Murnar Salla Ta Gani

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Bisimilla Wahidin Jalla Gwani mai iyawa.

    Bisimilla Wahidin Jalla Gwani mai iyawa.

     

    Da na je garin Gumel murnar salla ta Gani,

    A cikin garin Gumel na ga abin da ya suƙe ni.

     

    Da na je garin Gumel murnar salla ta Gani,

    A cikin garin Gumel na ga abin da ya suƙe ni.

     

    Bana na ga daren kure na ba da baya,

    Sukuwa da makahon doki na ƙidaya,

    Bikin salla ta Gani na hangi shirinya,

    Na ga abin al'ajabi ya suƙe ni.

     

    Taro irin na Gani tushensa maulidi ne,

    Taro irin na Gani tushensa al'ada ne,

    Taro irin na Gani tushensa zumunci ne,

    Mahara, mafasa ƙwauri kawai suka hana ni.

     

    Bana na ga mazaje sun rikiÉ—e daga mata,

    Sai ka ce ƙudan zuma neman rai maza da mata,

    Na mai-uwa-da-wabi sukai yi maza da mata,

    Bana na yi gamo da ya so ya iza ni.

     

    Ga kiÉ—a yana ta tashi da amo na kalangu,

    Lakulaku ko da ya auno sai yai kirif da kalangu,

    Sai kiÉ—a ake ta ji babu amo na kalangu,

    Ba amo da taswirar zakaran da ka nuni,

     

    Ƙasa koko bisa anka biɗe ni a gan ni,

    Ƙasa koko bisa anka gaza da a gan ni,

    Sai fa ganinmu akai za mu wuce a mayani,

    Yanayi na Gumel ya fa ta'azzara gani.

     

     

    Wani ya gudu ya bar motarsa a baya,

    Wani ya gudu ya bar matarsa a baya,

    Wani ya gudu ya bar yaransa a baya,

    Bana an yi daren kure ya ritsa ni.

     

    Ummaru na ÆŠalhatu can aka gan shi a mata,

    U'ula da Murtala sun rikiÉ—e duk a mata,

    Motar mutum huÉ—u ta É—auko takwas da mata,

    Allah kau da baÉ—ala kada wataran ta ritsa ni.

     

    Na ga masu yunifom na tuɓewa da kansu,

    Na ga masu agaji 'yansanda an tuƙe su,

    Da Lawandi direban Hikima a cikinsu,

    Har Sagiru mai Lalaiyo ma yai tsuguni.

     

    Can na hango babba na ta waige a turewa,

    An rutsa shi da wuƙa yana ta zizzillewa,

    Ƙarfi da ƙibarsa bai hana shi ya gujewa,

    HaÉ—arin da na gan shi a ciki shi ya tsuma ni.

     

    Shi ko Garba Shehu Senior masu sayar da kaset ne,

    Tara a tara 'yan ƙwaya suka mai ne,

    Sai ihu yake ya aza yau zai mace ne,

    Kai wuya a Gumel ranar sai salla ta Gani.

     

    Shi ko Bello Gumel ya rikice a kamanni,

    Don ko yai tanadin kaji da fura za ya ba ni,

    Ga shi 'yan banalin sun rikita ni a birni,

    Ya sani babu musu yanzu gida zan wuce ni.

    Bana an yi gumi nai sharkaf ya jiƙa ni,

    Na taho nai murna gun sarkinmu Sani,

    Mahara, mafasa ƙwauri kawai suka hana ni,

    Sai na dawo gida ɓacin rai ya ƙume ni.

     

     

     

     

    Sai na tambayi kaina me ya sanya hakan ga,

    Aka ce wai mashaya suka fara hakan ga,

    Banali da roci suka sha 'yan banga,

    Suka faɗa mutane sara ya suƙe ni.

     

    Na faÉ—a na kuma Allah wadai mai maye,

    Rikita-rikita aikin masu maye,

    A watan watarana ƙarshenka hawaye,

    Allah shirya É—iyanmu daga shan shanshani.

     

    Bana in na taho kun ji gurin ajiye ni,

    Jami'a za ku kai ni a gurin ku aje ni,

    A.T.C Gumel can aka san ni da auni,

    Ilimi tarbiya can aka san a tsare ni.

     

    Masoya na Gumel kui haƙuri da zuwana,

    Wanda anka raunata ga jaje daga guna,

    Ba ni sake ma zuwa don guje a yi É“arna,

    Na bar ku lafiya sai wataran da ku gan ni.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.