Ticker

6/recent/ticker-posts

Tambarin Amarsu Da Ango

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Waƙar tambarin amarsu da ango ni nake,

Soyayya a kai a yau ɗaurin aure muke.

 

Dukkan lokaci yana tafe kan rana yake,

Duk al'ammari yana bisa kan ƙaidi yake,

Kowane sha'ani a kan sharaɗoɗi nai yake,

A yau alƙawari na aure yau ranar take.

 

Yau ranarku ce amarsu ta ango yau ake,

Yau shagalin biki amarya ta ango ya ku ke,

So da farin ciki a gunku a yau duka sun fake,

Zangon rayuwa mataki na biyu yau ake.

 

Farko rayuwa ta macce ka san abba take,

Kun san rayuwa ta tarbiya ahli suke,

Sai kuma rayuwa ta aure wacce a yau ake,

Ƙarshen rayuwa ta macce a gun ‘ya’ya ta ke.

 

Kin dacen uba mahaifi son kowa yake,

Kin dacen uwa abar faharin kowa take,

Kin dacen miji dukanku ɗiyan asali kuke,

Yau ranarku ce kawai taya murna mu muke.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments