Auwalu Garba ɗan Borno,
Ka bi a hankali yanzu,
Sha’anin mutum yanzu,
Sha’anin amana ba.
Allah Ubangiji Rabba,
Ka agaje ni ya Rabba,
Dan in yo batu babba,
Ba da nufin nufaƙa ba.
Tsira amintaka Rabba,
Daɗa ga mursali babba,
Har sahabihi babba,
Tabi’i na ɗan babba.
Za ni batun zumunci yau,
In yi batun amana yau,
In yi batun shaƙiƙi yau,
Ba nufin in ci fuska ba.
Auwalu Garba Ɗan Borno,
Mai baituka kamar nono,
Barin giya kamar gwano,
Fargaba nishaɗi ba.
Malaku aljanu duba,
Da halittakar abba,
Ba su riƙe amana ba,
Ta yin Ubangiji Rabba.
Dubi mutum gwanin darga,
Mai ayyukansa dan burga,
Ya karkaɗa kamar izga,
Bai sadu bai amana ba.
Yau in ana biɗar ranka,
Da na kaza a ɗau ranka,
Shaƙiƙu ko amininka,
Da ina amana ba.
Yau ga ni ga ka aboka,
Harƙa muke ta san barka,
Ba na zo na ɓata ka,
Da ina amana ba.
Mun ta shi tin a yarinta,
Tare mukai makarranta,
Har muka iyo mata,
Yanzu kuma muna gaba.
Wuyanmu ya zamo babba,
Mai arziki abin duba,
Ba za a massa barka ba,
Sai aibata shi dan zamba.
Ɗayanmu mai muƙami ne,
Ku zo mu bi shi dan hau ne,
Mulki rabo na Allah ne,
Sai aibata shi dan giba.
A kan batun amana ne,
Kai ko batun zumunci ne,
Ko batun aminci ne,
Wanne ba mu kasa ba.
Auwalu marubuci ne,
Auwalu manazarci ne,
Auwalu makaranci ne,
Ba za ka kasa sharhi ba.
Baban Aminu ga saƙo,
A taskace cikin ƙoƙo,
Ba za ka kasa sharhi ba.
Baban Aminu ga saƙo,
Ka ce da ni fa ma ƙoƙo,
A taskace cikin ƙoƙo,
Ina da ba batu zamba.
Aminu ga saƙo,
Ina da ba batu zamba,
A taskace batun saƙo.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.