Ta’aziyyar Mai Martaba Alh. Dr. Ado Bayero

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Ganin mutuwarka ya gwada bak ka yo mulkin banza ba,

    Rabuwa da masoyi Ado Bayero za mu kai shi kushewa,

    Da ganin mutuwarka ya gwada bak ka yo mulkin banza ba.

     

    Bankwana da masoyi Ado Bayero sa’inai ya yi,

    Rabuwa da masoyi Ado Bayero za mu kai shi kushewa,

    Mai tagwayen masu Ado Bayero hamshaƙin sarki,

    Da ganin mutuwarka ya gwada bak ka yo mulkin banza ba,

    Bankwana da masoyi Ado Bayero Sa’inai ya yi,

    Rabuwa da masoyi Ado Bayero za mu kai shi kushewa.

     

    Rabbu gagari koyo mai zarafin aro na kujerar sarki,

    In ya so ya ara ma ai maka tambura da amon kakaki,

    Kai Ado mu raka ka mui maka bindiga alamin kai sarki,

    Ga wuƙar yanka nan ka sagale alama ta ƙarfin mulki,

    Kan a tashi tana nan sai ta dangana ka babban sarki.

     

    Wanda yai kyakkyawa zai shi ya tad da shi a cikin ƙwarya tai,

    Wanda mummuna za ya tad da shi a cikin ƙwarya tai,

    Wanda yai adalci yai guzurin zama a kufai na makwantai,

    Wanda yai mummuna yai guzurin zmaa a kufai na makwantai,

    Ga masoyin Annabi mun masa rakkiya da dubu na salatai.

     

    Yau me zan ce ne Juma’atu da taz zama ranar kuka?

    Shekara ta dubu biyu sha huɗu taz zama ranar kuka,

    Ran shida ga wata na shidda Juma’a lamarin fa ya sauka,

    San da lamarin ya ishe ni a waya sai nas saka kuka,

    Sai jiki yai nauyi har na kasa sauke ƙafata hakka.

     

    Masakan saka tsinke babu a san da na isa rinkar sarki,

    Jami’ai na tsaro sun tsinke ga igwa da sukayen sulke,

    Ba ta su muka yi ba burina in je in ga babban sarki,

    A yi sallar haja ai rakiya da ni a raka shi masauki.

     

    Da shigar mu gidan nan sai na jiwo amon wani sautin kuka,

    Wani na furtawa gata babu yau kuma dai sai kuka,

    Wasu na ji suna wayyo Allah gare ka muna kai kuka,

    Garun jingina ya kwanta babu gun da muke kai kuka,

    Yau gare muke alfarmar littafan da ka sa suka sauka.

     

    Inda nak kaɗa kaina sai jama’a dubu daga masu muƙamai,

    In juya idona sai jama’a dubu da ganin su sarakai,

    Yau dubun jama’a ba ƁIP bare wani yai ma jin kai,

    Dukka dai alhini ko ta ina na juya idona ko kai,

    Babu wane da wane ko ɗan wane ko ko jini na sarakai.

     

    Yau fa ranar tsumi ta zago an daɗe fa da harsashen ta,

    An daɗe fa ana ƙaryar mutuwa ta Maikano yau dai ga ta,

    Masu dokan rana taz zuwa gas hi yau dai ta zo ga ta,

    Mu da ke kuka ga fili, wanda ke murna dai ga ta,

    Mu yi duk mu gama kuma mu ma ƙabari za mu je fa mu kwanta.

     

    Allah kyauta makomar Bubakar na ukku sulɗanin sarki,

    Cibiyar mulkinmu Sakkwato sansanin na Fulanin sarki.

     

    Allah hukkumu sa’a sarki Usmanu na Gombe sarki,

    Ta’aziyyar ƙauna nai maka zuciya da gaɓa har baki.

     

    Allah kyauta makomar sarki Kabiru Kattsina babban sarki,

    Rahama jin ƙai ne sudan a cikin ƙabari na ma sarki.

     

    Allah ƙara salama sarkinmu Bashar basaraken Daura,

    Allah haska ƙuburirana ta gamo da su’al a masauki.

     

    Allah gyara makwancin sarki Ummaru alkanimin Borno,

    Dausayi a makwanci kana ƙamasasa da turaren miski.

     

    Allah kyauta makomar saki Aminu Zazzau babban sarki,

    Ta’aziyyar nai ma albarka ta Maikano giwar sarki.

     

     

    Gaisuwar ta’aziyya gun Lamiɗo Mustafa a Adamawa,

    An yi an ƙare lau Allah ya ƙara ƙauna ga babban sarki.

     

    Allah kyauta makwancin Haruna Jakwalo basaraken Gwandu,

    Allah kyauta makwanci yai masa armashi da turaren miski.

     

    Allah kyauta masaukin sarki Suleimanu mazajen Bauchi,

    Sanadin ɗan Bayero nai ma baituka basaraken sarki.

     

    Ga masoyin Annabi nan ɗan Abdu ya baƙunci masauki,

    Allah lamunce mar dukka su’al da duk aka yi masauki,

    Allah ba shi iko amsa batun duk da ake a masauki,

    Mala’ikun rahama ga baƙo nan gare ku ku ba shi masauki,

    Ku baɗe shi turaren Aljanna da ke ƙamnshin nan muski,

    Allah kyauta zuwanmu mu ma a gare ku mu samu masauki,

    Mu samu masauki, mu samu masauki.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.