Muhammed Tukur Ango Na Fatima

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 

Abin fahari da farin ciki aure jigon ƙauna,

Muhammed Tukur ango na Fatima auren soyayya.

 

Shimfiɗa

Bikin girma na taho na shaida ‘ya’yan alfarma,

Asin da asin na taho na kalla auren alfarma,

Wuri da wuri na taho na duba don halin girma,

‘Ya’yan asali aka sa a lalle ‘ya’yan mai girma,

Muhammed Tukur ƙarami magajin hafsan alfarma,

Muna murna da hawa matakin aure mai girma,

Angon Fati ka riƙa da kyau Allah ƙaro alfarma.

 

Alƙahharu wanda ya wajabta nake wa bautawa,

Altauwabu Sarki guda da ya keɓu na tubar wa,

Alrazzaƙu wannan da shi yakkeɓe azirtawa,

Sunnar aure fa tana cikin falaloli mai girma.

 

Da faɗin Allah aka ce da malu banuna adon duniya,

Da kuɗi da ɗiya aka ce ado ne na rayuwar duniya

Samun ‘ya’ya ko na arziki sai an aure ku jiya,

Sunnar aure fa tana matakin farko al-farma.

 

Biki uku ne ake yi wa taron murna hamshaƙi,

Na farkonsu bikin haihuwa a farkon mattaki,

Na biyyunsu bikin aure ka hau farkon mataki,

Na ukun shi ne bikin a naɗa muƙamin hamshaƙi.

 

Tuwon girma aka ce da nama an ka yi mai girma,

Gidan girma aka ce a nan aka shimfiɗa tabarma,

Halin girma aka ce da shi aka gane mai girma,

Tukur junior ka riƙa da kyau da halinka halin girma.

 

 

 

Kowa ka gani sanadi na taron nan murnar aure,

Dangi na amarsatu na ta murna kan shagalin aure,

Dangin ango fa suna ta murna don shagalin aure,

Da abokan arzurƙai sun ga hali fa halin girma.

 

Tukur ango riƙƙe amanar Fatima matarka,

Hakin aure kar ka rage duk kasa ga matarka,

Tufatarwa muhalli da ci da sha duka na kanka,

Sai tarbiyya da uwa uba addini mai girma.

 

Fatima Usman ina shaidarki da halayyar kirki,

Ki ƙauwame kai naki ki ƙauwame sirrin angonki,

Ki tsaftace kayinki gida ki haɗa sirin girki,

Ki yo kissarki gami da gwalli gunsa da taƙamma.

 

Tukur Yusuf Buratai ubanmu abin fahari ya zo

Uban tafiya baba ga ango ba ka halin bozo,

Ina murna kan wanga aure don haka ma naz zo,

Ina fatan rabon alkhairi mai ɗimbin girma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments