Hikima Taguwa

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Hikima taguwar hawana,

    Mannufa Allah ya ƙaryar zumana.

     

    Hattara dai Aminu Ala,

    Ka gode Ubangijina.

     

    Jalla sarki abin dogarona,

    Abin bauta da tsantsanina,

    Ina godiya ga kaliƙina,

    Da baiwar hikkima a guna.

     

    Salati salo salo na ƙauna,

    Ga Manzo abin kwafa a guna,

    Habibi abin yabo a guna,

    Karimi uba ga Binta Nana.

     

    Ƙwaƙwalwa turken jikina,

    Dukannin sassan jikina,

    Nan suke karɓe na ayyukana,

    Sug gabatar bissa ra'ayina.

     

    Hankali mizani awona,

    Sai tunani akalar batuna,

    Illimi jagoran jikina,

    Hujja sanda ta kare kaina.

     

    Sai azanci armashin batuna,

    Laffuza gwalagwalan batuna,

    Basira adon batuna,

    Bincike hujja a kan batuna.

     

    Da ganÉ—a a furrucina,

    Da hanƙa a furrucina,

    Haƙora da hasarana,

    Da tantani maƙwallatona.

    Da harshe cikin batuna,

    Da laɓɓa a taimakona,

    A gun harba sautukana,

    Na gode wa Kaliƙina.

     

    Ƙafafu maɗaukakan jikina,

    Hannuwana masu tallafina,

    Lafiya ce jarin zubina,

    Rabbi sarkina ka taimakona.

     

    ÆŠaukaka Allahh da kai a guna,

    Godiya ce buÉ—in rabona,

    Kats tsare sharrin dare da rana,

    ÆŠan’adam, Aljan a magautana.

     

    Hikima taguwar hawana,

    Mannufa alƙaryar zuwana.

     

    Ka gode Ubangijinka.

     

    Manufa alƙaryar zuwana.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.