Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
Marhaba da aure na sunna,
Marhaba da aure na ƙauna,
Ussuman Lawan ne fa ango,
Zainabu Abdullah amarya.
Marhaba da lale,
Ga amarya lalle,
Tai kitso da lalle,
Mu muna ta lale,
Marhabin da lale,
'Yar uwa a lalle,
Za a kai amarya Zainabu
Gun miji Ussuman na ƙauna.
Haƙƙuri ka ɗauka,
Ba fushi mushakka,
Kan haƙin gidanka,
Kat tsare girarka,
Miƙa godiyarka,
Gunsa wanda yai ka,
Wanda yai amarya da ango,
Yau suke bikin so da ƙauna.
Marhaba da wannan mataki,
Ussumanu ka zam sadauki,
Ka biya halali sadaki,
Za ka sami babban masauki,
Rukkuni na aure mataki,
Sharruɗa na aure mataki,
Kat tsare dukannin hakoki,
Da suke a kan auren sunna.
Shawara gare ki,
Kirriƙe mijinki,
Ki yi ado da miski,
Ga mutumta girki,
Kit tsare gidanki,
Ki mutumta kanki,
Kar ki saɓa zancen mijinki,
Yin hakan yana ƙara ƙauna.
Allah ƙara ƙauna da yalwa,
Allah bar zumunci da kewa,
Allah saba hali na kowa,
Kui zaman aminci da kewa,
Kar ku ɗau zugar masu kwawa,
Masu gulma aiki na wawa,
Kui riƙo da sunnar ma'aiki,
Mai izo tafarki na sunna.
Ko’ina da ƙamshi,
Armashi na ƙamshi,
Shi yake ta tashi,
Ga ado na ƙunshi,
Ƙyalƙyali na leshi,
Tambari ka tashi,
Don bikin amarya da ango,
Marhaba da aure na sunna.
Tambari na ƙauna,
Ma su so da ƙauna,
'Yan uwa na juna,
Ga aminan juna,
Goggo na ta murna,
Mama na ta murna,
Yau biki na auren Usuman,
Gobe sai biki kau na suna.
Tambari na ƙauna, amarya,
Ma su so da ƙauna, amarya,
'Yan uwa na juna, amarya,
Ga aminan juna, amarya,
Goggo na ta murna, amarya,
Mama na ta murna, amarya,
Yau biki na auren Khadija,
Gobe sai biki kau na suna.
Gaisuwar iyayen amarya,
Baba ga ni na zo da zarya,
Ginshi na tsatson amarya,
Gaisuwar iyayen amarya,
Goggo ga ni na zo da zarya,
Ginshi na tsatson amarya,
Ginshiƙin amarya Khadija,
Ginshiƙi na so ne da ƙauna.
Gaisuwar iyaye na ango,
Alhaji Lawan baban ango,
Allah ƙara danƙo na ungo,
Yat tsare amarya da ango,
Gaisuwa gurin maman ango,
Hajja Zainabu maman ango,
Hajja Fatsima maman ango,
Allah ba da zamman lumana.
Alhaji Isma'ila Lawan-
Ga yabo na girma da ƙauna,
Manya manya yayu na ango,
Ga yabon yabawa da ƙauna,
Godiya ga danginmu Ila,
Na taya ka murna ta ƙauna,
Allah ƙara danƙo na ƙauna,
Sui zaman lumana na sunna.
Yayyen ango,
Alh Ismaila Lawan,
Jinjina ta girma na ƙauna,
Alh Nura Lawan ma,
Ga yabo na girma da ƙauna,
Alh Sani Lawan ma,
Ga yabo da barka da sunna,
Hauwali Lawan jinjinawa,
Don yabo a aure na ƙauna,
Ladidi Lawan yabawa,
Jinjina da aure na ƙauna.
Ƙannen ango,
Nasiru Lawan ga yabona,
Tijjani Lawan ga yabona.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.