Almuhajura

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Ala ba ku mu samu Alhaji Alhajiya,

    Ban sadaka saboda Manzon Allah.

     

    Allazi wahidun babu ya Allah,

    Ban sadaka saboda girman Allah,

    Ban sadaka saboda ƙaunar Allah,

    Ku ban sadaka saboda Manzon Allah.

     

    Inna Uwa ta ƙi ban dan Allah,

    Baba Ubana ka ban domin Allah,

    Ko gajala ko ƙanzo ban don Allah,

    Ban sadaka saboda Manzon Allah.

     

    Almajiri yana bara bayin Allah,

    Da mai ƙanzon tuwo cikin bayin Allah,

    Da Inna da Baba ko da sauran gajala,

    Ko da miya ko babu ku bani a ƙalla.

     

    Idan na je bara gidan masu da daula,

    Da an tarkato gajala fa a ƙalla,

    Su ba ni in tarkato ina murnad daula,

    Har wani lokaci su nai min umbola.

     

    Da na zauna cin abinci sai kuma ƙwalla,

    Sai na tuno martabar bawan Allah,

    Sai na tuno darrajar bayin Allah,

    Ir riƙa kuka hawaye sui ta dalala.

     

    Yanayi ne yas saka ni tilas ba wai ba,

    Barace-barace ko ina ba so ba,

    Ina fa dakon giya ba wai dan na so ba,

    Dan in tsira da kaina yunwa ba dan so ba.

     

    Gidan dandina karuwai ko ma a ina,

    Ina fa zuwa da aikatau ku ji dangina,

    Ina zuwa sayo taba dangina,

    In tsira da kaina yunwa ku ji dangina.

     

    Idan na tuno É—imin jiki na iyayena,

    Idan na tuno da tarbiya ta iyayena,

    Idan na tuno kular Uwa ku ji dangina,

    Sai nai kuka kamar yaf fita raina.

     

    Ga ni a birni cikin yankan ƙauna,

    Karatun boko harna addinina,

    Ammana fintinkau ta ma ko ta ina,

    Babun baÉ—illahu mu kai a ganina.

     

    Ba ni da tsuntsu ba tarko a ganina,

    Ba ni ga noma ba sana’ar kaina,

    Babu karatu na zamanina,

    Babu karatu na addinina.

     

    Babu kulawar Ubana ba ta Uwa,

    Babu isashshen lafiya sai ƙwawa,

    Babu isassar sutturar sanyawa,

    A yau sadakar ma babu mai bayarwa.

     

    Da sanyin sassafiya a ke tashi na,

    Da mun shafo fatiha na É—auko kwanona,

    Muna bin kan tituna da yawon maula,

    Anai mana kallon hadarin kazar bola.

     

     

     

    Uba ya kawo ni ba abincin cina,

    Hatta Mallam ma dogaron sa a kaina,

    In je ni in samo duk abincin kaina,

    Sannan fa in koma in samo wa Mallamaina.

     

    Ina ɗan ƙolo wallana ga ta kaina,

    Gardawa ma duk suna a wuyana,

    Abincin Mallam duk yana a wuyana,

    Kuma haƙƙina na wuyan Babana.

     

    Ƙafafuna babu ko silifan sawa,

    Sawayena sun fashe da tsatstsagewa,

    Riga wando dukan u sun yagewa,

    Kowa Baba da Inna É—an kacewa.

     

    Nai wani birjik da ni kamar majanuni,

    Na yi baƙi sai ka ce mashafin shuni,

    Rana ta mai da ni abin tsantsani,

    Ga annakiya dan rashin tsantseni.

     

    Gurin kwancina babu kyau Babana,

    Abincin cina babu kyau Babana,

    Ruwanmu na sha ma babu kyau Babana,

    Jiɗim wala hairan da ƙwarƙwata a jikina.

     

    Idan na yi rauni babu mai dubi na,

    Idan ba ni da lafiya nai ta kaina,

    Nike jinyar kaina da fa kaina,

    Da ganyen darbejiya fa nake jiƙona.

     

    Ina kokawa Baba je wa yauwa,

    Rayuwa ta sauya jiya ba yau ba,

    Tausai har taimako ba kowa ba,

    Inna da Baba kuy yi duban duba.

     

     

     

    Sauyin yanayi damina ko rani,

    Ko bazara ko lokacin É—ari ni,

    Ba nitsuwa ko ‘yar kaÉ—an a gare ni,

    Da Baba da Inna kani kayina ke yi.

     

    Ba zan manta da hantarar da a ke min ba,

    Kamar ba É—an Adam ya haife ni ba,

    Karatun yara yana ga Inna da Baba,  

    Yana bisa tarbiyar Uwa koko Uba.

     

    Ranar alkiyama da Inna da Baba,

    Za mu tsaya gaban Rabbi ba ashaka ba,

    Ranar baki ba zai zamo shaida ba,

    Sai dai gaɓɓai saboda ƙudira babba.

     

    Alan waƙa ƙira ya ke ga iyaye,

    Tarbiya ta ‘yan ‘ya‘yaye.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.