Salo Asirin Waƙa na Farfesa Abdullahi Bayero Yahya [04 - Babi Na Uku]

     Salo Asirin Waƙa

    Salo Asirin Waƙa

    Salo Asirin Waƙa
     

    BABI NA UKU

    Muhimmancin Salo

    A cikin babin da ya gabata ba za ta rasa bayyana ba cewa lalle mawaƙi yana da matuƙar bukata ga salo domin ya isar da abin da ya ji ko yake ji a ransa, ko ya gani da idonsa (na zahiri ko na zuciya), ko kuma abin da ya ji ga jikinsa, zuwa ga mai saurare ko karatun waƙarsa. Haka kuma ba za ta rasa ɗarsuwa ga zuciyar mai karatun babin ba cewa lalle salo mai ƙwaƙƙwaran tasiri ne kan mai saurare ko karatun waƙa, ta fuskar jinsa a rai da zuciyarsa, da kuma ta fuskar yadda ma’anar (saƙo) waƙar take a fahimtarsa. Lalle kuma salo muhimmin gimshiƙi ne da ke zaƙulo martanin da mai sauraren waƙa zai yi.

    Idan kuwa haka abin yake ashe da’awar nan ta daddale wadda aka yi kan cewa salo shi ne asirin waƙa. Saboda haka duk wani abu da za a faɗa a wannan babi ƙari ne bisa ga hujjojin da suka riƙa kunno kai a babin da ya gabata yayin tattaunawa kan tubakan salo. Wannan ƙari kuwa shi ne abin da Babi Na Biyu yake ɗauke da shi da taken muhimmancin salo.

    Akwai aƙalla fuskoki goma da za a iya kallon muhimmancin salon waƙa da su. Waɗannan kuwa sun haɗa da kwarzanta waƙa da isar da saƙonta da bambanta mawaƙi da kuma ita kanta waƙa. Salon waƙa mai rayar da harshe da kaifafa tunanin mai ji ko karanta waƙa ne, a waje ɗaya kuma salo shi ke sa waƙa ta sosa zuciya bayan da shi ne musabbin sanya waƙa ta kasance mai iya sarrafa tunani tare da bayyana shi cikin wata fahimta da sauran ɓangarorin adabi ba su iya yi sosai kamar ita waƙar. Ta haka ne sai salon waƙa ya sadar da mawaƙi ga mai saurare har su ɗanɗani kusan abu guda fiye da yadda abin zai kasance tsakanin sauran mawallafan adabi da mai sauraren su. Cikon na goma ɗinsu shi ne cewa salo asirin waƙa ne. Waɗannan su ne fuskoki goma da za a yi tsokaci kan su da ɗai-ɗai yanzu.

    1. Kwarzanta waƙa

    Kwarzanta waƙa yana nufin yi wa waƙa kwalliya. Wato maganar da ke a cikin waƙa ta kasance da ƙawa da birgewa, a taƙaice cikin kwalliya. Ta zamo da ado mai burgewa, son kowa kuma ƙin wanda ya rasa-ko kuma a ce sha’awar kowa surutun marashin kunnuwan sauraren waƙa.

    Salo ne zai sanya wa saƙo kalmomi masu kyawo da daɗI da garɗI da zaƙi, wato waɗanda suka fi dacewa da shi, cikin jumloli masu kyakkyawar saƙa da ɗaukar hankali da idon zuciya, sannan kuma ya sako saƙon ta yadda fahimta ba za ta kure shi ba.

    Za a fara da kawo saƙo a cikin zube sannan a kawo yadda mawaƙi ya kwarzanta shi. Idan aka yi haka za a ga cewa saƙon tsirara yake cikin zube duk kuwa da cewa an yi ƙoƙarin suturta shi. Ga saƙon.

    Cikin zube:

    Waɗɗara ya’e! Ga gwarzon da ya gagari gwaraje tun ba su kara ba! Maza in da mai son gwadawa wai don a san da shi. Ga fa aminin Yari, mutumen Majidaɗi! Ga shi nan ba a ɓoye yake ba.

     

    Yanzu kuma ga saƙon a cikin waƙa tare da kwalliyarsa cikin waƙa.

    Zaki watce gumin mafarauta,

    Wadda yar riga yai gumza yan nisa,

    Ko guda bai tsaya mai ba

    Ga giwa ga hili tsakak karkara

    Mahalba ina masu son suna

     

    Gagarau mai shirin daga

    Na Yari gagon Majidaɗi.

     (Alhaji Musa Ɗanƙwairo: Gagarau Mai Shirin Daga)

     

    Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi amfani da salo domin ya yi wa saƙonsa kwalliyar da ta dace da shi. Ya zaɓo kalmomi sannan ya tsara su ya kuma sanya su cikin jumlolin da suka tsara tunani daki-daki. Kalmomi kamr /watce/ (watse) da /gumi/ da /mafarauta/ da /gumza/ da /gago/ da yankin jumla kamar /tsakak karkara/ da /yan nisa/ da /ga hili/, duk cike suke da kaifin da zurfafan ma’anoni ta yadda nan take za a ga siffar tauraron saƙon a idon zuciya. Watse abu yana ɗauke da tunanin cewa mai aikata watsewar bai saunar yin haka, sannan kuma da gaske yake yi ba da wargi ba. Furta kalmar ‘gumza’ ma tattare take da ƙarfi, ba lahe-lahe ba. Wannan shi ke kawo mana tunanin ƙasaita da shirya ma yin karo ko da wa, ba tare da waswasin kasawa ba. Ita kuwa kalmar ‘gago’ sat guda sai ta kawo hoton mutumin da Hausawa kan kira tsayayye.

    To kuma sai Ɗanƙwairo ya danganta kalmar ‘watse’ da ‘gumi’ da kuma ‘mafarauta’ domin ya ƙirƙiro mana hoton firgitattun mutanen da saboda firgita ba su ko kula da taronsu da ƙarfin yawansu da akan ce ya fi taron ƙarfi ba!

    Lura da cewa kalmar ‘gumi’ tana iya ɗaukar ma’anar taron mutane ko abinci. Amma a nan maganar Ɗanƙwairo ta fi dacewa da manufar cewa wannan mutum kai tsaye zai watse taron firgitattun abokan hamayyarsa. Wannan taro kuwa ba ƙarami ba ne. Taro ne na gaggan abokan hamayya. To amma ba a kan kome suke ba ga wannan zaki, wato ‘Yandoto Aliyu. Muna iya cewa yadda guguwa kan watse tarin takardu ko auduga haka wannan zaki kan yi da wanann gumin mafarauta.

    Furucin ‘tsakak karkara’ yana zayyana faffaɗan wuri mai ka da gaban wanda abokan gaba suka tare babu wurin gudu ko damar samun ceto. Shi kuwa yankin jumla, ‘yan nisa’ da Ɗanƙwairo ya danganta da ‘yai gumza’, jaddada niyyar wanda ya yi gumzar yake yi. Yankin jumla, ‘ga hili’ (ga fili), shi ne ya fara kawo hoton marashin mataimaki a faffaɗan wurin da ake da magauta. Wannan yankin jumla shi ne ‘tsakak karkara’ - ya ƙara fitowa da shi a sarari.

    Duk wannan tarin bayani fa ya tusgo a sakamakon kalmomin da Ɗanƙwairo ya zaɓo wa saƙonsa ne. To, ko bayan haka mawaƙin ya yi amfani da salon kinaya domin ya fito da hoton tauraron saƙonsa. Ya kira tauraron da cewa zaki ne da ke gumza sannan kuma giwa ne. Tunanin da kan zo ma masu sauraren Ɗanƙwairo, wato Hausawa, idan aka furta kalmar zaki shi ne, majiyin ƙarfi wanda bai da tsoro ko kasawa, kuma wanda babu mai iya karo da shi. Wannan tunani game da zaki shi ke wullawa zuwa ga tauraron saƙon waƙa daga wajen mai saurare. Ita kuwa kalmar gumza da kinayar zaki ke ɗauke da ita takan kawo wa Bahaushe sauti ko ƙarar ƙasaita a cikin tunaninsa, kuma wannan ƙarar ta zaki ce ba ta kowa ba. Ba ɗaya take da gurnani ba wanda shi kuwa sauti ne na damisa wadda ke neman ta tsoratar saboda tana da niyyar kai hari. Ɗanƙwairo ya yi kinaya da giwa, kalmar da kan kawo wa Bahaushe tunanin abu mai cika ido saboda girmansa.

    Akwai kuma wasu kalmomi kamar ‘mahalba’ da ‘gagarau’ da kuma yankin jumlar ‘masu son suna’, waɗanda su ma Ɗanƙwairo ya kawo su cikin salo domin saƙonsa ya samu kwalliya. Bayan da ya ambaci giwa don ta yi kinaya ga tauraron saƙon ta fuskar kasancewa mai cika ido, sai Ɗanƙwairo ya kira maharba ba tare da ware ko ɗaya daga cikinsu ba. Wato da waɗanda gwanaye ne su, da masu bi musu balle waɗanda suke bamaye (jam’in bami), duk su zo, ga fili ga mai doki. Me Ɗanƙwairo ya ce da su? Ai ta amfani da salon tambaya ne ya ba su albishir da cewa idan dai har akwai wani daga cikinsu wanda ke son sunansa ya gira, to ga ranar ta zo domin ga giwa tauraron saƙon nan a fili ba a ɓoye ba.

    Lura da cewa a nan inda Ɗanƙwairo ke kiran maharba, ya yi amfani da salon yin magana kai tsaye da su ne, ba da masu saurare yake yi ba. maganarsa.

    Albishirin da mawaƙin ya yi wa maharba, ba a’a ce yake yi musu. Wannan ba’a tana ƙunshe cikin kalmar ‘gagarau’ da Ɗanƙwairo ya siffanta tauraronsa da ita. Wannan fahimta ke sanya a tsaya a yi tambaya kamar: Anya kuwa Ɗanƙwairo ba iza-mai-kantu-ruwa ba ne yake yi wa waɗannan maharba? Amsa kuwa ita ce, lalle iza-mai-kantu ne ya yi musu. Wato dai Ɗanƙwairo ya yi amfani da wani salo da za a iya a kira ‘salon ba’a’ domin ya yi wa saƙonsa kwalliya.

    A bayyane take cewa salo ne Ɗanƙwairo ya yi amfani da shi ya ƙawata saƙon waƙarsa har ya kasance ana iya ganin mutanen da aka ambata cikin waƙar, wato da tauraro (a nan ‘Yandoto Tsafe Aliyu ke nan) da mafarauta da mahalba (su kuma a nan masu neman sarautar Tsafe kuma masu adawa da ‘Yandoto ke nan). Ana iya ganin waɗannan mutane da idon zuciya, kuma kowane da irin tasa sifa da ƙira da haliyya waɗanda Ɗanƙwairo ya ba su. Ire-iren salon da Ɗanƙwairo ya yi amfani da su sun haɗa da kinaya da dabbantarwa da bi-ma’ana. Sauran su ne salon tambaya da salon ba’a da kuma na ba shamaki, wato magana kai tsaye ba wani tsakani.

    Waɗannan kaɗan ne daga salailan da Ɗanƙwairo ya sa cikin ɗan/baitin da aka tsakuro, sai dai su ne muhimmai ta fuskar kwarzanta saƙo.

    2. Isar Da Saƙo

    Isar da saƙo a cikin waƙa yana nufin mai saurare ya fahimci jigon waƙar, ya kuma samu tasiri a cikin haliyyarsa daga kalmomin da aka yi amfani da su cikin waƙar. Wannan tasiri kan haliyya na iya kasancewa ko dai mai saurare ya samu haliyya irin wadda mai waƙar ya shiga, ko ta yi kusa da ta mawaƙin ko kuma ta zamo wadda mawaƙin ke bukatar mai sauraren ya shiga. Haka kuma takan kasance tasirin ya haifar da haliyya a cikin mai saurare wadda sam ba ta cikin waɗannan da aka ambata. Haliyya dai ce da kalmomin waƙar suka haifar.

    Alƙali Alhaji Haliru Wurno yana faɗa wa ƙanensa, Alhaji Bello, irin matsallar da ya shiga, yana cewa:

    1. Yi zafi tafi kai iske ƙanen naka da kanka

    Faɗa mai bari shakkar ka faɗa mai maganakka

    Ta motakka da taf faɗi da kyar kaf fita kanka,

    Faɗa mai haɗari wanda ya faɗa bisa kanka,

    Ji ta ɓaci ƙwarai yanzu zama ba ta ɗagawa.

     

    2. Yi dai Gande wajen Bello ƙane don ka faɗa mai,

    Zama ba ka da ƙarfin da kakai ban da faɗa mai

    Ga kwaltammu ta can Wurno ta juyo bisa kainai

    Mutanenmu da kukansu tuli nan bisa kainai

    Tsarin Jalla Guda yah hana yayanka macewa.

     

    3. Da tab birkita taw wakita taƙ ƙara zubewa,

    Da tam mazaya tak karkata tak koma jicewa,

    Da taw wantsala tam mulmula nif fara ɗimewa

    Da nif firgita nit tsorata kaina ka kaɗawa,

    Malakul mautu ga sannan nika hange da isowa.

     

    4. Ina kwance tana nan bisa taro bisa kanmu,

    Da manyansu da yaransu da kyar sunka cire mu,

    Gani na haka can kwance kamar za ta kashe mu

    Duhu nata ƙaruffanta kujeri ka jice mu

    Da saura na ka sha ma’u dalilinka fitowa.

     

    5. Na zabura na jirkita na koma ɗimewa,

    Ban gane gabas yamma bale dama arewa,

    Ji kaina ka ta motsi katarata ka kaɗawa,

    Idona ka hawaye ciki ƙalbi ka bugawa,

    Ganin na aza guri cike raina ka tunawa.

     

    6. Ina nan tsaye na yamutsa kowa ka wucewa,

    Ban gane fari dud da baƙin masu shigewa,

    Ɗumin nan da akai ban iya amsa da mayarwa,

    Ganin ba kariya ga ni jinni ba shi zubowa

    Allahu kiyaye gaba kowa ka faɗowa.

     (Alƙali Haliru Wurno: Babban Bajini/Yabon Bello Yahya Sakatare)

     

    Saƙon da ke ƙumshe cikin waɗannan baitoci shi ne:

    Ya kai ƙanena Bello ga ni na zo in faɗa ma matsalar da ta same ni duk kuwa da cewa da farko na ji nauyin in zaka. To amma tilas in faɗa ma don shi kaɗai nake iyawa. Haƙiƙa na yi fitar kutsu. Allah dai ya nufi ina da rabon ganin gaba. Mummunar faɗuwa motata ta yi. Yanzu haka ba ta ɗagawa ko’ina. Ni da kake gani a nan sai da aka ƙwato ni daga cikin ƙarafanta. Mutane sai faɗin sukai Allah ya kiyayya gaba. Ni kuwa ga ni zugun na giɗime, ban san abin da ake yi ko faɗi ba

    Wannan shi ne saƙon da ke cikin baitocin, amma shi Haliru Wurno yana bukatar mai saurare ya gani da idanun zuciyarsa da kansa, ya kuma ji da kansa duk abubuwan da suka gudana game da haɗarin. Kama tun daga faɗi-tashin da motar ta yi da birkice-birkicen da ta yi, har zuwa danne su Haliru da ƙarafanta da kujeri suka yi, da agajin da mutane suka kawo har zuwa irin tunanin da shi Haliru ya shiga yi, da kuma yadda ya kasa ima jikinsa bayan an fitar da shi. Kai hatta da ƙulle-ƙullen da zuciyarsa ta shiga yi game da ko ya tafi ko kuma kar ya tafi, duk waɗannan abubuwa suna cikin abin da Haliru yake bukatar mai saurare ko karatun waƙarsa ya ji ya kuma gani da kansa. Duk kuwa waɗannan zuciyar mai saurare da tunaninsa za su aiwatar ne.

    Abin da kuwa zai yi wa Haliru wannan aiki shi ne salo. Domin mai saurare ya mai da hankali ga saƙon baitocin sai Haliru ya fara amfani da salon jinkirtawa. Shi bai faɗi saƙonsa ba, shi kuma bai ƙi yin magana ba, dubi jinkirtawar:

    Yi zafi tafi kai iske ƙanen da kanka,

    Faɗa mai bari shakkar ka faɗa mai maganakka.

     

    Haliru bai faɗi saƙon ba a nan amma ya yi nasara ga jan hankalin mai saurare zuwa gare shi ta wajen amfani da salon jinkirtawa wanda aka saƙa da salon maimaitawa. Da /yi zafi tafi/ da /iske/, duk suna bayyana yin tafiya. Haka kuma Haliru ya maimaita kalmar faɗa. Duk waɗannan suna ƙarfafa cewa lalle Haliru yana da muhimmin saƙo zuwa ga mai sauraren sa. To amma kuma har ila yau waɗannan salailai sun taimaka ga bayyana mana irin ƙullawa da kwancewa da Haliru ya riƙa yi. Ya je wajen ƙanensa ko kuma a’a kar ya je? Ya je ya faɗa wa ƙanensa labarin matsalarsa ko kuma kar ya je ya faɗa?

    Sai a ɗango na uku ne Haliru ya fara ambaton muhimmin saƙon waƙar, wato haɗarin da ya yi da motarsa wanda kuma da kyar ya samu ya kuɓuta. To amma har yanzu Haliru bai daina amfani da salon jinkirtawa ba. Hasali ana iya cewa finto saƙon ne Haliru ya yi a cikin baiti na farko. Fincen kuwa shi ne ‘motata ta faɗi da ni cikinta, ni dai da kyar na fita, ita kuwa motar a halin yanzu ba ta zuwa ko’ina’. Ina ne Haliru ya samu haɗarin? Yaya haɗarin ya auku? Ta yaya za a san cewa Haliru da kyar ya fita? Da wa da wane ne suka kawo masa gudummuwa? Mene ne dalilin nauyin da Haliru yake ji ga faɗa wa ƙanensa labarin wannan haɗari? Duk waɗannan tambayoyi Haliru bai kawo amshoshinsu ba sai a baiti na biyu da waɗanda suka biyo bayansa. A baiti na biyun ma sai da ya ƙara yin jinkirin faɗin saƙon, domin kuwa a ɗango na ɗaya maimaita maganar tafiya zuwa ga ƙanensa ya yi. Wannan kuwa ya gyara mana zukata ne domin karɓar dalilinsa na yanke shawarar tafiya inda ƙanensa. Dalilin kuwa shi ne cewa Haliru bai da ƙarfin da zai iya yi wa kansa kome, saboda haka ba laifi ba ne idan ya je ya faɗa wa ƙanensa domin ya taimaka masa. Da yana da ƙarfin yi wa kansa wani abu, da sai ya yi ɗin sannan zai faɗa wa ƙanen, kuma da bai ji nauyin faɗin ba.

    A ɗango na uku zuwa na biyar na baiti na biyu ne Haliru ya ba da amsar tambayar da aka yi ta, a ina haɗarin ya auku da kuma ta su wane ne suka kawo gudummuwa. Haka kuma ya ƙara maimaita cewa da kyar ya fita. Wato dai har zuwa ƙarshen baiti na biyu Haliru ya yi ta amfani da salon jinkirtawa da na maimaitawa. Wannan kuma duk domin ya cusa mana muhimmancin saƙon da zai zo a sauran baitoci ne. Wato haɗarin motarsa da fitar kutsu ɗin da ya yi. Shi kuwa wannan saƙon, Haliru ya kawo shi ne a cikin ɗango na uku. Haliru ya kawo shi ne cikin salon zayyana.

    Ba sat guda motar Haliru ta faɗi ba. A cikin ɗango uku Haliru ya faɗi abubuwan da motarsa ta yi kamin ta zamo abin da ya faɗa mana a baitocin da suka gabata, kuma sun kai takwas: ta birkice, ta wakita sannan kuma ta zube kamar sarƙa. Daga nan kuma sai ta mazaya kana ta karkata ta kife (jice). Amma kuma bayan ta yi hakan sai ta wantsala kamar yara suna lambe, amma ita daga nan mulmulawa ta yi kamar ‘yan wasan tsalle.

    Yadda Haliru ya kawo abubuwan nan takwas da motarsa ta yi cikin ɗangogi uku rak ya nuna mana ɗan taƙaitaccen lokacin da motar ta ɗauka ga yin su. Duk kuwa ya zaɓo kalmomin da ke yin ishara ne ga ma’anoninsu. Wato bi ma’ana. Wannan zaɓe shi ya zayyana mana yamutsi da tashin hankalin da motar ta yi ta kuma sa Haliru ciki. Hasali muna iya hango idon Haliru sun yi turu-turu. Ga firgita ga tsoro ga kuma rashin sanin mafita ko makama. Haƙiƙa bai cikin hayyacinsa. Bai tare da mutanen duniya. Kai shi mala’ikin mutuwa kawai yake gani ya zo don ya ɗauki ransa!

    A cikin irin wannan hali na tashin hankali da mutuwa-bisimilla-na-saki-kari ne mutane suka kawo agaji. A nan ma sai da Haliru ya ci gaba da amfani da salon zayyana ya nuna mana yanayin shi gashi kwance mota tana a kan sa, sannan ga taro a kan su da shi da motar. Ma’ana dai ita ce motar ce ake iya gani ba Haliru da abokan tafiyarsa ba. Taron mutane kuwa ya haɗa da manya da yara amma fa da kyar suka samu ƙwato su Haliru daga dannewar da motar ta yi musu.

    Yaya motar ta yi wa su Haliru? Su Haliru sun kasance cikin duhu. Shi kaɗai suke gani domin ko bayan duhun motar, ƙarafanta da kujerinta waɗanda su Haliru suke a kai kamin haɗarin, yanzu duk sun jice su. Ga su nan danne sauran ƙiris motar ta kashe su. Abin da kakwai ya hana Haliru ya mutu shi ne fitar da shi da aka yi daga wannan hali. Yadda ma Haliru ya faɗi wannan kuruwa ko fitar kutsu da ya yi, wato ɗango na biyar na baiti na huɗu ana iya ɗaukar ta tamkar ajiyar zuciya ce Haliru ya yi. Bayan duk ya zayyana yamutsin da motar ta yi da kuma uƙubar da shi Haliru da abokan tafiyarsa suka sha, sannan a yayin da yake hangen mutuwa ga fili, mutane suka zo suka ƙwato shi daga ƙarƙashin ƙarafan motar, sannan Haliru ya yi ajiyar zuciya:

    Da saura na ka sha ma’u dalilinka fitowa

    Wannan amfani da salon zayyana ya ci gaba a baiti na biyar da na shidda. A nan ne Haliru ya kawo hotonsa na biyu. A can baya hotonsa na cikin mota ya kawo. A yanzu kuwa yadda ya kasance ne bayan an fitar da shi daga cikin ƙarafan mota. Ga shi nan bai ima kansa. Ya yi ƙoƙarin ya tashi tsaye amma ina? Yunƙurawar da ƙarfi ya yi ta alhali kuwa jikinsa bai jimirin wannan. Nan take sai jiri ya kwashe shi ya jirkice. Nan da na giɗimewarsa ta komo. Ina ne gabas ko yamma, ina ne kuma kudu ko arewa? Duk bai sani ba. Har yanzu kan Haliru bai daina rawa ba saboda firgita. Ƙari ma shi ne katarsa da ke kaɗawa, ga kuma hawaye na tarara. Bisa ga dukkan alamu waɗannan hawaye na fitar kutsu ne ba na raɗaɗi ba. Zuciyar Haliru ita kanta ba a hankali take bugawa ba.

    Zayyanar ba ta tsaya a nan ba. Irin wannan hali da Haliru ya shiga yakan sa ran mutum yin tunani iri-iri. Ran Haliru bai da lafiya. Ina ban da wannan tunani na dogon guri da yake da tun gabanin wannan haɗari da ya yamutsa gurin, Haliru bai gane kome, bai jin kome kuma bai iya yin kome. Su kuwa mutanen da suka ga Haliru bai samu wani babban rauni ba, babu kariya, kuma babu tsiyayar jini daga jikinsa, sai suka ɗora yi masa fata da addu’ar Allah ya kiyaye gaba.

    Duk wanda ya ji ko ya karanta waɗanann baitoci bai rasa ganin hoton kai-kawo da faɗi-tashin da motar Haliru ta yi, da kuma irin firgita da uƙubar da shi Haliru ya shiga ciki. Mutum ba zai rasa ji a zuciyarsa irin yadda Haliru ya ji ya gani ba. Wannan kuwa ya samu ne a sakamakon amfanin da Haliru ya yi da salon zayyana da na jinkirtarwa da na zaɓen kalmomi bi-ma’ana, kai har ma da amfani da wani harshe, wato Larabci, a wuraren da suka dace, da kuma salon maimai domin saƙa salon jinkirtawa.

    3. Bambancin Mawaƙi

    Salo tambarin mawaƙi ne. Shi ke bambanta wannan mawaƙi da wancan. Kowane mawaƙi yana da wata ɗabi’a ta karkata zuwa ga amfani da wani nau’i na salo a cikin waƙoƙinsa. Akan lura da cewa wannan mawaƙi yakan yi amfani da salon ban dariya a kai a kai a cikin waƙoƙinsa, a yayin da wancan shi ko ya fi karkata ga yin amfani da salon tambaya. Wani kuwa duk da yana amfani da salon tambaya sai ka tarar ya fi karkata ga yin tambayoyin tare da amsoshinsu. Haka kuma a waƙoƙin wani mawaƙi sai ka tarar cike suke da kalmomin bi-ma’ana da na bi-amo. A waƙar wani kuwa salon siffantawa ne asirinsu. Haka abin yake tafiya

    A kan wannan lura ce ake cewa salo yana da muhimmanci domin shi ke fitar da mawaƙi daga sauran mawaƙa. Naƙaltar salon da mawaƙi ya fi amfani da shi kan taimaka wa manazarci wajen tantancewa da sahihancin waƙar da ke a gabansa. Haka kuma naƙaltar salon mawaƙi kan taimaka wajen fahimtar waƙoƙinsa. Duk da yake an san cewa da Ibrahim Narambaɗa da Musa Ɗanƙwairo duk mawaƙan fada ne, ba za a rasa lura da cewa yayin da Narambaɗa ya fi karkata ga cusa maganganun hikima, dangane da halin rayuwa, shi Ɗanƙwairo sai ya karkata ga amfani da ban dariya da kuma kalmomi ko maganganu masu tsima mutum ko shammatar sa.

    A waƙar da aka tsakuro baitocinta ɗazu, Haliru Wurno ya ci gaba da cewa:

    Shi radiyo na samu gani nai da fitowa

    Ji jikkanmu da kuɗɗinmu ga wa za mu biɗowa

    Mutum ya hi ɗari uku ina za mu ɗumawa

    Da lemunmu abarbammu guda ba ka biɗowa

     Bale magauro ya nakkasa har shi ga fashewa

     (Alƙali Haliru Wurno: Babban Bajini/Yabon Bello Yahya Sakatare)

     

    Wanda fa ya yi fitar kutsu ne nan yake batun radiyonsu! Wanda fa ya cusa mana tausayi a zukatanmu ne ga batun ƙarafan mota sun danne shi, yana ganin mutuwa a fili, wanda kuma ya bayyana mana gaba ta koma baya, magaji da roƙon ƙane, shi ne nan ya dawo bayan ya zayyana mana artabun da mota ta yi da shi, da kyat ya kuɓuta, shi ne yanzu ke batun radiyonsa da lemunsa da magauronsa! Shi ke batun kuɗi, duk da yake ya san ba su samuwa a wannan hali. Haƙiƙa a nan Haliru yana ƙoƙarin ya sa raha ne a cikin waƙarsa kamar yadda yakan yi a sauran waƙoƙinsa. Dubi wani misali:

    Don na ƙyale suka son taki na

    Don sun mame ni cikin dangina

    Sun haƙa gurunsu a kan hanyana

    Wanga da ab baya shina kaɗi na

    In hasale in shiga ban ganewa

     

    Bai san na gane nufin ɗan Bargu

    Ƙaton kolon ga abokin burgu

    Ɗan baubawa ba shi faɗin zangu

    To na shirya ni aɗ ɗan Dusgu

    Kwai mai kirɓinsa ina damawa

     (Alƙali Haliru Wurno: To Bisimilakku Ina Karɓawa)

     

    Bayan da Haliru ya nuna ba zai yi fushi ba saboda makircin maƙiya don gudun ya afka cikin haɗarin da ba zai iya kuɓuta ba, sai ga shi a cikin baiti mai bin wannan ya hasala har da yi wa kansa kirari tare kuma da ƙalubalantar maƙiyan. Wato wai shi ne ɗa ga babansa, Dusgu, kuma duk wanda ya yi masa kan kara zai yi masa na itace! Wannan baiti na (18) cike yake da raha musamman idan aka nasarta yadda kalmomin da ke cikin baitin suka nuno Haliru yana yi wa kansa kirari yana buga tafin hannunsa a ban ɗaya, watakila ma har da marin katarsa kamar yadda mata kan yi!

     

    Ga wani misali:

    Rabbana kai ad da iko

    Kai ka baiwa babu tsaiko

    Dauri can ni ba ni biko

    Yanzu na koma adiko

    Mairi don ta kama kaina.

     (Alƙali Haliru Wurno: Soyayya Ruwan Zuma)

     

    Ba wai karya ƙa’idarsa ta fita batun duk wata mata tasa da ta yi yaji Haliru ya yi ba, ba wai kurum karya ƙa’idarsa ta ƙin zuwa bikon irin wannan mata Haliru ya yi ba, a’a yanzu shi kansa ne ya zamo adikon da ake zuwa bikon da shi! Wato, ga al’ada akan je gidan iyayen matar da ta yi yaji a nemi sasantawa da matar domin ta yarda ta koma ɗakinta. To shi Haliru a da can ba ya tura kowa zuwa gidan iyayen duk wata mata tasa da ta yi yaji. Duk matarsa wadda ta yi yaji sai ya fita batunta. Ya gama da ita. Amma fa duk wannan kafin ya auro Mairi ne. To yau Mairi ta yi yaji sai ƙaƙa? Ai ba ma ta batun aika masu yo masa biko Haliru ke yi ba. Shi ne da kansa, ido a rufe ya tafi!! Tuni ya yi watsi da al’adar aika masu yin biko. Kai hasali ma shi ne adikon matar. Wato duk inda ta sa ƙafa tasa tana nan! Yadda mace a ƙasar Hausa ba ta rabuwa da adiko haka Haliru bai rabuwa da Mairi. Shi ne adikonta! Wannan ita ce rahar da Haliru ya buɗe waƙarsa da ita. Raha mai nuna saiɓi.

    Ba wai a waƙoƙinsa da za a iya kira da sunan waƙoƙin duniyanci ne ba kaɗai Haliru kan yi amfani da salon raha. A waƙoƙinsa na addini ma bai aje raha a gefe ba. Dubi wannan misali:

    Waƙar mutane na yi ga ta a kai a kai

    Wasu na yi zambo sun ji har aike nikai

    Wasu na yaba su suna biɗa aike sukai

    Na rera waƙoƙin sarakai hakimai

     Na ya da saiɓi ‘yan kazagge ka ɗauka

     

    Har masu tebur na yabe su na ƙauyuka

    Har ‘yan farauta masu hira da karnuka

    Matan da nay yi saki cikisnu akwai Juka

    Sannan ga alƙalai da limammai duka

     Waƙarsu na tsara ta mai albarka

     

    In yo yabon wani nan da nan ka ga yai zurum

    In tona halayensa sai ya yi langadam

    Kuma zan yi kushen al’amurran ɗan Adam

    Na kai iyaka can ga shammatar mutum

     Wani bi ina zambo lakan in soka

     

    An ba ni boya Ba’u har na saisuwa

    An ba ni takalma gami da buhuhuwa

    Shi kam yabo na yo shi har da na saisuwa

    Na samu kurɗi har da riga zannuwa

     Na samu kyauta don ganin na bar ka

     (Alƙali Haliru Wurno: Ƙorama)

     

    Waɗannan baitoci sun fito ne daga waƙar Haliru ta yabon Annabi Muhammadu (S.A.W). Wato dai waƙar tana daga cikin rukunin waƙoƙin addini da ake kira waƙoƙin madahu. To amma kasancewar ita waƙar addini ce bai hana Haliru ya saka raha a cikinta ba. Saboda haka ne ya ɗan yada zango ya faɗa mana cewa ya yi wa mutane daban-daban waƙa, daga cikinsu kuwa har da mafarauta waɗanda ya ce sukan yi hira da karnuka! Ya yi wa ‘yan ate, masu sana’a kan tebur, da ‘yan mata da kuma matansa. Sai da ma ya faɗa mana sunan wata matarsa, wato Juka. Wannan labari da aka kawo cikin waɗannan baitoci cushe yake da raha.

    Idan aka koma ga da’awar da aka yi cewa Ibrahim Narambaɗa mawaƙi ne da za a iya cewa fitaccen salonsa shi ne saka maganganun hikima na koyar da rayuwa, wato yakan cusa falsafa a cikin waƙoƙinsa, ana iya a kawo misalai a nan ƙasa don su wadatarmi.

    A waƙarsa da ya yi wa Sarkin Gobir Na Isa Amadu Bawa I, mai suna Gogarman Tudu, Narambaɗa ya ce:

    Shiri gama aiki na Dodo

    Ƙi fasawa Amadu wan Sardauna

    Ruwa da kada baban Mandele

    Baban shamaki manyan daga

     (Ibrahim Narambaɗa: Gogarman Tudu)

     

    A ɗango na ɗaya Narambaɗa ya ba mu wani muhimmin makamin rayuwa. Kome yawan aiki, kome wuyar aiki, maganinsa shi ne mutum ya shirya masa. Rashin yin shiri shi ke haifar da dagulewar al’ammura. Rashin shirya yadda za a fito wa aiki shi ke haifar da rashin kammala shi cikin lokaci.

    To irin wannan kalami na hikima shi ake nufi da cewa Narambaɗa ya siffanta da salon sanya maganganun hikima a cikin waƙoƙinsa. A gaba kaɗan cikin ɗan waƙar na biyu za a iya lura da irin wanann salo aƙalla sau huɗu:

    Ai sarauta ban da nufin Allah ce

    Da ɗibat ta akan yi da ƙarfi

    Waɗanga da nag gaza ganewa

    Da sun ga

    Ana haka nan da sun yi

    Ku dangana tun ga uwaye

    Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki

    Wane ku dangana tun ga uwaye

    Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki

    Ɗan sarki duka yag ga sarauta

    Ga ta kamak kusa tai mashi nisa

    In dai bai yi sarautan nan ba

    Sai ya tusfa da mikin zucci

    Ɗan sarki duka ab ba kowa

    Ɗan sarki duka ab ba komi

    Sannan yat tsira yawon ƙarya

    Ya san ba ya sarauta

    Sai fa ya kwam nan

    Gobe ya kwan nan jibi

    Dangi nai mashi Allah waddai

    Baƙam magana ba ɓaci ta ba

    Amma ta ɗara ɓaci zafi[19]

     (Ibrahim Narambaɗa: Gogarman Tudu)

     

    Maganganun Hikima da ke cikin wannan baiti su ne:

    1. A ɗango na ɗaya da na biyu, Narambaɗa yana faɗin cewa samun zama sarki abu ne daga Allah kuma saboda zamowar sarauta haka shi ya sa Bahaushe bai neman ta da ƙarfi. Wannan imani da Bahaushe ya yi na zaman sarauta kyutar Allah Maɗaukaki shi ke hana shi amfani da ƙarfi domin ya same ta. Sai fa a wannan zamani da ake mulkin soja. Duk da haka kuwa maganar Narambaɗa ba ta kau ba domin shi Bahaushe sarautarsa ta gargajiya yake nufi kuma ita ce Narambaɗa yake nufi. Har ila yau sarauta ce wadda aka shimfiɗa a kan tafarkin addinin Musulunci.

    2. A ɗango na 6 zuwa na 7, Narambaɗa ya gabatar mana da wata farar gaskiya, cewa duk da yake a ƙasar Hausa a kwana a tashi ɗan sarki ne kan zama sarki, wannan bai zama hujja ga a ce kowane ɗan sarki zai zamo sarki ba. Tarihi ya nuna mana cewa waɗansu ‘ya’yan sarauta kan gama rayuwarsu amma sarautar da suka gada ba ta faɗi ba balle su neme ta. Ko bayan wannan ma ai sarki guda tal akan yi a zamani guda.

    3. To sai kuma a ɗango na 10 zuwa na 13 inda Narambaɗa ya ba mu labarin yadda ɗan sarki ke ji a ransa idan bai samu zama sarki ba, bayan kuwa ya ga alamomin samun ta. Misali a ce an ba shi muƙamin yarima ko kuma malaman tsibbu sun tabbatar masa ita cewa shi zai gadi mahaifinsa ko wanda ke ci a lokacin. To, a faɗar Narambaɗa irin wannan ɗan sarki idan bai samu sarautar ba haƙiƙa yana cike da baƙin ciki dare da rana.

    4. Duk ɗan sarkin da bai aje ba, bai kuma ba wani ajiya ba, sannan ga shi ba wata sarauta ko matsayi ne yake da ba, ya ɗauki ɗabi’ar yawon banza yana ƙarairai wato yana cutar talakawa ko yana yawon raraka, a ganin Narambaɗa wannan ɗan sarki ba zai zamo sarki ba a ƙasar Hausa. Dalili kuwa shi ne ya ɗauki halayen da Bahaushe bai amince basarakensa ya zamo yana da su ba. Wannan shi ne abin da ɗango na 15 zuwa na 17 suka ƙunsa.

    5. Baƙar magana ta fi zagi ciwo, in ji Narambaɗa. Wannan wata irin lura ce Narambaɗa ya yi game da maganganun ɗan Adam. Shi dai zagi ga al’ada mutum biyu ke yi wa juna shi, kuma a fahimtar Bahaushe wanda duk ya ziga wani to iyayensa ya rena domin zagin su za a yi! To, amma baƙar magana fa? Takan zo ma wanda aka yi wa ita cikin ba-zata. Wanda aka yi wa ita bai sa ran za a yi masa ita. A dalilin haka ne a koyaushe aka yi wa mutum baƙar magana yake ba a shirye ba, balle ya rama. Kuma a kan haka ne baƙar magana ta fi zagi ciwo domin babu wanda aka rena sai wanda aka yi wa ita. Wanann shi ne ke cikin ɗango na 21 zuwa 22.

    Wannan shi ne abin da ake nufi da cewa salo yakan bambanta wannan mawaƙI da wancan. Za a tarar da cewa duk da yake mawaƙi kan yi amfani da salailai da yawa cikin waƙoƙinsa, akwai wani salo guda ko jumlar wasu salailai da suka fi yin fice cikin waƙoƙin nasa. Samuwar haka kuwa ita ke bambanta wannan mawaƙi da sauran mawaƙa. To amma ya kamata a jadadda cewa bai kyautuwa manazarci ya yi wa mawaƙi hukunci kan kyawo ko rashin kyawon waƙarsa ta ɓangaren salo a dalilin salon da ya bambanta shi da sauran mawaƙa. Dalili kuwa shi ne ai akwai sauran salailai a cikin waƙar mawaƙin waɗanda ke da muhimmanci kamar wancan ɗin. Kar mu rufe ido ga sauran salailansa.

    4. Bambanta Waƙa Ko Ɓangaren Waƙoƙi

    Abin da kamar wuya, rarrabe muhimmancin salo ta fuskar bambanta mawaƙi da kuma ta fuskar bambanta waƙa. Dalili kuwa shi ne idan aka tsaya tsaf aka duba sai a tarar da cewa a mafi yawan lokuta mawaƙi yakan yi zaɓen salo ne ta la’akari da irin waƙar da yake son ya tsara. Wato waƙa ko ɓangaren waƙoƙi kan taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen salon da zai tsara su. Salon da waƙoƙin addini, kamar na madahu, za su ƙunsa babu shakka zai bambanta da wanda waƙoƙin duniyanci kamar na fada za su ƙunsa. Haka kuwa ya kasance ne duk da cewa waƙoƙin madahu da na fada sukan yi tarayya da waɗansu muhimman ƙananan jigogi kamar yabo da bayyana fifiko.

    Tattare da wannan lura za a taƙaita bayani a wanann ɓangare kan muhimmancin salo ta fuskar bambanta waƙa ko waƙoƙi, domin kuwa abubuwan da aka riga aka ambata a ɓangaren da ya gabata, wato bambanta mawaƙi, masu dacewa ne da wanann ɓangare na bambanta waƙa

    Wani ɓangaren waƙoƙi ya fi ɗaukar wani salo, ko mu ce an fi yin amfani da wani salo a cikin ɓangaren bisa ga wani ɓangare daban. Alal misali a cikin waƙoƙin fada za ka tarar da cewa nau’o’in salon siffantawa na kinaya da na jinsarwa da kuma na alamtarwa sun fi yin fice bisa ga sauran nau’o’in siffantawa da kuma waɗansu salailai.

    Mu ɗauki nau’in kinaya ga misali. A cikin waƙar da Alhaji Ɗanƙwairo ya yi wa ‘Yandoto Aliyu akwai waɗannan kinayoyi:

    A. Gizago ba ka da sabo wandara

    Gamda’aren ‘yan waire tsayayye

     

    B. Guru ba ka da daɗin taki

    Kowat takai sai yai raki

    Yanzu ka iske miki ga farcenai

     

    C. Gulbi ya cika ya ba daji

    Sai wawa sai baƙo

    Kowas shiga ya ɓace ba ya tasowa

     

    D. Alu namijin zuma mai wuyac cima

    Kowah hi ka harbi shi sha kainai

     

    E. Zarto kake mai ciwon yanka

     

    F. Ali bindiga mai zahin tashi

    Maza da shirinka koyaushe tas samu

     (Alhaji Musa Ɗanƙwairo: Shirya Kayan Faɗa)

    A waƙar Salihu Jankiɗi wadda ya wa Sarkin Musulmi Abubakar na III akwai waɗannan kinayoyi:

    A. Fitila mai korewat duhu

    Sabulu mai wanke dauɗa

    Abubakar annurin duniuya

     

    B. An san ruwan da akan shiga ai iyo

    Kway yi nuta maliya ba shi ganin waje

     (Salihu Jankiɗi: Shugabanin Ɗakin Duniya)

     

    A wata kuma da ya sake yi wa Sarkin Musulmi ga abin da ya ce:

     

    A. Manyan daji giwa an nan,

    Ruwa ba su yami don banza

    Wanda Mu’azu yai daga ka riƙa

    Halin Shehu shi yay yi Bubakar

     

    B. Wargin da akai ma karen daji

    A kama shi a yi wargi da shiya

    Zaki don bai ɗaukaw wargi.

     (Salihu Jankiɗi: Bajinin Gidan Bello Bubakar)


    Haka kuma za mu lura da cewa a waƙoƙin da Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo, kamin ya zama Sarkin Musulmi (Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III, Sarkin Musulmi na 19), salon kinaya yana fitowa a kai a kai. Misali:

    A. Tanƙwasau na Alhaji Sarkin fada

    Ruwan kashin fari.

     

    B. Bajini ɗan gaggara gasa amalin sarakuna

    Toron giwa ɗan Abdu ƙanen Ali ɗan Iya

     

    C. Gulbi ya ba da ruwa fadama dut ta shahe

    Masu hito has sun fara faɗin yanzu tay yi kai.

     (Sa’idu Faru: Alhaji Macciɗo Jikan Mamman)

     

    D. Baba na shamaki mai hana noma

    Baba ganɗon gabas raba-kaya.

     

    E. Babban daji kake ɗan Abu

    Ko icce ko namun dawa,

    Ko manya ko ‘yan ƙanƙane

    Da mutum da dabba da itatuwa

    Kowa ƙamnam Mamman shikai

    Mamman jikan Attahiru

    Baba na Sidi Mamman gwarzon Cika.

     

    F. Baban mai Abu Faru na Mai’akwai

    Ɗan giwa komi tad daɗe,

    Ta tabbata yin giwa yakai

    In ji sarkin Maradun sarkin Ƙaya

     

    G. Kana shire baban ‘yan ruwa

    Na Bello jikan Ɗanhodiyo

     (Sa’idu Faru: Gardaye Zo Ka yi Man Iso).

     

    A waƙar da ya yi wa Alhaji Sale sarkin Yaƙin Banga na Ƙauran Namoda, Sa’idu Faru bai fasa amfani da wannan salo na kinaya ba. Dubi waɗannan misalai:

    A. Gwabron giwa uban Galadima

    Ɗan Sambo gimshimi

    Gamshiƙan Adamu na Maigandi

     

    B. Jan zakara ya yi ƙiƙiriƙi

    Ya tare garkag gidan ubanai

    Ya bak kwaɗɗo shina cikin rame

    Ya lamƙwashe tsara

     

    C. Zama giwa ta fito kiwo

    Tai miƙa ta zo ta sha ruwa

    Ku ji wai zomo na faɗin

    Faɗa ma su tsari, tsara mu tai gida

    Daji ya ɓaci ka’ a take mutum

    Baƙi a’ akwai ciki

     

    D. Gurnanin damisa ka sa mafarauta

    Su ɗora ɗemuwa

     

    E. Kowane

    Icce shina kamas shi kare

    Dub ban da tsamiya

     (Sa’idu Faru: Ɗan Sambo Gimshimi Gamshiƙan Amadu)

     

    Yanzu da yake mun ga misalai na salon kinaya a waƙoƙin baka na sarauta, bari mu gani idan abin haka yake a takwarorinsu rubutattu

    A waƙar da ya yi wa Alhaji Abubakar Koko Sarkin yaƙin Gwandu, Alhaji Garba Gwandu yana cewa:

    Garba sinadari abin haɗa manyan gadaje

    Zaki zaburo ka kai zama gun mazaje

    Gwarzo garzaya ragargaji gabrin gwaraje

    Alhaji Garba ɗan bani mulki ƙi-garaje

     

    Inda Waziri nij ji swan giwa bai ɓacewa

    Bai da kaman na raƙumi ko a wajen taɓawa

    Giwa du abin da tah haihwa bai ɗimewa

     Duka daji gidansu birni ab bai shigowa

     (Alhaji Garba Gwandu: Yabon Sarki Yaƙin Gwandu)

     

    A wata wadda ya yi wa Makaman Gwandu Alhaji Balarabe, Garba Gwandu ya yi amfani da wannan salon kinaya yana mai cewa:

    In Allah ya ba ka ka girku

    In ko ya hana ka ka tusku

    ‘Ya’yan mulku had da ɗan tunku

    Ba mai so a mai da shi jaku

    Kowa ya fi son zama babba

     (Alhaji Garba Gwandu: Yabon Bajini Ya zama Tilas)

     

    Shi ma Alƙali Alhaji Haliru Wurno a waƙarsa ta yabon Sarkin Musulmi Abubakar III ya saƙa wannan salon kamar haka:

    Ba a so na don na fi son sarki

    Na fi so nai ban bi ma tankarki

    Mai isar banza ba kamar kwaki

    Bai da abki illa cikin baki

    Bai da ɗaki sai guɗɗu tai nata

     

    Ban hita inwa don ganin lema

    Ban sakin ɗunƙule don ganin damma

    Ban barin waina don ganin nama

    Wanda yas shure furad da yad dama

    Ya ga kwano ya iske dussa ta.

     (A.A. H. Wurno: Safiya Da Gaskiya Taka Aiki)

     

    Shi kuwa Alƙali Shehu Alƙanci da ya yi wa Sarkin Musulmi Abubakar III waƙa ga yadda ya tumƙa salon:

    Mun sami sarki wanda yaz zama Garkuwa

    Sarkin Musulmi a uba shi ne uwa

    Babban kwadarko maganin ƙarfin ruwa

    Ya tallaɓe jama’arsa ya riƙe ‘yan uwa

    Ya taimake su wa taimakon Usmanu

     (Alƙali Shehu Alƙanci: Yabon Sarkin Musulmi Abubakar III)

     

    5. Raya Harshe

    A babi na ɗaya an lura da cewa daga cikin tubalan da kan gina salo akwai mallakar kalmomi. Wannan kuwa yana bukatar mawaƙi ya ƙware ga iya zaɓo kalmomin da suka dace da saƙon da waƙarsa za ta ɗauka. Haka kuma an lura cewa ƙirar jumla da nau’o’inta duk suna daga waɗannan tubalai. Ta fuskokinsu ne mawaƙi kan kawo jumloli masu hikima da zalaƙa, wani lokaci ma har ya ƙirƙiro wasu maganganunn hikima sabbi a cikin harshe. Wato dai ko bayan rayar da kalmomi da suka kusa shigewa duhu, salo kan taimaka wajen rayar da harshe ta fuskar ƙirƙiro sabbin maganganun adabi kamar magana.

    Duk da shike abu ne mawuyaci mu tantance ko waɗannan baitoci da ke tafe sabbin maganganun hikima ne ko kuwa sake ƙirar jumlolinsu mawaƙin ya yi, babu shakkar cewa suna a matsayin kyakkyawan misali na yadda salo kan raya harshe. Ko da mun ɗauka cewa da ma akwai karin maganganu a cikin harshen Hausa masu kama da waɗannan baitoci, ba za mu iya kawar da gaskiyar rayar da Hausa da salon baitocin ya yi ba. Ga baitocin:

    Rashi na kore dattako

    Kwaɗai da rashi ka cutawa

     

    Ruwan tabki a jefa kuti

    Ta nuna ta ɗora walawa

     

    Ruwan zafi a kaɗa kuti

    Da ta shiga ba ta motsawa

     

    Ji kai in ka gantai yashe

    Kutunbun ba shi tserewa

     

    Jinin kai na gami da wuya

    Da sun rabu ba su komowa

    Baƙin nan tun da yaƙ ƙuna

    Ka wankai ba shi ɗebewa

     

    Fari shuni ka shafa mai

    Ka sa ruwa shi ka wankewa.

    Kufan so inda yaf fara,

    Ƙiyayya ba ta zamnawa

     

    Ƙiyayya inda taf fara,

    Ku san so ba shi zamnawa.

     (Alƙali Haliru Wurno: Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau)

     

    Idan akwai tababar kasancewar baitocin a matsayin sabbin karin maganganu na Hausa, to ga waɗansu da haƙiƙa sabbi ne saboda samuwar baƙin kalmomi da abubuwan da suka ƙumsa waɗanda Bahaushe bai daɗe da sanin su ba

     

    A. Mota idan ta ƙiya kura akai da ita

    In mas’ala ta yi tsauri sai a sake wata.

     (A.B, Giɗaɗawa: Zuwa Ga ‘Yan Uwa Masu Tunani)

     

    B. Bari son ka rena ƙafarka don motad daɓe

    In ka ga an koro ka nemi wuri laɓe.

     (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Hannunka Mai Sanda).

     

    Haka kuma idan Bahaushe ya daɗe yana furta karin magana mai cewa “Mene ne gamin kifi da kaska” a matsayin tambayar da ba ta da amsa face “babu”, to shi Bello Giɗaɗawa yana da nasa ra’ayi daban domin kuwa ga abin da ya ce:

    Mai ag gamin kifi da kaska anka ce,

    Ce nagge ce tak kai ta cana cikin ruwa.

    (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Baje Kolin Hajar Tunani)

     

    Ana iya kuma shaƙo sansanar karin magana a wanann baiti:

    Shi ko ƙuje ai na ga wari yaf fi so,

    Ƙamshin turare ba shi sa shi ga zakkuwa.

     (A.B. Giɗaɗawa: Baje Kolin Hajjar Tunani)

     

    A fagen waƙoƙin baka ma akan samu irin wannan rawa da salo ke takawa. A cikin waƙar da ya yi wa Nomau, Alhaji Kassu Zurmi yana cewa:

    Haba Nomau,

    Nomau jigon faɗa Karen masu gari

     

    Torankawan tciya uban mai rogo

     

    Ko fatara tai yawa takan zan iko

     (Alhaji Kassu Zurmi: Nomau Na Magarya)

     

    Haka kuma za mu lura da makamanciyar wanann rawa a waƙarsa ta Sale inda yake cewa:

     

    Nic ce to Sale na ga ƙumshi

    Amma a ban cikin kaya

     

    Ina ruwanka da ciki

    Wan’en turamen lailai ne

    Wan’en ko riguna

    Wan’en atanhwa ne

    Kwance su kai ta wasa

    Dud don ka ina ruwanka

    Nic ce had da hwarauhwarauna

     (Alhaji Kassu Zurmi:Sale Bahago Baban Mamman Ɗan Geshe)

    A cikin waƙar da ya yi wa ‘yan taurin Jabanda, musamman kuma tauraronsa Gandau, Kassu ya kawo wata magana mai kama da wadda aka saba ji, wato “Gaskiya mai ɗaci”. Salon waƙarsa shi ya fito mana da ƙira ta daban da wannan karin magana da aka sani. Yadda abin ya kasance shi ne cewa Kassu ya rattaba mana yadda ‘yan taurin Barkeji suka yi ta yi wa ‘yan taurin Jabanda barazana da ta-da-ƙura a cikin kasuwar Dauran. Wannan barazana ta sa har mutanen suka ɗora cewa ‘yan Jabanda sun tsorata da ‘yan Barkeji har suna gudu. A cewar4 Kassu wanann magana zuga ce. Su kuma ‘yan Barkeji sai zugar ta shige su har suka shiga yaba wa junansu. Misali, Bala ɗan Sharu, ya yabi Sharu saboda zagin ‘yan Jabanda da ya yi a cikin kasuwar Dauran.

    Kassu Zurmi ya ci gaba da faɗa mana irin hura hancin da ‘yan Barkeji ke yi har aka samu ɗaya daga cikinsu mai tsinkaya ya faɗakar da su gaskiyar lamari. To amma ina! Sun yi nisa ba su jin kira. Maimakon su saurare shi sai suka mayar masa da baƙa. A nan ne Kassu ya yi tsokaci kan gaskiyar da wannan ɗan uwan ya gaya wa ‘yan uwansa. Wannan tsokaci na Kassu shi ne ya zo da wata sabuwar ƙira ta Gskiya mai ɗaci” cikin waɗannan baitoci:

    An sha ruwa an ƙoshi,

    An takekke

     

    Daɗa hwaɗi banza hwaɗi yohi,

    Sai Bala ɗan Sharu ya ce yau Baba kai muna daɗi

    Gara da kaɓ ɓaci ‘yan Jabanda

    Ashe ko can da biladiful suka cim mu

     

    Sai arne ɗan Sani yac ce a’a

    Ku bam maganan nan

    Ba hwa ita am mazakuta ba

    Daji hwa da kunnuwa da idanu

     

    Sunka ce kai ɗan bura uban mai tsoro

    Mun sa ka cikin waɗan Jabanda

    In tas samu ka ka raga mu

     

    Gaskiya mugunyam magana

    Ba a son ki sai ke tsuhuwa.

     (Alhaji Kassu Zurmi: Jabanda Ɗan Daji Ta)

     

    Shi kuma Alhaji Muhammadu Gambu ya yi amfani da salon kamance ya fito mana da sabuwar ƙirar jumlar da za mu iya mu yi amfani da ita idan muna bukatar bayyana jin daɗin zuciya wanda bai da awa. A waƙar da ya yi wa Inuwa Ɗan Maɗacci, Gambu ya bayyana daɗin da ya ji lokacin da ya sauka a masaukinsu da shi da Inwa, ya kuma tarar da taron ɓarayi da suka hallara domin su yi bai’a ga sabon sarkinsu. Ga dai yadda ya bayyana daɗin

    Da munka jeka majiɗi tun zuwammu

    Nig ga ɓarayi ga su birdit

    An yi naɗin sarkin ɓarayi

    Ni j ji awa na taki Arfa

    Da ba a barin kayan mutane

     (Alhaji Muhammadu Gambu: Inuwa Ɗan Maɗacci

     

    6. Kaifafa Tunani

    Dutci sitin

    Da arba’in ɗai babu

    Jama’a ku lissahwa

    Su ag ga zuri’am Mujaddadi

    Da shi suka jihwam munahuki

     (Alhaji Kassu Zurmi: Bala Babban Bawan Firimiya)

     

    Mene ne Kassu ke nufi da /Dutci sitin/Da arba’in ɗai babu/ a cikin waɗannan ɗangogi? Sanin haka sai ga Musulmi ko wanda yake da sani game da al’adun Musulmi, musamman ta fuskar salla da addu’a da yin salati. Amma wanda bai da wannan sani ba zai yi saurin ɗago cewa carbi ne Kassu ke nufi ba, in ma har ya ɗago.

    Kassu Zurmi ya yi amfani da salon da za mu kira a nan da sunan salon kacici-kacici, wanda babbar manufarsa ita ce ya saka mai saurare ko karatun waƙa cikin zurfin tunani kamin ya gane ainihin saƙon da salon yake ɗauke da shi. Carbi dai ƙodaggai tis’in da tara yake da su domin musulmi ya samu sauƙin yin hailala da hamdala da salati. Waɗannan ƙodaggai (wato, carbin) su ne Kassu ya yi wa kinaya. ‘Ya’yan nan (waɗanda a gargajiyance har ƙodaggan magarya na iya kasancewa su) su ne Kassu ya yi wa kinaya da duwatsu. Kuma a maimakon ya faɗe su a dunƙule, wato tis’in da tara, sai ya rarraba su zuwa sittin da kuma arba’in amma a cire ɗaya daga cikin arba’in ɗin nan. Wannan salo na kacici-kacici wanda aka gina da salon kinaya da kuma salon amfani da tsohuwar Hausa, (cewar da ya yi ‘arba’n ɗai babu’), shi ne ke sanya mutum ya sosa kansa kamin ya gane inda Kassu ya dosa.

    Kassu ya yi amfani da wannan salo domin ya san sai mai kaifin hankali da tunani zai gane manufarsa. Haka a bayyane yake domin mun ji Kassu yana kira ga jama’a da su lissafa. Wato, su natsu domin waɗanann ɗangogi suna bukatar haka.

    Hasali muna kyautata zaton cewa waƙar da waɗannan ɗangogi suka fito cikinta tamkar waƙar siyasa ce mai ɗauke da zuga mai dafi. Wato, muna kyautata zaton cewa Kassu ya yi amfani da waƙar domin ya jefi tsuntsu biyu da dutse guda. Tsutsu na farko shi ne tauraronsa, wato Bala. Tsuntus na biyu kuwa mutanen jihar Arewa ta Nijeriya wadda ba ta jima da rasa shugabanta Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan jihar, ga lokacin da Kassu ya yi wannan waƙa. Waƙar tana zuga ‘yan Arewa ne da su koma ga Allah (ta amfani da addu’a suna jan carbinsu da aka san su da shi) domin su ɗauko fansa daga waɗanda suka kashe musu shugaba (wato sojojin da suka yi bore a shekarar 1966). Muna iya cewa wannan waƙa tana daga cikin musababban kora da kashin da aka yi wa ‘yan ƙabilar Ibo a arewacin Nijeriya da kuma boren da ‘yan Arewa suka yi mai suna Ba-mu-so, duk a shekarar 1966. Bari dai mu tsakuro waƙar da ɗan dama:

    Bala ƙara magani

    Ƙara magani ƙara magani

    Na Gumi

    Tun da akwai ku da yaƙi

    Da ‘yan uba

    Allah shi sauƙaƙe

    Jama’a Allah jiƙan gaba

    An dai yi muna miki

    Ga zucciya

    Saura dangi mu hanƙure

    …..

     

    Allah shi sauƙaƙe jama’a Allah jiƙan gaba

    Mmh!

    Haka Allahu yan nuhwa

    Allah nuhwakka ta

    Bobawa a’a’ yaka gaba da jikan Mujadaddi

    Ba ya ruku’i

    Ya sujjade

    Anne bai iya kalmas shahada ba

    Taro

    Mi nar raba arne da auraki

    Nuhwan mai abummu ta dai

    Haka Allahu yan nuhwa

    Mhm

    Dutci sittin

     

    Da arba’in ɗai babu

    Jama’a ku lissahwa

    Su ag ga zuri’am Mujaddadi

    Da shi suka jihwan manahuki

     

    Dutci sittin da arba’in ɗai babu

     

    Jama’a ku lissahwa

    Su ag ga zuri’am Mujaddadi

    Da su suka jihwam minahuki

    Sai ko bawa ya barkace

    Don ko ya yi dubara

     

    Ta barkace

    ‘Yan nema

     (Alhaji Kassu Zurmi: Bala Babban Bawan Firimiya)

     

    Ɗangogin da ke da gicciyen rubutu su ne ke ɗauke da zuga duk kuwa da haƙurin da Kassu ya ba jama’a a ɗango na goma.

    Ko bayan amfani da salon kacici-kacici, har ila yau mawaƙa kan yi amfani da wasu salailai domin waƙoƙinsu su kaifafa tunanin masu jin su ko karatun su. Misali, akwai salon da za mu kira salon ishara wanda ke ɗauke da maganganun da suka tusgo a sakamakon nazarin da mawaƙi ya yi zuwa ga abubuwa da ke a gabansa waɗanda kuma galibi sukan zo su wuce ba tare da sauran mutane sun lura da hikimomin da ke tattare da su ba. Wannan kuwa watakila saboda idanun mawaƙi daban suke da na sauran mutane. Watakila kuma saboda kasancwar abubuwan ‘yan ƙanana. To, ko ta yaya ne dai, salon ishara jan hankali ne aikinsa a cikin waƙa.

    A waƙarsa “A Bi Gaskiya Ad Daidai”. Alƙali Bello Giɗaɗawa ya buɗe ta da salon ishara kamar haka:

    Idan dabba tana sauri ga turke

    Da amfanin da tas san za ta iske

     (Alƙali Bello Giɗaɗawa: A Bi Gaskiya Ad Daidai)

     

    Wannan baiti zai saka mu cikin zurfin tunani saboda salon da aka saƙa shi da shi. Haƙiƙa kam babu dabbar da za ta kai kanta ga wurin da za a ɗaure ta idan ba ta riga ta kwana da sanin cewa zuwanta wurin har a kai ga ɗaure ta, a hana ta walawa, ba zai tabbatar mata da abinci ba. Idan kuma aka faɗaɗa wannan saƙo kaɗan sai mu fahimci cewa ɗan Adam ma haka yake. Da hankalinsa a kuma gane shi haiƙan ya tasar wa abin da ya tabbata mai cutarwa ne, to ka kwana da tabbacin cewa ya hango wata moriya da kai ba ka hango ba. Ba banza ba ne a ƙasashe masu tasowa sojoji da ma ‘yan siyasa ke ta kicaniya domin su kai ga karagar mulki, duk kuwa da yake sun san cewa akwai wasu can a ɓoye suna shirin makamansu. Sun sani cewa a mafi yawan lokuta ƙarshen shugabannin ƙasashensu a bakin bindiga yake.

    Amfani da salon ishara musamman wanda aka gauraya da wani salo, kamar na karin magana ko ƙirarsa, da kuma na tambaya, yakan kaifafa tunanin mai saurare. Dubi yadda waɗannan baitoci suka zo da wannan salo:

    Idan ka ce ma ɓera na da sata

    Fa ƙamshin daddawa shi anka ɓata

    ……

     

    Idan an ce da kai bari ƙulla sharri

    Riƙe horon ga nashi ƙwarai da sauri

     

    Zama sharri halin karnai gare shi

    Biyar mai shi yakai ai ba shi fashi.

     (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Magana Ciki Ke Sa Gunguni)

    Shi kuwa Wazirin Gwandu Alhaji Ummaru Nasarawa ya yi amfani da salon ishara kamar haka:

    Wasu ‘yan yara kurin sanin zamani

    Shi ka ruɗin su har ram ma manya sukai

     

    He ku luro da manyan ga dai naku su

    Sunka rene ku sun hi ku komi kukai

     

    In sani shi ka sawa ka rena su su ko

    Na bayanaka sun hi ka ram ma sukai

     

    Lura in don sani kak ka rena su don

    Yara su ko na bayanka tcar ma sukai

     (Wazin Gwandu U. Nasarawa:Yadda Ya Kamata Nijeriya Ta Zamo)

    7. Sosa Zuciya

    Waƙa, kodayake dai magana ce, ta fi magana saurin tasiri a zuciya. Da ita waƙa, da ita zuciya, duka sun rataya ne kan rauji, wato zubin sauti a tsare, a kan kari, ba kara-zube ba… Amma ita waƙa, duk da ita ma tana iya ƙunsar labari, wato tana takalar hankalin mutum, duk da haka kuma tafi takalar zuciya, nan take.

     (Ɗalhatu Muhammad: MUƘADDIMA kan Jigon Nazarin Waƙa)


    Wannan magana ta shaihin Malami ba ta bar kome ba daga abubuwan da muke da nauyin faɗa a wannan sashe. Waƙa ce ta ƙumshi abin da ake kira rauji wanda sauran manyan rassan adabi suka rasa. An lura a babi na biyu cewa rauji yana daga cikin muhimman tubalan da ke gina salo. Saboda haka babu bukatar fayyace abin da yake nufi a nan. Haka kuma misalin da aka gabatar a yayin da ake yin bayanin ma’anar rauji ya dace a wannan wuri. Da wannan misali da sauran waɗanda za su zo yanzu duk masu nuna yadda salo kan sosa zuciya ne.

    Kinaya salo ne da ke iya sosa zuciya nan take. Saboda haka ne ake ganin mawaƙa suna amfani da shi a duk lokacin da bukatarsu ita ce su zuga wanda suke yi wa waƙa. haka kuma saboda haka ne ake samun wannan salo a kai akai cikin waƙoƙin sarauta. Ta amfani da wannan salo sai mawaƙa su siffanta basarake da abubuwan da babu tababa ga ɗaukakarsu. Shi kuwa ɗan Adam da ke da halin son ya ji shi ne wannan abu a cikin saraukuna da sauran jama’a, sai ya hau. Ga misalan wannan salo mai sosa zuciya.

    Waƙar Baka (W/B)

    A. Ya gade gidan Bello

    Riƙa wandara sai Madi

     

    Manyan maza maƙara magana toron giwa

     

    B. Ɓauna masha dahi Garba

    Ya ba maƙiya haushi

     

    C. Rijiyar tsakar daji

    Mai ila ka faɗa

    Turbar bisa sai tsuntsu

     (Salihu Jankiɗi: Abubakar III Ya Gade Gidan Bello)

     

    D. Mai lihiddan faɗa, gimshiƙin shamaki

    Baba shimgin ƙaya

    Mai wuyur ratce

     

    E. Toron giwa kake mai Garewa Alu

    Ba a hwaɗa ka

    Tilas a kauce ma

     (Musa Ɗanƙwairo: ‘Yandoto Aliyu Shirya Kayan Faɗa)

     

    Rubutattar Waƙa (R/W)

     

    F. Kai ne Mu’azu haƙiƙa ka zama Ummaru

    Ka gadi Abdu mu bi ka ɗan Hassani

     

    Himma riƙa Ɗibgau salamun Makaye

    Shimgi na Gatau kamdaren Usmani

     (Alƙali Haliru Wurno: Yabon Sarkin Musulmi Abubakar III)


    Rawar salo a wajen sosa zuciya tana da yawa. Domin haka ba za mu iya fayyace dukkan salailan da rawar ta shafa ba. Sosa zuciya kuwa iri-iri ce kamar yadda aka san cewa haliyya tana da nau’o’i. Saboda haka ba kuskure ne ba idan aka ce salo shi ne musabbabin waƙa ta sosa zuciya.

     8. Sarrafa Tunani

    Tun da salon waƙa yana iya sarrafa zuciya ta shiga wata haliyya daban da yadda salon ya tarar da ita, ashe ba zai zamo masa abu mawuyaci ba ya sarrafa tunani zuwa nahiyar da yake bukata. Abin nufi a nan shi ne cewa, a dalilin salon da aka yi amfani da shi a cikin waƙa ne tunanin ɗan Adam kan tashi daga wannan nahiya zuwa waccan. Salo kan tarar da tunani yana fuskantar abubuwa ko rayuwa da yanayin haƙiƙani, wato yana duban rayuwa kamar yadda take a zahiri. To idan ya tarar da tunani cikin wannan hali, salo kan iya sarrafar da shi ya koma yana duban rayuwa ta fuskar romon ka. Wato sai salo ya sihirce tunani ya koma mai yarda da abin da ba haƙiƙani ba, ya saka tunani cikin mafarki nan take. Abin da babu ya zamo ya wanzu. Abin da bai yiwuwa ga hankali, sai ya kasance yana iya ya faru, ko ma ya faru ɗin, abin da ya riga ya auku ya zamo yanzu ne yake aukuwa….Duk wannan kan auku a cikin tunanin ɗan Adam a sakamakon tasirin da salon waƙa ya yi a kansa. Wannan shi ake nufi da cewa salon waƙa mai sarrafa tunani ne.

    Akwai salailai da dama masu taka wannan rawa ta sarrafa tunanin ɗan Adam. Daga cikinsu akwai salon zayyana da kinaya da jinsarwa da kuma na hira. Saboda taƙaitawa za a kawo misalan da ke ɗauke da fiye da salo ɗaya a lokaci guda.

    A waƙar da ya yi wa Maidabo, Kassu Zurmi ya yi amfani da salon labari da na hira da na zayyana domin ya sarrada tunaninmu. Kassu na cewa dangane da Maidabo.

    Tauri ya kyauta mai duniya

    Kuma ya kyauta mai lahira

    Yanzu wani ya ce ƙarya nikai

     

    To za ni hwaɗa muku abin da yak kyauta mai lahira

     

    Tun bariyac can da anka yi yayin kwallara

    Alloba tam matsa

    Ta wulla ƙatta ɗai takai.

    ….

    To Maidabo yay yi yanutsi da mutanen lahira

    Sha-biyun dare masassara tas samai

    Tun da sashe kulkin Badau yam mutu

     

    Yat tashi ya’ishe Nakiri yana wankin ido

    Yaɗ ɗibga mai sallama

     

    Yac ce ma Musa Kirca-Kirca

    Dibo min mai man sallama

    Ka gani wana ne yaz zaka

     

    Musa yaj ja sandatai ƙasa

    Yaz zo yac ce wa an nan mai mai sallama

     

    Bai dai tanka ba

    Shina kuruninai

    Ya cije na gidan Duwa

    Hwaɗin rainai ɗai yakai

     

    Wa an nan kai mai sallama

    Bai da tanka ba shina kuruminai

    Hwaɗin rainai ɗai yakai

     

    Sannan mala’ika yac ce

    Tanka ka ga baranai ya zaka

     

    Maidabo yac ce ban jiya ba

    Sai manyanai sun zaka

     

    Musa yak koma yak kai gami

    Yaz zo yac ce wai ya ce sai ka zaka

     

    Yac ce sai na zaka

    Wa an nan mai taurin ido

     

    Maidabo yac ce da zucci kowana ne ka sani

     

    Ya gamo sallatai Nakiri

    Duy yas sa kayan hwaɗa

    Yaj jawo sandatai ƙasa

    Yaz zaka yak kwakkware mai ido

    Ya aza wai shi tsoro nai yakai

     

    Wa an nan kai man sallama

    Bai dai tanka ba

    Shina kuruminai

    Hwaɗin rainai ɗai yakai

     

    Wa an nan kai man sallama

    Maidabo bai da tanka ba shina kuruminai

    Hwaɗin rainai ɗai yakai

    Zucciyatai na taso mashi

     

    Nakiri yac ce kai bawan wa ne kai

     

    Sannan Maidabo yac ce ba bawan kowa ba ne

     

    Ba bawan kowa ba ne

    Kai ko kai ne na gidan Duwa

    Yac ce ai ni na duk ka sani

     

    Yac ce kai dun na sani

    Maidabo na ji hwa ku as shaggun duniya

    Kowa tsoro nai yakai

     

    Ya ce i mu a shaggun duniya

    Kuma mu as shaggu lahira

    Mun taho

    Kowa tsoro na yakai

    Had da kai ma kau sai ka sani

     

    Sannan Nakiri yah hyaɗi gabanai

    Yara kui ta tauri ba ƙarya ba ne

     

    Ya ce kai sai na sani

    Kai kac ce sai na sani

    Maidabo to nan hwa ba a tauri

    Koma duniya

    Yi gida

     

    Ya samo sallama sabadda ya shikka mai gardama

    Yara kui ta tauri ba ƙarya ba na

     (Alhaji Kassu Zurmi: Na Gidan Duwa)

     

    Ka gani dai tun da farko ba a zuwa lahira a dawo. Na biyu ba mu san inda Nakiri yake ba balle har a ce Maidabo ya je wurin ya yi masa sallama. Sannan kuma ai iyakar sanin Musulmi mala’iki Nakiri tare da mala’iki Munkara yake. Ko a ina Kassu ya samo wani mai suna Musa Kirca-Kirca? Oho! Kuma yaushe ne Kassu ya ga Musan in har akwai shi balle ya san irin shigarsa? To daɗa ballanta shi Nakirin. Kai hasali ma Kassu ya sa mu yarda da cewa mala’ikin da ke tare da Maidabo (watakila ɗayan Raƙibu da Atidu, oho) ya lallashi Maidabo domin ya daina taurin kai. Haka kuma Kassu ya faɗa mana irin sa-in-sa ɗin da Maidabo ya yi da Nakiri wadda ita ce dalilin da ya sa Maidabo ya samo iznin dawowa duniya!!! Mun dai san cewa ba Maidabo ya ba shi wannan labari ba, domin yadda Kassu ya zayyana wannan gamuwar abin ya wuce ji, sai dai gani! Anya kuwa Kassu ya gano? Duk wannan abu da Kassu ya sa tunaninmu ciki yana ƙumshe cikin salailan labari da na hira da na zayyana waɗanda Kassu ya yi amfani da su.

    Yanzu kuma sai mu kawo wani misali daga rubutattun waƙoƙi kamin mu rufe wannan sashe.

    A wannan misali da za mu kawo za mu ga mawaƙi yana amfani da salailan hira da na labari da kuma na jinsarwa domin ya sarrafa tunaninmu daga wannan yanayi zuwa wancan. Haka kuma ya tsawaita wannan sarrafawa kamin ya kawo wani salo wanda zai sake sarrafa tunanin namu zuwa wata nahiya. A taƙaice abin da mawaƙin ya yi shi ne ta amfani da waɗannan salailai, tare kuma da na shillo sai ya riƙa kai tunaninmu ga wannan dabba da wannan wuri ko yanayi zuwa waccan dabba ko wuri ko yanayi yana kuma bayyana sakamakon gamuwarsu da shi tare da kawo dalilan da suka sa ya yi gaba. Ga dai yadda baitocin suka zo. A farkon waƙar ne suka fara suka ci gaba har zuwa rabinta:

    Na zaka ƙara na kawo ta

    Jalla gare ka ka dai dube ni

     

    Na ga rashin abkin kayna

    Don haka tsoro ya ribce ni

     

    Na ga dare da subahin haske

    Ga kuma rana ta dushe ni

     

    Na yi farat na sheƙa inwa

    Na ga kwamarci ya kore ni

     

    Na ga ruwan gulbi na zallo

    Na zo na shiga sun toye ni

     

    Na tuma na koma can ganga

    Ba wani mai jinya ya fake ni

     

    Na bi dibarorin balbela

    In ishe mai ƙarfi ya riƙe ni

     

    Na yi ga giwa sai tas sheƙa

    Karkandai sai yak kore ni

     

    Na yi ga zaki na ishe bai nan

    Na yi ga kura tac cije ni

     

    Na ga zarafatu na isko ta

    Sai tac ce mini ban son reni

     

    Na ce dubi jikin ya swale

    Ba ki yi min rahma ki riƙe ni

     

    Na ga ki ke yi tsawo ga kyawo

    Duƙo wuyanki ki dai dube ni

     

    Na ga tana da nufin banka ta

    Na yi sago sai tam mere ni

     

    Naƙatu na can inda mijinta

    Raƙumma ban son su gane ni

     

    Na ga kamar in amro zarafa

    Tai gumza tas shure ni

     

    Na yi gidan aladai in tsira

    Gunzu yac ce kar ka matse ni

     

    Na ga yana da nufin cuta ta

    Nif fita kar banza ta kashe ni

    Na ga barewa na tambai ta,

    Inda gada take don ta riƙe ni

     

    Na ce mat ta gwada mini hanya

    Inda gadar take ko ta rake ni

     

    Na ga gada da gudu ta sheƙo

    Tac ce min tafi kar ka biyo ni

     

    Na ga gudun da takai na ɓakita

    Na jaye mata ta hauro ni

    Na yi ga zomo bawan Allah

    In shiga kurhinai ya fake ni

    Na yi gabas wajjen yanyawa

    Kila dibaratai ta ishe ni

     

    Na ishe limami yanyawa

    Ga ni mu’allamu zo ka daɗe ni

     

    Na ga ashe smhi ma tai zahi

    Sa’alabu ya ce tashi ka bar ni

     

    Na yi zugum ya ce kai tashi

    Ba ka ganin inwa ta bar ni

     

    Na yi zufa rana ga zafi

    Matata ita ma ta bar ni

     

    Na ce Mallam ka san Allah

    Yac ce min ai Shin Yay yo ni

     

    Na ce dubi hadisin tanyo

    Ba ka yi min girman addini

     

    Na ga kamar maganar ta kammai

    Sa’alabu ya ce kai ka fi ni

     

    Na ga kana iya kanka da kawo

    Kwanana huɗu ban da sukuni

     

    Na yi biɗar ƙannen matata

    ‘Ya’yana huɗu dut sun bar ni

     

    Na ce assha na sa ƙaimi

    Kar ya tumam mini ko ya buge ni

     (Alƙali Haliru Wurno: Gudale)

     

    To duk wannan yawo da hankalinmu da Haliru ya yi manufar ita ce ya gina mana ƙimar wani wanda ya yaba a cikin waƙar. Saboda haka a duk inda Haliru ya yi amfani da salon jinsarwa za ka tarar kuma akwai salon kinaya cushe a ciki. Hasali kusan dukkan dabbobi da abubuwan da ke cikin waƙar cikin irin salon suke.

    9. Sadar Da Mawaƙi Da Jama’a Ga Ɗanɗanarsa

    Abin nufi da wannan rawa da salon waƙa ke takawa shi ne sanya mai saurare ko karatun waƙa ya ji abin da mawaƙi yaji kamin ko yayin da yake ƙirƙiro waƙarsa. Zaɓen kalmomi da tsara sauti tare kuma da sauran salailai kamar su kinaya da zayyana da ƙirƙirar jumloli, duk su za su kawo wannan ɗanɗana ta mawaƙi ga mai saurare ko karatun waƙarsa. A kan wannan magana ce muke ganin misalan da suka gabata da kuma tattaunawar da aka yi dangane da waɗannan salailai, musamman a ƙarƙashin muhimmanci da ya shafi isar da saƙo da sosa zuciya, ba sai an ƙara wani abu ba a nan.

    10. Asirin Waƙa

    Idan mai karatu yana biye da abubuwan da aka tattauna tun daga babi na biyu mai taken muhimman tubalan salo har zuwa wannan wuri da aka iso cikin babi na uku, zai lura da cewa ashe dai salo shi ne ruhin waƙa, shi ne ke sa ta zamo abin da za ta zamo. Idan babu salo to kuwa babu abin da za mu kira waƙa.

    Haka kuma wannan tattaunawa za ta lurar da mai karatu cewa salon waƙa ya fi gaban a kalle shi da cewar wata waƙa ba ta ƙumshe shi ba. Sai dai a ce wata waƙa ta ƙumshi salo marar yawa ko mai rauni ko makamancin haka. Wannan magana kuwa wadda ake iya sa wa ayar tambaya ce.

    Yarda da cewa salo shi ne ruhi, shi ne ke isar da saƙon waƙa kuma shi ke sa waƙar ta zamo waƙa, ba magana kara zube ba, ita ce ta sa aka ce salo shi ne asirin waƙa. Ba ka iya ganin abin da mawaƙi ya gani, ba ka iya jin abin da mawaƙi ya ji, ba ka aikata abu a sakamakon ji ko karanta waƙa, misali, kana basarake waƙa ta zuga ka ka ji ka fi kowa, ba ka yin duk waɗannan a sakamakon ji ko karatun waƙa ba tare da aikin salo ba. Haka abin yake kasancewa domin kuwa salon ne masubabbin jin waƙar da ka yi ko karanta ta da ka yi. Salo ne ya sa waƙa ta kasance maganar ɗan Adam mafi kyawon tsari wadda kuma ta kai matuƙa ga tacewa ba tare da ma’ana ko fahimta sun raunana ba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.