba
zai taba ƙarewa ba komin yawan masu ɗiba a kowane zango na rayuwa.
1.1
Ma’anar Karin Magana
Garba,
(2017) a wata maqala da ya rubuta mai taken “Nazarin Karin Maganar Hausa” ya kawo ma’ana daban – daban daga
masana kan karin magana, wanda ya ce wasu daga cikin masanan da suka tofa
albarkacin bakinsu dangane da ma’anar karin magana sun haɗa da: Finnegan
(1970), Hassan (1981), Tudun wada (1982), Ɗangambo (1984),
Guoling (1985), Umar (1987), Koko (1989), Yahaya, da wasu (1992), Aliyu (1996),
Bichi (1997), Birniwa (2005), Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007), Muhammad (2009),
Hassan (2009), Gwammaja (2010), Koko (2011), da Ɗanhausa (2012),
Bugaje (2014). Misali Finnegan (1970) ta ce: “Karin magana jerin kalmomi ne mai dubun hikima da zalaƙa wanda
ke zuwa a gajarce, tare da ma’ana mai gamsarwa idan aka tsaya aka yi sharhi”.
Sai
kuma Tudun wada (1982) wanda yake ganin ba wani abu ne karin magana ba illa: “magana ce wadda ake lanƙwasa
ta, ta yi daɗin ji a kunne ta kuma yi ma’ana”.
Shi
kuwa Tudun Wazirci (bkw) ya ƙara da cewa: “karin magana wani lafazi ne mai ƙunshe da hikima,
wanda yake ƙunshe da ma’ana biyu, watau bayyananniyar ma’ana (ma’ana
ta zahiri), da kuma ɓoyayyiyar ma’ana (ma’ana ta baɗini)
A taƙaice za a iya cewa
karin Magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaka
tare da bayar da ma’ana gamsasshiya mai fadi, mai yalwa, musamman in aka tsaya
aka yi bayani daki-daki. Wato karin magana takaitacciyar magana ce `yar kil
wadda ta kunshi hikima da zantukan ma’ana.
1.2
Asalin Karin Magana
Kusan a
iya cewa kowacce al’umma a duniya na da irin nata karin maganganun. Misali ɗauki harshen Larabci
a inda Bahaushe ke cewa “gani ya kori ji” balarabe kuma cewa yake “laisal al –
khabar ka al – mu’ayanah”, to haka dai abin yake. To amma dangane da batun ko
yaushe ne aka fara karin magana da kuma ko wane ne ya fara karin magana, to
“nan fa ɗaya wai an ce da
shege ina ubanka”?, don kuwa a bisa bin diddigin masana tarihi na adabi da
al’adu da harshe ba a sami wani takamaiman rubutaccen abu dangane da asalin
samuwar sassan adabin baka ba, sai dai hasashe. A sakamakon sanadiyar faruwar
wani abu sai wani abu ya samu, to wannan shi ya faɗa kan karin magana (Ɗangambo, 2008).
Masana sun ce kusan zai yi wuya wani ya bugi ƙirji ya ce ga wanda
ya fara karin magana ko ga lokacin da aka fara, wato kamar yadda yake da wuya a
ce ga wanda ya fara magana a duniya, to haka shi ma karin magana. Kusan ai ko
shi kansa harshen ma wato magana, hasashe ne da ra’o’i birjik kan asalin
samuwarsu a duniya, wanda yayin da wani ya kira sunan ra’insa da suna Bow –bow,
wani kuma da pooh – pooh ya kira sunan nasa ra’in, wani ya ce ding – dung, wani
kuwa ya ce ai tun ran gini ran zane, magana ta fara ne daga waƙa, wato daga ran da
aka haifi yaro ya fara kuka ai waƙa ce, wato ra’in
“tarara – bun – diya”. Wasu ko suka ce atafau abin na da alaƙa da addini.
To ashe kuwa ke nan a iya cewa an fara karin
magana tun lokacin da ɗan Adam ya fara sa
hikimomi da fasahohi cikin managarsa wanda ya ke tun kaka da kakanni ne. Sai
dai akwai hasashe da dama kan waɗanda ake jin su ne suka fi yin karin magana
ko haɓaka karin magana a
Hausa.
Hasashe
na nuna cewa mata, da ‘yan daudu, da maroƙa ne suka fi kowa
karin maganar Hausa. Dalilan da ke nuna mata a cewar Tudun wada (1982) ya ce
wai kusan kullum zaune suke a gida in ka ɗauke ‘yan ƙananan aikace-aikacen
gida ba sa wani aikin cas bare as, sai dai a kawo musu su dafa su wanke goma su
tsoma biyar, ba sa yin faɗi-tashin neman abinci
irin na maza, kai in har ma ka ga sun fita to da dalili wani abu ne ya taso na
buki ko kuma wata larura ta zuwa asibiti. Wannan ya sa da sun haɗa ‘yan
aikace-aikacensu na gida sai su zauna zaman hira, wannan ne ma ya sa Bahaushe
ke cewa “ƙarfin mata sai yawan magana” to cikin yawan maganar ne
suke jefa ‘yan karin maganganu wani lokacin ba ma tare da sun sani ba, shi ke
nan fa sai wani ya ji ko wata, wanda suma da sun ɗora a gaba sai ka ji wannan karin
magana ta yaɗu wanda ya ji ya ƙara yaɗa ta.
Wata
madogarar kuma ita ce ta fuskar kishi. Bisa al’ada mata ba sa son kishiya ko kaɗan, wannan ya sa ma
suke kiran kishiya da cewa tunkiya. Kishi kumullon mata in ya motsa sai an
haras, wannan ya sa a zamantakewarsu da kishiya suke jefa wa junansu ‘yan
maganganu na habaici da karin magana don muzantawa da tunzurawa. Tabbaci game
da wannan shi ne samuwar karin maganganu da ke nuna kishi kamar haka:
i.
Ba
zafi barkonon taro a idon kishiya.
ii.
Ban
gane ba an doki ɗan kishiya.
iii.
Da
alheri uwar kishiya ta hau kura.
iv.
Da
zaman banza gara aikin kishiya ko tsine mini aka yi na samu.
v.
Haka
tara inji kishiyar mai mageduwa.
vi.
Wada da wadaƙa, ta da kai da ɗan kishiya.
vii.
Ya
na iya da abin da ya gagari wuta inji kishiyar ƙonanniya.
viii.
Ku
taya ni figa, uwar kishiya ta zama kaza.
Idan
kuma aka juya ga ɗan uwan ɗayar, wato Ɗandaudu wanda shi ma
bisa ga hasashe an nuna cewa yana ɗaya daga cikin waɗanda suke ƙirƙiro karin magana.
Wannan kuwa shi ma bai rasa nasaba da yawan maganarsu da kuma kasancewar su
cikin mata a kodayaushe ba.
Rukuni
na gaba shi ne na maroƙa, wanda su ma ba baya ba ne wajen taka mahimmiyar rawa
ga ƙirƙiro ko samuwar karin
magana a Hausa ba. Su maroƙa su ne waɗanda suka riƙi roƙo a matsayin sana’a,
wannan roƙo kuwa kan iya zama roƙon baki ne irin waɗanda ake cewa maroƙan baki ko kuwa masu
amfani da kiɗa ne, duk dai harka
ce ta magana wanda wannan ne ya sa suke da yawan karin maganganu. A cikin
maganar ne sukan yabi wanda suke son abinsa. Don haka kusan ya zama dole su yi
amfani da kalamai masu armashi wanda karin magana na ɗaya daga ciki. To fa
a nan ne za ka ji karin magana na fita, wani lokacin ba tare da ma sun sani ba.
Duba kirarin da sukan yi wa jarumai ko yabon gwanayensu za ka iske karin
maganganu ne a ciki.
Shi kuwa Gusau (2003) a nasa bayanin, cewa ya
yi irin waɗannan zantukan karin
magana sun samo asali ne lokacin da Bahaushe ya fara yin farauta yana kama
namun daji, idan wani ya yi ƙoƙari ya kama dabba ko
ya kashe ta, a wajen wannan yunƙuri na bajinta yakan faɗi wasu lafuzza na
maganganu na kuranta kai waɗanda suka ƙunshi hikima ko wasu
kalmomi da suka yi kama da “karin magana”. To, a na ganin daga irin waɗannan maganganu ne
aka fara ƙirƙirar karin magana.
Koma dai ya abin yake, a ƙarshe dole a tafi bisa ga ra’ayin nan na tun ran gini tun ran zane. Wato babu wanda zai iya cewa shi ne asali ko mafarin karin magana, kowa sai dai ya buɗe ido da kunnuwa ya ji ana yin sa.
1.3
Rabe–Raben Karin
Magana a Hausa
Garba,
(2017) ya bayyana cewa dangane da ire – iren karin magana a Hausa, akwai masana
da dama da suka tofa albarkacin bakinsu. Sai ya kawo misali da Hassan (1981), Ɗangambo (1984),
Guoling (1985),Yahaya, da wasu (1992), Aliyu (1996), Hamisu (2006), Junaidu da
‘Yar’aduwa (2007), Hassan (2009), Tudun Wazirci (bkw). Sai dai kusan kowane da
yadda yake kallon yadda ya kamata a rarraba karin magana. Wasu na la’akari da
lokacin samuwar karin maganar ya yin rarraba su, ya yin da wasu kuma ke
la’akari da siga ko tsari ta wannan karin maganar. Ko kuma a yi rabon ta
la’akari da jigogin karin maganar. Amma dai a wannan takarda an kawo dukkan
rabon da manazarta da masanan suka yi ne a zube, kan yadda aka samar da kowane
nau’i na karin magana. Ga su kamar haka:
·
Karin
magana mai “tambaya da amsa”.
·
Karin
magana mai “labari”.
·
Karin
magana mai “in ji”.
·
Karin
magana mai “an ce”.
·
Karin
magana mai “ya fi” ko “ta fi”.
·
Karin
magana mai “kowa”.
·
Karin
magana mai “nasiha”.
·
Karin
magana mai “habaici”.
·
Karin
magana mai “Hausawa sun ce”.
·
Karin
magana kafin zuwan addinin Musulunci.
·
Karin
magana bayan zuwan addinin Musulunci.
·
Karin
magana bayan zuwan Turawa. Misali:
·
Karin
magana mai ɗauke da gajeruwar
Jumla.
·
Karin
magana mai “ɓangare biyu”.
·
Karin
magana mai “alaƙa da tarihi”.
·
Karin
magana mai mai “faɗar gaskiya”.
·
Karin
maganar “ko oho”.
·
Karin
maganar da ta fara da “In” a farko.
·
Karin
maganganu masu daɗaɗɗen asali.
·
Karin maganganu da suka samu a sanadiyyar
la’akari da rayuwa.
·
Karin
magana mai mutumtarwa.
·
Karin
magana mai kamantawa.
·
Karin
magana mai kanbamawa.
·
Karin
magana mai korewa.
·
Karin
magana mai tabbatarwa.
·
Karin
magana mai nuna sana’a.
Daga
cikin waɗannan rassa ne maƙalar za ta yi magana
a kan ɗaya wato karin magana
mai labari.
2.0
Karin Magana Mai
Labari
Wannan
wani nau’i ne na karin magana wanda a bisa asali ya samu ne ta hanyar wani abu
da ya faru. Ire-iren waɗannan karin maganganu
sukan samo asali ne daga wani labari wanda ya faru da gaske, ko kuma wani
labari da aka ƙirƙire shi wanda bai faru da gaske ba, ko kuma labarin da
aka same shi daga wata tatsuniya, (Gwammaja, 2018). Shi irin wannan karin
maganar da wuya a fahimci abin da ya sa gaba ko abin da ake nufi da shi, idan
ba a san asalin labarin da aka samar da karin maganar daga shi ba. Domin haka
ana fahimtar karin maganar ne idan an san labarin abin da ya faru wanda ya
haddasa samuwar wannan karin magana. Wannan takarda kamar yadda aka bayyana a
baya wajen gabatarwa za a kawo irin waɗannan karin maganganu tare da bayyana yadda
labarin asalinsu yake. Kaɗan daga cikin misalan
da wannan takarda ta yi ƙoƙarin bincikowa sun haɗa da:
1.
Saurin
Tagumbi Saurin Banza.
2.
Sammakon
bubukuwa
3.
Gyaɗar Dogo.
4.
Biɗar Gatarin Arne.
5.
Sautun
Mahaukaciya.
6.
Adashen
Balaraba.
7.
Adashen
Uwar Nuhu.
8.
Isar
ƙadagi
Isar Banza.
9.
Cin
Daƙuwar
Buzu.
10.
Faɗan Gwaggo a Kofa.
11.
Sanin
Damisar Bunu.
12.
Jiran Gawon Shano.
13.
Gaba ta Kai ni Gobarar Titi a Jos.
14.
Rufin Kan Uwar Daɗi/Lulluɓin Taladan.
15.
Zuwan Fara Garko.
16.
Lissafin Dokin Rano.
17.
Dare Mahutar Bawa.
18.
An Yi Daidai, Sayen Wandon Bafullace.
19.
Fargar Jaji.
20.
Jifan Gafiyar Vaidu.
21.
Ƙunar Baƙin Wake.
22.
Ɗaukar Ruwan Ɗan’amo.
23.
Gamon
Katar
24.
Sayen
Dusar Kwarto
25.
Biyar
biyu ba ta goma
26.
Taka
Wutar Ungulu
27.
Ana
so Ana Kaiwa kasuwa.
Domin
fito da ma’anar muƙalar, ga bayanin kowane daga cikin karuruwan maganar da
aka ciro da tare da dalilan amfani da su a harshen Hausa.
2.1
Saurin Tagumbi Saurin
Banza
Wai
wani mutum ne da matan sa guda huɗu amarya da uwar gida, da turaki da kwari.
Ita amaryar ita ce mai suna Tagumbi. To a bisa al’ada sukan je gona su ɗebi amfanin gona,
amma akan ware wata rana da za su je. Sai ranar kwanan amarya ya faɗa don haka sai mijin
ya gaya mata, kan ta yi sammako ta je don kafin kishiyoyinta su iso ta tara da
yawa, saboda ya fi son ta samu mai yawa. Da asubahin fari amarya ta fita ba
tare da ta sanar da sauran matan ba, sai bayan ta tafi da daɗewa ya zo ya faɗa wa uwargida da
turaki, da kwari suka fito suna sauri. Bayan sun kusa kaiwa gona sai suka haɗu da amarya, ita da
ta je amma ta juyo, suka tambayi Tagumbi lafiya? sai ta ce “ai ta manta da
laujen da za ta yanki shinkafar, domin haka za ta koma gida ne ta ɗauko”. Ai ko kafin ta
dawo sun tara shinkafa mai yawa sai saura kaɗan. To wannan shi ne idan mutum saboda sauri
ya mance wani abu muhimmi sai a ce wannan ai shi ne saurin Tagumbi saurin
banza.
2.2
Sammakon Bubukuwa
Bubukuwa
tsuntsuwa ce wadda kan yi sammako da sassafe duku-duku, ko ma ka ce da assalatu
ta tafi bakin ruwa kiwo amma kuma ba ta fara kiwo sai rana ta take, bayan ƙwari da dukkan abin
ruwa sun koma. Da yamma sai ta tafi can kan tudu ta kwana. Wannan ya zama
sammakon banza domin ga shi ta fito tun safe amma ba ta fara kiwo ba sai bayan ƙwari sun koma na ruwa
sun shige ruwa wanda ya zama sammako marar amfani. Ana amfani da shi lokacin da
mutum ya kasa moriyar amfanin wani abu lokacin da ya dace, sai bayan lokaci ya ƙure.
2.3
Gyaɗar Dogo
A nan
ma cewa aka yi wani mutum ne ake bin sa bashi, sai ya ce in amfanin gonarsa ya
yi zai biya. Ya yi ta karvar bashi da zummar in an sare amfani gona zai biya.
Sai ya shuka gyaɗa, ga shi kuma bashin
yana da yawa. To a she a gonar bai sani ba varayi wata rana sun yiwo satar kuɗi sun zo gonar sun
binne. Da gyaɗa ta nuna ya zo farɗa, yana tona rami
guda sai ya ga kuɗi. Bugu da ƙari ya samu amfani
mai yawa, ga kuma kuɗin da ya tono, ya
biya bashin da ake binsa duka har ya rage saura. Idan mutum Allah ya taimake
shi ya samu mafita kan wani al’amari akan ce Allah ya masa gyaɗar dogo.
2.4
Biɗar Gatarin Arne
Shi
kuma wannan kamar yadda aka sani galibi shi arne kullum gatarinsa na kafaɗarsa. An ce wani arne
ne ya zo yana ta faɗan ina gatarinsa
yake, ya manta da cewa yana nan a kafaɗarsa. Daga nan ne in mutum ya manta yana
neman abu bayan abun na gare shi ko ma a hannunsa akan ce wannan ai shi ne biɗar gatarin arne. Ga
abu a hannunka kana ta nemansa har da faɗa.
2.5
Sautun Mahaukaciya
Mahaukaciya
ce ta ga za a kasuwa kowa na ba da nasa sautun, wannan ya ce ga shi a sayo min
abu kaza, wannan ya ce a sayo min abu kaza na kaza. Sai ita ma ta ɗauko kuɗi ta ce ga shi. Aka
ce “me za a sayo miki” sai ta ce “ni na sani?”. A wata faɗar kuma aka ce ta ce
“komai”. A wani labarin kuma cewa aka yi ta ce “a sayo mata nama, amma ban da ƙashi ban da tsoka ban
da kitse ban da jijiya”. Idan mutum ya yi abin da shi kansa bai san mene ne ba
sai ace masa ya yi sautun mahaukaciya.
2.6
Adashen Balaraba
Ita dai
Balaraba ta ga matan unguwa sun shirya adashe, aka taya mata sai ta ji kunyar
ta ce ba ta yi don kar a ga kasawarta, sai ta yarda za ta yi duk da cewa ta san
ba ta iya zubi, don ba ta da sukuni kamar sauran matan, domin haka da lokacin
zubi ya yi sai ta aiki ‘yarta maƙwabta ta ranto mata
kuɗi sai ta zuba, da
wani lokacin zubin ya yi sai ta sake aika wa wajen wasu daban aka ranto mata kuɗi ta zuba. Haka ta yi
ta yi har lokacin ɗauka ya zo da ta
kwasa sai ta rarraba wa waɗanda ta yi ta karɓo kuɗin su tana zubi. Da ‘yar ta ce to ke inna ba
ki samu ba, sai ta ce ba dai mun shiga mu ma an yi da mu ba.
2.7
Adashen Uwar Nuhu
Akwai
wata mace da ake kira uwar Nuhu, wadda ta shiga adashe irin na mata. Da shigar
ta sai ta yi sa’a aka ba ta kwasar fari. Da lokacin zubi ya yi aka zo karɓa, don a haɗa a ba wata, sai ta
ce ai ita ta fita adashen tuntuni. Wannan karin magana mata sun fi amfani da
shi in suna son nuna wa mutum ya kasa rama alkhairin da aka masa musamman wajen
rikicin biyan buki.
2.8
Isar Ƙadagi
Isar Banza
Wani
mutum ne mai suna Ƙadagi, wanda shi a kullum yakan yi kyauta ne da abin da
ba nasa ba, saboda isa. Hausawa na amfani da wannan karin magana idan mutum ya
yi kyauta da abin wani ko kuma yana nuna iko da abin da ba nashi ba sai a ce
isar ƙadagi isar banza.
2.9
Cin Daƙuwar
Buzu
Wannan na kusan ɗaya da sayen sabulun Ba’auzini. Wai
buzu ne ya sayi wani abu da ake yi da toka. Ya gan shi kato a cure ya ɗauka daƙuwa ce, ya kira
yarinya ya ce mata ke ban daƙuwa. Sai ya ba ta kuɗi ta bashi. Ita kuma
ba ta ce masa ai ba daƙuwa ba ce. Da ya tafi sai ya fara ci ya ji abu ba daɗi. To don kar ya
yasar, ya yasar da kuɗinsa sai ya ci gaba
da ci, yana rufe ido, wannan shi ake cewa cin daƙuwar buzu. Wasu kuma
cewa suka yi Ba’auzini ne ya sayi sabulu ya ɗauka abin ci ne ya kama ci, ya ji ba daɗi. Ba ya son kuma ya
zubar yana ganin ya yi asarar kuɗinsa. Ana amfani da wannan karin magana in
mutum yana amfani da abu a bisa dole ba da son ransa ba.
2.10
Faɗan Gwaggo a Kofa
Wai
wata tsohuwa ce ta ci kwalliya irin ta yara ‘yan mata ta sa takalmi coge ta yi
shafe-shafe irin su jan baki da sauran su kwalliya ta yara, ta shiga cikin
birni. Tana tafiya sai ta haɗu da yaran birni suka yi ta mata ihu da dariya, ba ta
kula su ba. Sai bayan da ta dawo gida ƙauye, wato garin su
sai ta haɗu da wasu yara na
wasa sai ta hau su da zagi da duka wai yara sun mata ihu a cikin birni. To daga
nan ne aka sami wannan karin magana in mutum ya tasamma faɗa ba a inda ya dace
ba sai a ce wannan ai shi ne faɗan Gwaggo a Kofa.
2.11
Sanin Damisar Bunu
Wai an
ce shi kuma wannnan karin maganar ya samo asali ne daga wani da ake kira Bunu.
Wanda aka tambaye shi ko ya san damisa ya ce eh, aka ce ya take. Sai ya ce tana
nan jikin ta dabbara-dabbara kamar jikin mussa, wato kuliya. Sai aka ce eh
lalle ka san ta, sai ya ce tana ma da ‘yan ƙahonni. Sai aka bushe
da dariya aka ce, ya san ta amma ba sosai ba. Shi ne in mutum bai san abu sosai
ba sai a ce ya wa abin sanin damisar Bunu.
2.12
Jiran Gawon Shano
Wannan
kuma an ce shanu ne za su kiwo sai suka ga gawo, wani ita ce ne mai ‘ya’ya
wanda ‘ya’yan a wajen dabbobi abu ne mai daɗi, kamar ka ce mayunwaci ne a ƙasar Hausa ya samu
damammiyar fura da nono kindirmo, ko ya samu tuwon laushi miyar kuɓewa da man shanu da
yaji da naman rago. To amma fa shi gawo sai iska ta ɗan kaɗa yakan faɗo. Domin haka, ba
tabbas ba ne cewa zai faɗo. Sai kawai shanun
nan suka ƙi tafiya kiwo suka zauna jiran in ɗan gawon nan ya faɗo su ci. Har dai suka
gaji, su ba su je kiwo a ranar ba, shi kuma gawo bai faɗo ba. Shi ne Bahaushe
ke amfani da wannan karin maganar in mutum ya tsaya jiran abin da ba shi da
tabbacin samunsa. Maimakon ya tafi ga wanda yake da tabbaci.
2.13
Gaba ta Kai ni
Gobarar Titi a Jos
Wai
wata ce ana ce mata Titi, wuta ta kama ɗakinta ta yi gobara kusan komai nata ya ƙone wuta ta cinye.
Mutane suka yi ta zuwa suna mata jaje, duk wanda ya zo jaje yakan ɗan zo mata da wani
abu, wani ya kawo riga wani ya kawo zani mai abinci na kawo wa, mai kawo kayan
amfanin gida ya kawo har aka haɗa wa Titi kaya sama da abin da gobar ta cinye. Sai ta ce
wannan gobara ai ni gaba ta kai ni. Wato ta samu abu sama da wanda take da shi.
To shi ne ya zama karin magana Hausawa na amfani da shi in sun so nuna yadda
wata asara ta juye zuwa samu ko amfani.
2.14
Rufin Kan Uwar Daɗi/ Lulluɓin Taladan
Uwar Daɗi wata dattijiya ce
mai tsananin sakarci. Wata rana ta fito za ta je maƙwabta daga ita sai
zane ga ba ɗankwali ba mayafi, ko
ma ka ce ɗaurin ƙirji. Sai kawai ga
surukinta tare da abokansa sun doso wajenta, can gefe kuma ga taron jama’a suna
zaune suna hira. Da ta ga sun yi ido huɗu da surukinta cikin wannan hali, sai kunya
ta kama ta. Saboda haka, sai ta cire zanen da take ɗaure da shi ta rufe
kanta da shi ta bar gabanta fayau a gaban surukinta. Wannan ne ya sa Bahaushe
ya ɗauki wannan labari ya
mayar da shi karin magana yake amfani da shi in ya so nuna cewa mutum ya bar
abin da ya fi dacewa ya tafi zuwa ga wanda ba shi ya dace ba, ko bai kai shi
muhimmanci ba. Wasu ma kan ce rufin kan uwar daɗi gabanta babu kariya ko lulluɓin Taladan.
2.15
Zuwan Fara Garko
Wai
wata rana ne fari suka dira cikin wani gari da ake kira Garko da nufin yin ɓarna. Amma da suka
isa garin sai suka tarar har an tattare amfani an sanya cikin rumbu an rufe.
Domin haka sai farin suka kama hanyar da suka fito, amma sai mutanen garin suka
riƙa
kama farin ba tare da sun bari sun kai labari ba, suna cinyewa. Wannan karin
magana shi ne Hausawa ke amfani da shi in sun tashi nuna wani ya je neman wani
abu amma maimakon ya samo sai ya rasa nasa. Ko ma ya halaka a can, kamar yadda
farin suka halaka.
2.16
Lissafin Dokin Rano
Rano
bawan wani sarki ne mai yawan dawakai. Wata rana ya je kiwo sai ya hau doki ɗaya. Lokacin dawowa
gida ya yi, Rano sai ya ƙirga dawakin don ya tabbatar ba a bar ko ɗaya a baya ba. Ko da
ya ƙirga
sai ya ga babu ɗaya, sai ya sauko
daga doki don ya duba ko ya je wani waje ne, amma bai gan shi ba. Sai ya komo
ya sake ƙirgawa ya ga sun yi daidai, amma da ya sake hawan dokinsa
ya ƙirga
sai ya ga kuma ba su cika ba. Bai san cewa shirme yake yi bai ƙirgawa da wanda yake
saman sa ba. Akan yi amfani da wannan karin magana idan mutum yana shirme a
cikin lissafi.
2.17
Dare Mahutar Bawa
Shi
kuma wannan an gina ta ne kan labarin wani bawa da ya taɓa katoɓara a kunnen
maigidansa. Shi dai wannan bawa an ce kullum ba shi da hutu cikin aiki yake,
sai dai in dare ya yi yakan je ya kwanta kafin safiya ta waye ya koma kan aiki.
A haka ne wata rana ya yini yana aiki ya matsu dare ya yi ko ya kwanta ya huta.
Da dare ya yi ya zo kwanciya sai ya ce “dare mahutar bawa ko ubangida bai so
ba”. Ashe ubangidansa na kusa kuma ya ji abin da ya faɗa. Domin haka nan take
ya umarci bawan nan da ya je gulbi ya ɗauko ruwa kai/sau goma. Sai bawan nan ya
fahimci cewa ubangidansa ya ji abin da ya ce. Domin haka da ya ƙare ɗiban ruwan ya zo ya
kwanta sai ya ce “dare mahutar bawa in ubangida ya so”.
2.18
An yi Daidai, Sayen
Wandon Bafullace
Wannan kuma labarin na cewa wai wani Bafullace
ne ya je kasuwa don ya sayo wando. Da isar sa shagon farko, sai ko ya ga wandon
da yake so. Ya tambaya nawa wando? Aka ce naira biyar (5), ya ce an yi daidai,
da ma su kaɗai ne a cikin aljihun
amshi ga su. Hausawa na amfani da wannan karin magana idan an so a nuna cewa faɗuwa ta zo daidai da
zama.
2.19
Fargar Jaji
Shi
kuma wannan an ce wani mayaƙi ne Jaji wanda a saboda tsananin
shirinsa har layar ɓata yake da ita.
Wadda in ana yaƙi in ya taɓa ta sai ya ɓace. Wata rana aka je yaƙi, amma Jaji ya manta
da cewa yana da layar ɓata, har dai aka sare
masa kai can sai ya tuna bayan har an riga an sare kan. Wai kafin ka ce me ana
sare kan sa sai ya taɓa layar sai ga kan
Jaji yana ɓingirawa ɓingir-ɓingir, amma gangar
jiki kuma ta ɓace. Wato ya makara,
bai yi amfani da layar ba a lokacin da ya dace. To shi ne in mutum ya tashi yin
abu bayan abin ya wuce akan ce wannan kuma ai ya zama fargar Jaji.
2.20
Jifan Gafiyar Ɓaidu
Shi dai
Ɓaidu
an ce mafarauci ne. Wata rana ya je farauta sai ya kama gafiya, har ya juya zai
tafi sai ga wata kuma ta fito daga ramin a guje, sai Ɓaidu ya kai mata jifa
da ta hannunsa da nunin ya buge ta ya haɗa ya kama duka biyu. Sai ita ma ta ware ta bi
‘yar uwarta suka gudu, ya yi biyu babu, ba wadda ya kama ba wadda yake son ya
kama ɗin. Shi ne mutane ke
amfani da wannan karin magana in an ga mutum na neman sakin wanda ke hannun sa
bayan bai riga ya samu wani ba.
2.21
Ƙunar Baƙin Wake
Shi
kuma wannan wani bawan sarki ne mai suna baƙin wake. To shi sarkin
nan yana da wani ɗa wanda shi maimakon
ya hau doki irin yadda sauran ‘ya’yan sarki ke yi, a’a shi bawa yake hawa.
Bawan ya goye shi ya zaga da shi duk inda yake so saboda isa da ƙasaita. Dukkan bayin
nan abin na damunsu. Sai ranar nan abin ya faɗo kan baƙin wake, wato yau shi
za a hau. Domin haka yana ɗaukar ɗan sarkin nan sai ya ruga ya faɗa da shi cikin wutar
katsi da ake dafa baba na yin rini. Ya kuma riƙe ɗan sarkin nan suka ƙone gaba ɗaya ana kallon su ba
mai shiga. Ɗan sarki ya yi ta ihu, ina a banza suka ƙone da shi da ɗan sarki. To shi ne
in mutum ya ta shi hallaka wasu ko wani, duk da cewa shi ma zai mutu tare da
wanda yake son ya kashe, shi ne ake cewa ƙunar baƙin wake.
2.22
Ɗaukar Ruwan Ɗan’amo
Shi kuma wannan wai wani tsoho ne da ake cewa Ɗan’amo wanda yake son
ya samu wani aiki na lada da zai riƙa yi. To amma kuma ba
shi da ƙarfi na yin wani aiki mai wahala, saboda haka sai ya zaɓi da ya ji an yi
mutuwa ya je ya ɗebo ruwa a bokiti ya
kai ya ce ga shi a wanke mamaci da shi. To shi ne aka samu karin magana, wanda
in an yi wani abu da mutum ke neman shiga abin da zai kai shi ga mutuwa sai a
ce kai kar Ɗan’amo ya ɗauko maka ruwa. Ko kuma a ce yanzu Ɗan’amo ya ɗauko maka ruwa.
2.23
Gamon Katar
Katar wani mutum ne mai aikata saɓo, ɗan fashi ne. Ya kashe mutum har ɗari ba ɗaya. Sai shiriya ta zo masa ya ce yana so ya tuba in Allah zai gafarta masa. Sai ya sami wani malami ya ce masa, kaji-kaji irin aikina, amma so nake na ji ko in na tuba Allah zai gafarta min. Sai malamin nan ya ce kai wannan aiki naka ya yi muni, mutum ɗari ba ɗaya, ai ba kai ba rahama, ba abin da Allah ya ƙi kamar kashe ran mumini ba tare da haƙƙi na shari’a ba, tafi-tafi ba ni wuri kar laifinka ya shafe ni. Ƙatar na jin haka sai ya ce ah to ai tun da haka ne, bari na cike na ɗarin, sai ya kashe malamin. Duk da haka Ƙatar bai haƙura ba sai ya sake zuwa gun wani malamin ya bayyana masa halin da yake ciki. Sai malamin ya ce masa ai Allah mai gafara ne in ka tuba Allah zai gafarta maka. Sannan in ka tuba akwai wani gari na tubabbu da za ka je can ka yi ta ibada in ka mutu sai ka shiga aljanna. Sai ya ce to ya ji ya gode, Ƙatar ya tuba ya kuma kama hanya zuwa garin nan da malamin ya faɗa masa. Ya kusa isa garin sai Allah ya ɗauki ransa, Ƙatar ya faɗi ya mutu. Sai mala’ikun rahama da na azaba suka iso waɗannan na cewa nasu ne, waɗannan na cewa nasu ne. Sai nan kuma Allah ya aiko wani mala’ika don ya raba musu gardama, aka ce a auna da inda ya baro da inda za shi ina ya fi kusa. Sai aka ga inda ya nufa ya fi kusa. Sai aka ce to na mala’ikun rahama ne. Mafarin amfani da wannan karin magana shi ne idan mutum ya shiga tsaka mai wuya kuma ya samu fita.
2.24
Sayen Dusar Kwarto
Wannan karin magana ya samu ne lokacin da wai wani mutum da matarsa bayan ya tafi wurin neman abinci wajen fatauci kullum sai abokinsa ya zo wurin matar. Sai rannar nan mijin matar ya nuna wa abokin ai zai yi tafiyar nan da ya saba. Da ya tashi sai ya tura matar gida ya zauna shi kaɗai. Can sai kwarton ya zo kai tsaye ya shigo gidan sai mijin ya fito ya ce me ya kawo ka sai ya ce dusa na zo saya. To shi ne in mutum ya yi wani rashin gaskiya aka kama shi amma ya waske sai a ce yay i sayen dussar kwarto.
2.25
Biyar Biyu ba ta Goma
An ce wai wani mutum ne yake da ‘ya’ya huɗu sai ya auro wata mace ita kuma da ta zo sai ta zo masa da ‘ya’ya huɗu sannan kuma ta haifa masa ɗaya. Idan an haɗa da ɗan matar da nasa huɗu sun zama biyar ita ma idan ta haɗa da na mijin da huɗun sun zama biyar amma kuma da za a haɗa biyar da biyar ɗin ba za su zama goma ga kowannen su ba. Shi ne ake cewa biyar biyu ba ta goma. Ana amfani da shi idan an ga wani mutum ya tashi nuna isa kan wani abu wanda duka ba nasa ba ne.
2.26
Taka Wutar Ungulu
Karin maganar ta samo asali wai lokacin da ɓera ya ga ungulu za ta taka wuta, sai ya ce mata ungulu za ki taka wuta. Sai ta sa ƙafa ta taka ta ce masa “an taka ɗin ina ruwan ka”. Da ungulu ta ji zafi sai ta fitar ta ce “an ɗauke kuma an ƙi a taka”. To shi ne in mutum zai yi wani abu aka hana ya ƙi bari, bayan ya aikata sai ya yi nadama nan da nan sai a ce ya taka wutar ungulu.
2.27 Ana so ana kai wa kasuwa
Shi kuma wannan karin maganar labarin samuwarsa ya nuna ne cewa wai wata rana ne wata Bafulatana ta xauki nono za ta kai kasuwa, sai ta haxu da wata mahaukaciya ta ce mata “ke zo, kawo sauke, zuba na xari” Bafulatana ta zuba tana rawar jiki, ta sake ce mata “to shanye” Bafulatana ta shanye, ta sake ce mata “qara na xari” ta zuba ta sake ce mata “shanye” Bafulatana ta shanye. Sai ta ce mata “to xauke tafi, a she ana so ake kai wa kasuwa”. To shi ne asalin samuwar wannan karin magana da Bahaushe yake cewa ana so ana kai wa kasuwa. Wato idan mutum ya na son abu amma yana nuna kamar ba ya so, yana fulako shi ne sai a ce masa oh kana so kana kai wa kasuwa, kana so kana nuna kamar ba ka so.
3.0 Kammalawa
Hikimar
Hausawa ta cewa “zama wuri ɗaya tsautsayi in ji kifi” shi ya tabbatar da zancensu na
da koyo a kan iya. A wannan takarda kamar yadda bayani ya gabata an ga cewa
karin magana wani fannin nazari ne a farfajiyar adabin baka wanda ke da faɗin gaske. Kowane rabo
aka ɗauka a cikin waɗannan ya isa a yi
bincike mai yawa a kansa har a samar da abin da ake hanƙoron samu. Kuma kamar
yadda aka sani kowane harshe na da karin magana duk da dai in dambu ya yi yawa
ba ya jin mai. Amma duk da haka mai nazari kan iya kwatanta na wani harshen da
wani harshen domin ganin ta ina suka yi kama da kuma ta ina suka bambanta kuma
ta wace fuska, tsari ko jigo. Akwai harsuna masu yawa cike da guraben bincike
da ɗaliban Hausa ya
kamata su ɗauki ko da nau’i ɗaya tare da kwatanta
shi da na harshen uwa domin ganin ya ya yi kama ko ya bambanta. Sannan a duba a
ga ko wannan nau’i na karin magana mai Labari akwai shi a wasu harsunan ko kuwa
babu? Ko ba komai da komai hakan shi zai sa a ƙara inganta fannonin
da samar wa kowane fanni gyauto daidai da kwankwason sa. Domin kuwa tabbas
zancen Hausawa gaskiya ne da suke cewa da rashin tayi akan bar arha.
Manazarta
Aliyu,
M. (1990) “Sabbin Karin Magana A Hausa”. Kundin Digiri Na Farko. Zaria: Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Ahmadu Bello.
Amin,
M. L. (2004). ‘Re – Interpreting Hausa Proverbs On Duniya.’ Harshe 2. Zaria: Department Of Nigeria
And African Languages, Ahmadu Bello University.
Birniwa,
H.A. (1984). “Tsintar Dame A Kala: Matsayin Karin Magana A Cikin Waƙoƙin Siyasa”. Ɗunɗaye Jounal Of Hausa
Studies.
Department Of Nigerian Languages. Sokoto: Usman ƊAnfodiyo University.
Bugaje,
M. H. (2016). HaƙUri Da Juriya A Mahangar Bahaushe: Tsokaci Daga Karin Magana. Takarda Da
Aka Gabatar A Taron ƙAra Wa Juna Sani, Jami’ar Bayero Kano Ranar 9-12 Ga
Watan Oktoba, 2016.
Bugaje,
M. H. (2014). Karin Magana Mahanga Tunani: Nazarin Lokaci A Hausa” Kundin
Digiri Na Uku. Zaria: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da
Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.
ƊAngambo, A. (1984) Rabe-raben
Adabin Hausa Da Mahimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triuph Publishers
Ltd.
ƊAngambo,
A. (2008) Rabe-raben Adabin Hausa.
Zaria: Amana Publishers Ltd.
ƊAnhausa,
A.M. (2012). Hausa Mai Dubun Hikima. Kano:
Century Research And Publishing Company.
Garba,
B. (2017). Nazarin Karin Maganar Hausa. A Cikin Reading In Languages, School Of
Languages Federal College Of Education Pankshin.
Guoling,
Z. (1985). “Kwatanta Karin Maganganu
Na Hausa Da Na Sinanci” Nazari A Kan Harshe, Da Adabi, Da Al’adu. Kano: Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Gusau,
S.M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar
Baka.
Kano: Benchmark.
Gwammaja,
K. (2010). “Karin Magana A Ƙasar
Hausa”.
Kano: A Division Of Rabi’atu Publishers.
Hamisu,
A. (2006). Dangantakar Karin Maganar Hausa Da Wasu Ayoyin Ƙur’ani Da Hadisai.” Kundin Digiri Na Farko. Zaria: Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya Da Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.
Hassan,
M.B (1981) “Karin Magana Da Salon
Maganar Hausawa”, Nazari A Kan Harshe, Da Adabi, Da Al’adu. Kano:
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Hassan,
S. (2009) “Nazarin Karin Magana Da
Suke Nuna Rarrashi”. Harshe 3. Zaria: Department Of Nigeria And African
Languages, Ahmadu Bello University.
Junaidu,
I. Da Yar’aduwa, T.M (2007) Harshe Da
Adabin Hausa A Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Spectrum
Books Limited.
Kirk –
Greene, A. H. (1966). Hausa Ba Dabo Ba Ne.
Ibadan: University Press Ltd.
Koko,
H. S. (2011). “Hausa Cikin Hausa”. (Ba
Maɗaba’a).
Koko,
H. S. (1989). “Karin Magana A Hannun Mata A Garin Sakkwato.” Kundin Digiri Na
Farko, Sakkwato: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.
Kwakwaci,
K. H. (2010) Asalin Hausawa. Kano:
Harsashi Punlishers, Ltd
Muhammed,
Y. M. (2003). Adabin Hausa. Zaria:
A.B.U University Press Ltd.
NNPC
(1958). Karin Magana. Zaria: Northen
Nigerian Publishing Company.
Tudun
Wazirci, A.G.I (Bkw). “Ƙalailaicewa A Kan Karin Maganar Hausawa.” Kano: Sashen Nazarin
Harsuna, Makarantar Shari’a Da Nazarin Addinin Musulunci Ta Aminu Kano.
Yunusa,
Y. T/Wada (1981). “Tsari Da Ma’ana A
Karin Maganar Hausa”, Nazari A Kan Harshe, Da Adabi, Da Al’adu. Kano:
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Yusuf,
Y. (1970). Hausa A Dunƙule. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.