Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Shimfiɗa
Wanga zango ne na biyarrrrrrrrr,
Rukunin nasara a guna.
Cikkamakon tarihi,
Alfiyya ta gudana.
Amshi
Shahara sanadin bugawa,
Nasara ta samu guna.
Haka mun ka yi ni da Tola,
Wancan loton da kaina.
Shi ya sa shi da jin bayanin,
An kamo ni da rana.
Yaz zo ya tunasasheni,
Shawararmu da ta wakana.
Muka tafa ni da shi “Taf!”,
Dariya taɗ ɗan gudana.
Wani mamaki kumawa,
Da ya sake zuwa a kaina.
Aka ce in charge na furzin,
Na nema na mu gana.
Na ishe shi a ofishinsa,
Bisa tebur na gudana.
Sai ya ce a shigo da ALA,
Aka min izini na zauna.
Sai ya ce ALA na waƙa,
Ya hakka ta faru kaina?
Nai masa fiɗar bayani,
Daga farko har zuwana.
Ya yi min fata na khairi,
Da du’a’i a wajena.
To ashe incharge na furzin,
Na bikon baitukana.
In na dawo za ni zauna,
Sai a ce an zo kirana.
In na ɗan zauna in huta,
Incharge sai yai kirana.
Furzin Taigas suna so,
Mu yi hira da su da juna.
Incaji yana buƙatar,
Ya ji zancena da kaina.
Ga tsararru ‘yan uwana,
Na shauƙi don mu zauna.
Ga baƙi ‘yan ziyara,
Ba ƙaƙƙauci kirana.
Ni fatana a bar ni,
Da tsararru don mu gana.
In tsinci abin buƙata,
Daga bakin ‘yan uwana.
Ɓacin raina guda ɗai!
Mai sanya bugun gabana.
Ƙara don buɗe ƙofa,
Ke juyan hankalina.
Wai doka ce gurinsu,
A dare ne ko da rana.
Shiga da fita ta ƙofa,
Sai an doka da gunna.
Daga an taɓa wagga ƙofa,
Sai ta ja hankalina.
Alamin aikin tsaro ne,
Yas sa haka ke gudana.
Hikimar wai masu laifi,
Ba su yin haka za su ɓarna.
Duk mai aiki na laifi,
Sanɗa yaka yi sanina.
Ba shi ƙaunar a yi ɓuruntu,
Ko ko motsi ya gudana.
Shi ya sa suka doka ƙofa,
Ko dare safe da rana.
In ka ɗauke wagga illa,
Babu ɓacin rai a guna.
Domin na san kulawar,
Mai tsaron ɗaki a guna.
Wani mai suna da Bello,
Shi ya zamto hadimina.
Sabulun wanka da omo,
Da ruwan wanke jikina.
Sun mani karɓar karamci,
Sanadin ƙaunarsu guna.
Wanka sai nai sau uku,
Duk wayewa ta rana.
In gajarce makku komai,
Wanshekare da rana.
Aka maishe ni a kotu,
Ta aminta da mai belina.
Aka dagga zama na kotu,
Muka je mu tsumayi rana.
Sai na sami ubangidana,
Sani Lawan maigidana.
Na gaya masa can a jarum,
Kwai sadaka mai gudana.
Saddakatujjariyar nan,
Mai lada mai gudana.
Wani yawon darre yay yi,
Ya shekara gun da kwana.
Wani rikici na iyali,
Yas shekara gun da kwana.
Wani matsala ce ta aure,
Tak kai shi wajen da kwana.
Wasu ba hali na biyan,
Tara ya saka su kwana.
Wani fayif tausan kaɗai ce,
Ta hana a sake shi kana.
Wani ten tausan kaɗai ce,
Ta zamas shi gurin ya kwana.
Wani ko a jaka ɗari ne,
Ya gaza ya biya ganina.
Sai Sani ya ce a ƙirgo,
Adadin saba’in a zana.
Zai biya masu dukka tara,
Su baro jarum da kwana.
Haka kuwa an kai da yardar,
Allah mai taimakona.
Aka sayi jallabiyoyi,
Aka babba su da rana.
Aka sallami ko wannensu,
Sanadin sadakar ga nina.
Daga nan muka mai da komai,
Gun mai iko da rana.
Na ga al’ajabi a jarum,
Da ya shalake hankalina.
A awa ashirin da huɗu,
Da na yo a gidan kasona.
Na laƙanci zubi da tsari,
Na gidan firzim da kaina.
Rukun-rukuni na ɗakin,
Na tsaron laifi ganina.
Har da Ɓ.I.P. a jarum,
Rukunin manya a suna.
Ɓigiren aje mai muƙami,
Ko mai matsayi kamana.
Sanata, ɗanmajalissa,
Ko rankin tsohon gwamna.
Ƙasaitaccen siyasa,
Ko mai shahara irina.
Ba a so a haɗa su,
Da waɗan can masu ɓarna.
Tsoron da ake ta ɗauro,
Da akwai mai yin haƙona.
Kai mulki a baya,
Wani na haushinka kana.
Police ne muƙami,
Ka hore su da kuna.
To da zarar an haɗa su,
Fansa za ta gudana.
Shi ya sa aka yo sifeshal,
Ga sifeshal dai irina.
Sannan kuma na ga ɗakin,
Baƙi farkon zuwana.
Inda anka marabci baƙi,
Kan gobe a kai su rana.
Daga nan kuma sai a ware,
Kowa gurbin ya kwana.
Farko da shigarka jarum,
Sai a kai ka a ɗauki suna.
Sannan kuma sai a tuɓe,
Maka kayan duk adona.
Da waya, zobe, agogo,
Da kuɗi duka ba ka kwana.
Daga nan sai a rubuta,
Su a fayel a adanna.
Da shigarka waje na wados!
Sai a tara ku a rana.
Sai a bi ku da tambayoyi,
Me ya kawo ku da kwana.
Ni abin da ya sani kyarma,
Ba a ƙarya a sanina.
Duk abin da ya faru nan gun,
Sai a faɗe shi a baina.
Tamkar an yo asiri,
Na hanin ƙarya a baina.
Na ji wani ya ce kisa yai,
Aka kamo shi da rana.
Wani yac ce Amirobi,
Suka yo ɓaci na rana.
Wani an kamo shi ne don,
Fyaɗen yara ƙanana.
Wani fo-wan-nayin ya aika,
Wani ko yai soja gona.
Wani ko ma ɗan gida ne,
Ko ya fita in ka zauna.
Kan mako ko wata ɗai,
Zai komo gun da kwana.
Wani sane wani bizi,
Wani sungume yai da rana.
Ni da na ɗauki sata,
Sunanta guda na rana.
To ashe ta karkasu ne,
Rukuni-rukuni a jina.
Da akwai ‘yan sibarayye,
Masu sungume ko da rana.
Da akwai kuma masu wafce,
Bainar Jama’a da rana.
Haka rukunin masu sane,
Masu turmutsutsu a baina.
Da akwai mai bi na mota,
Daga baya ya shuka ɓarna.
Sai ya ce kwai nan ya sauka,
Sai ya ɗau kaya a jina.
Da akwai masu asiri,
Sai dai ɓaci na rana.
Da akwai mai haura rinka,
Ko cikinta dare koko rana.
Kowa aka tambaye shi,
Za ya bayyana tasa ɓarna.
Wani in yaƙi a buge shi,
Take sai ka jiyo bayana.
Sannan kuma can a gefe,
Mai aski tal-kwabo na.
Ba ruwa ba sabulu ko,
Aka askin nan da rana.
Mai aski sai ya duban,
Sai ya ce malam ka zauna.
Furzin Taiga ya ce mai,
A’a ai ban da ni na.
Alfarma ce ta waƙa,
Ta kai ni gurin na kwana.
Alfarmar dai ta waƙa,
Ta hana a ci zarrafina.
Don an tambayi kowa,
Hujjar zan ko ya kwana.
Ni sai aka tsallake ni,
Don sassauci a guna.
Da yamma ta yi daidai,
Ƙarfe huɗu da rabi na.
Sai a kora su a ɗaki,
Magrib Issha a can na.
Ni ko bisa alfarma,
Don tausata da ƙauna.
Nan za mu yi Mangaribba,
Mu yi Issha’i da juna.
Daga nan sai kai ni ɗaki,
Ɗakin baƙi na zauna.
In na so in yi barci,
Da akwai fa gado na kwana.
In na so in yi taɗi,
Sai in nemi abokanaina.
Burinsu su ji daga gare ni,
Burina sui bayana.
Na ji labari na laifi,
Da yas saka jim a kaina.
Na ji sirri cikin ɓarayi,
Da yak kaɗa ‘yan cikina.
Wai ashe ita kanta sata,
Bisa kaidin lokacina.
Mai yin sabe na sata,
Wai da rana yake gudana.
Loton duk magidanci,
Ya tafi nema da rana.
Sannan zai nemi kango,
Ya aje wifon da rana.
Ƙarfe ɗaya duk suna gun,
Biyu na yi sun wakana.
Sai su fantsama ofireshan,
Zuwa uku da ɗigonna.
Kan asubahi a fara,
Kiran sallar Gwanina.
Sun yi har sun ƙare aiki,
Fataken dare sun yi ɓarna.
Suka su matsalar su,
A gida in sun wakana.
Mace mai shayar da yaro,
Suka ce ita ba ta kwana.
Barcinta rabi da rabbi,
Ba wuya ta tashi arna.
Suka ce mace mattsala ce,
Daga ɗan motsi a bana.
Yanzu ta kurmama ihu,
Jama’a su fito a baina.
Ko da kuwa kai atakin,
Da abin harbi ka nuna.
In ta razana tay yi ihu,
Ko ka taffasa ko ka ƙuna.
Suka ce namiji a gunsu,
Kyanwar Lami da rana.
Suka ce haushin kare ma,
Bai kai mace ba a jina.
Labarai ba iyaka,
Wasu na manta a kaina.
In kana biye mai karatu,
An saki beli a kaina.
Duk sanda a kai kirana,
Zan je kotu da rana.
Ba na latti da fashi,
Balle in saɓa rana.
Tun jama’a na raka ni,
Har ya zam sai ni da kaina.
Daga ni sai kuma garanto,
Da ya sa hannu a kaina.
Sai kuma lauyan wajena,
Mai kare ra’ayina.
Mu uku mukai ta jele,
Haka shara’ar dai ta kwana.
Ba a kai ƙarshe ba kana,
Ba a yo ba hukunci kaina.
Da haka komai ya watse,
Sun cika buri a kaina.
Daga baya na san dalilin,
Da ya ja ɗauri a kaina.
Lokacin da a kai muƙalu,
Masana suka tauna kana.
A gidan Mumbayya Hawus,
Aka ban faifar bayana.
Mai ɗauke da dukka ƙullin,
Da a kai kanmu a baina.
Marubuci na muƙalar,
Abdallah Prof. na guna.
Wai ashe mun goyi baya,
Gun Sani Lawan na guna.
Muka tattara gangamin ‘yan,
Wasan Hausar garina.
Sannan muka gwama murya,
Muka yo waƙar gwanina.
Muka mai bai’a da waƙa,
Sanadin haka ‘yan uwana.
Fulogan Gwamnatin can,
Suka sa a saka mu rana.
Falala ta zama a jarum,
Ilimi ya samu guna.
Sanadi na zama a jarum,
Kuɓutar wasu sannadina.
Sanadi na zama a jarum,
Daraja ta daɗa gudana.
Inda nan nufi in ishewa,
Na kasa isa da kaina.
Sanadin aikin jarida,
Ko’ina su jiyo amona.
B.B.C. har da Jamus,
Murya ta Faransa ɗina.
Murya ta Amurka nan ma,
Sun bayyana cin amana.
Haka Leadership jarida,
Su Sheme sukai bayana.
Ƙungiyar kare haƙin nan,
Human Right ta yi kana.
Darajata sai ta ƙaru,
Har idanun maƙƙiyana.
Waƙar da mu kai ta ƙara,
Hasbinallahu da guna.
Tsangayar Kura, Alaika,
Tawakkalna Gwanina
Gambiza, walle-walle,
Suka fassara ƙuddurina.
Suka bayyana alkaba’in,
Manyan maciya amana.
Suka rugguza masu mulkin,
Ƙarya bisa cin amana.
Wasu sun karke da ciwo,
Na gulankoma da rana.
Wani in ji ya cire mai,
Yatsu da tsaka ta rana.
Wani ko cayel abiyuzin,
Aka iske yanai a baina.
An kama wani da macce,
Da azumi don hiyana.
Wasu sun rasa martabarsu,
Da muƙamansu da rana.
Kafin waƙar ta ƙare,
Ba in gaida maza na zana.
Musbah. M. Ahmadu,
Da Adam Kirfi na zana.
Sadi-Sidi Sharifi,
Da Bashir ɗan Ɗandagona.
Rabi’u taka lafiya,
Sai ko ni na.
Kafin rufe wagga waƙa,
Zan gai da jinin gidana.
’Ya’yan Alhajji Ladan,
Mahaifi a wajena.
Alhaji Tijjani Ladan,
Mustafa Ladan Yayana.
M. Husaini jini na Ladan,
Nasir Ladan Yayana.
Abubakari na Ladan,
Sai Shehu ƙani gurina.
Habibu da Ibrahim,
Da Husaini ƙani gurina.
Ɓarayin mata na dawo,
Lantana Faɗima Antina.
Sai Halimatu Sani Ladan,
Da Ummulkhairi dina.
Sai A’isha Sani Ladan,
Da Binta cikin jinina.
Da Khadijatu Sani Ladan,
Hauwa’u cikin jinina.
Kattume Sani Ladan,
Da Lubabatu a jinina.
Aminatu Sani Ladan,
To kun ji tsatson ubana.
Yarana a cikinsu,
Sagir Lalayyo guna.
Sanin Baba na waka,
Jallaba cikin jinina.
Ga Miftahu Lafazzee,
Isah da Sa’idu guna.
Babare yana cikinsu,
Kwanciya tashi na kwana.
Kafin rufe wanga babi,
Ba in ambaci Malamaina.
Malaman ilimin karatun-
Ƙur’ani ƙira’a da gunna.
Har da Malumman Hadisi,
Da na sirar Annabina.
Malam Muhammadu Sani,
Ɗan Sakkwato Malamina.
Allah ka jiƙansa Malam,
Sanadi nasa illimina.
Malam Umar Faƙihi,
Ɗan Sakkwato Malamina.
Malam Usumanu nawa,
Zaharaddini ta kaina.
Malam Ahmadu nawa,
Da Kabiru a Malamina.
Malam Usaini Ladan,
Da Sani a Malamaina.
Malam Idrisu nawa,
Ibrahimu Malamina.
Malamai na Furamare,
Za ni tsakura in bayana.
Headmaster M. Isah,
Malam Tajo na zana.
M. Daɓid, M. Aminu,
Malam Musa gwanina.
Malamai na Sakanni dire,
Form Master malamina.
Principal na Kawaji,
Ɗan Ƙuda laƙabinsa guna.
Maluma na Kwaleji,
H.O.D shugabana.
Hajiya Fati da Nasir,
A ciki nasu Malamaina.
Art History Aliyu,
Mungus mai taimakona.
Basic Art Ɗalhatu,
Ya koya min na zana.
Malamin General Drawing,
Ci gari ne takwarana.
Painting oil da kambass,
Malam Gausu gwanina.
Ceramic kama sculpture,
Malam Ɗanliti ɗina.
Malamin fashion Design,
Mu’azu Fagge na guna.
Sai kuma fannin Graphic,
Ibrahim Gyaɗi-Gyaɗina.
Teɗtile ba ni mance,
Malam Shehu na guna.
M. Ahmad, M. Hassan,
Duk sun koyar a guna.
Allah ya jiƙan su samin,
Da Makama Malamaina.
Nura Garba ko Monitana,
Ya wakilci abokanaina.
Ɗaliban Art and Design,
Takwarorin illimina.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.