Gabatarwa - Daga Diwanin Wakokin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    WaÆ™a zance ne mai tattare da hikima da tsari cikin sautin murya mai zaÆ™i da jan hankali, wadda ake yin ta domin isar da saÆ™o ga al’umma. Irin wannan saÆ™o shi ake kira da jigo, wanda kuma ke bijirowa ta fannoni daban-daban cikin sha’unan rayuwar al’umma. A wannan babi za a gabatar da waÆ™oÆ™in ALA ne masu jigon ilimantarwa da wa’azantarwa da kuma faÉ—akarwa. Duk da cewa waÉ—annan batutuwa suna cin gashin kansu, to ana kuma iya samun su É—amfare a farfajiyar ilimantarwa. Wato kamar yadda batutuwan wa’azantarwa kan nufi al’amuran addini, kuma na faÉ—akarwa suka fi karkata ga wayar da kai, to a gaba É—aya ana iya dunÆ™ule su a matsayin ilimantarwa. A taÆ™aice dai, jigon waÉ—annan waÆ™oÆ™i ya taÉ“o waÉ—annan muhimman batutuwa guda uku.


    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.