Zan Iya Ba Wa Wanda Ba Musulmi Ba Gidan Haya?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum malam. Don Allah ya halatta a gina gida a ba wa Kiristan haya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam.

    Ya halatta mana, tun da Annabi S.A.W. ya yi mu'amala da Yahudawa kuma ya mutu silkensa na yaki yana wajan Bayahude saboda Sha'ir din da ya amsa kamar yadda ya zo a hadisi ingantacce

    Akwai gonakin Annabi S.A.W. da na sahabbai a wajan Yahudawan Khaibar inda suke aiki a cikinsu suke bawa musulmai rabin abin da ya fito na amfani kamar yadda ya tabbata a Sahihu Al-bukhari

    In har an san zai yi ɓarna ko saɓon Allah a cikin gidan bai halatta a ba shi hayarsa ba, Allah maɗaukakin sarki yana cewa: "Kada ku rika taimakekeniya wajan aikata saɓo" Suratu Al'ma'idah aya ta: 2.

    A cikin Suratu Al-mumtahanah Allah ya yi bayani cewa: Ana iya kyautatawa kafirai a kuma yi musu adalci mutukar ba sa yakar musulmai, hakan sai ya nuna halaccin ba su haya

    Allah ne mafi sani

    Dr, Jamilu Zarewa

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.