Ticker

6/recent/ticker-posts

Waiyo Kaico

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Waiyo waiyo waiyo waiyo kaico!

Gambiza da gamma gamin bauta,

Waiyo kaico,

 

Ba ilimi na zamani ba,

Ba ilimi na addini ba,

Ba ƙirƙira ta zamani ba,

Mu ba kwanciya ta hankulla ba,

Mu ba rayuwa ta jin daɗi ba,

Sai dai gunguni da mungun gaba,

Sai dai hassada da aikin zamba,

Kuma ba shirya ci na addini ba,

Sannan ci da da ceto aikin zamba,

Ba shimfiɗa ta makirci ba.

 

Allah kai kaɗai ake bautawa,

Mai bautar waninka ya yo wauta,

Bauta wa waninka gamin bauta,

Rabbi tsare mu da gamin gambiza,

 

Allah kai daɗin salati dubbai,

Gun manzo Aminu har da sahabbai,

Alaye da tabi’ai da sadaukai,

Mai ƙaunar Nabiyyu ba ya ashsha,

Balle kaico.

 

An ba Tela ya yi gadon katako,

Ga Kafinta nan yana yin dako,

Masu jira ko sun yi cirko-cirko,

An yi badan-badan kwaɗon wawaye.

 

Failot anka bai wa aikin Likita,

Renon ‘yan yara sai dai mata,

In aka bai wa namiji zai wauta,

An yi ɓarin ƙasa-ƙasa don ashsha.

 

Ga Kafinta yai tsaye a mahauta,

Ya ɗauko wuƙa da jantaɗinta,

Wai zai feɗe raƙumi don wauta,

Mai ƙaryar gudu yana tatata.

 

Wai gyartai ka bai wa ƙirar mota,

Mai ƙira ka ba shi saƙar mata,

Ya zama ‘yar burun-burun don wauta,

In an yi fakafniya ya mai tatata.

 

Kai Musbahu me kake wa guɗa?

Rainin hankali ya sa na ji murɗa,  

Na hango ana rawa babu kiɗa,

Lallai ko tambaɗar ta ƙasaita.

 

Kai ALA ko me yake damunka?

Tambotsai nake gani da duhun ka,

Wai ka kasa gane zamaninka,

Dole kuwa ka zama kurar baya.

 

Rana tai nufin ta hudo kanta,

Mai kantafi na shirin damƙe ta,

Dan mutsurulle mai haƙon damƙe ta,

Kifi ya gano ka mai jar koma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments