Sababin Mutuwar Aure

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Sababin mutuwar aure umumi a wannan zamani,

    Ku biyo ALA bisa tsinkaya ba don ya fi ku ba.

     

    Ahadun samadin sarki Tabara, Allahu nake kira,

    Wanda bai da É—iya kuma bai da mara, a wajenka nake bara,

    Rabbuna ka yi min narkon basira, waƙa zan kattaba.

     

    Rabbuna yi daÉ—in tsira karamci, da ba kai adadinsu ba,

    Ga mafi tsarki kuma mai aminci da ba ka yi kamar sa ba,

    Wanda babu tsimi ko ko dabara, ƙaunarsa na sa gaba.

     

    Hujja ta naƙalto 'yar ƙasida, ita za ku ji nan gaba,

    Wasu na ji suna furucin talauci, shi ne wai kan gaba,

    A fagen mutuwar auren garinmu, ALA bai yarda ba

     

    Wasu ko suka ce aure na ƙarya, ko auren sha'awa,

    Wasu ko suka ce aure na dole, ko aure na ƙawa,

    Wasu auren kwaikwayo da jari, jahilci kan gaba.

    Wasu na ji suna furuci da cewa, auren kashe gobara,

    Sai na ce dangi ku taho ku zauna, hankalinku ku tattara,

    Ku biyo ALA bisa tsinkaya, ba don ya fi ku ba.

     

    Mafi kyawun rayuwa Umumi, a wannan duniya,

    Ƙi da son ka fa babu kwatankwacinsu, 'ya'ya har dukiya,

    ÆŠan uwa 'ya'ya a ina ka samu, idan ba aure ka yi ba.

     

    Shi talauci ba shi a wanga tsari, in ko ba ku yarda ba,

    Sai in ce ku nazarci ƙasar Afirika, wacce ce kan gaba,

    A fage na rashin ma'adinai har, daulolin ci gaba.

     

    Ga misali ɗauki ƙasa ta Ghana, saka Nijer a gaba,

    Chadi, Mali da Kenya, Madagascar, Kamaru ban bar su ba,

    Ya ba su yi suna ba fagen mutuwar, aure ba a san su ba.

     

    In da gaske muke fa a kan talauci, dawo fa cikin gida,

    Babarawa, Igbo haÉ—a Yoruba, suna ta hada-hada,

    Katafawa ga Bendel, Igala aure ba su sau shi ba.

     

    Kau da wannan Malam ka yi duba, magabatan Unguwa,

    Wanda su suka haifi majoratinmu, ka yi duban nutsuwa,

    Talakoki suke babu shakka, aure ba su sau shi ba.

     

    'Yan uwa in dai har kun makance, to a nemo magani,

    Asahabu Rasulu abin kwatance, babu wanda muka gani,

    Ya yi saki don hujjar talauci ko don bai ƙoshi ba.

     

    Abin da ya yi ragowa zan faÉ—e shi, jin daÉ—in talaka,

    Auren sunna da É—iyar mutunci, wanda ya fi na saÉ—aka,

    Marhaban shukuran fa ku na yi wa juna, ba za fa ku gaji ba.

     

    'Yan uwa kun dai ji talaucin nan, ba a kanmu ya somu ba,

    Na yi hange ba kuma mu ba ne, a sahu fa na kan gaba,

    Iskanci babu kamar bature bai sau matarsa ba.

    Aure ni'imar bayi halala don samun nutsuwa,

    Garkuwa na tsiraici ba fasadi, hanyar ƙarin yawa,

    Kwarjini da muhibba na cikinsa, ba a ƙasƙanta ba.

     

    Kuma ga shi Ilahu ya la'anci mai auren É—anÉ—ana,

    A maza suke ko jinsi na mata, sun faÉ—a la'ana,

    Zuciya tasu ba ta nutso a kullum, ba za fa su gamsu ba.

     

    Wanda ya yi aure don kyan sura, ko domin sha'awa,

    Kyau za ya bishe sha'awa ta kauce, ba sauran yin ƙawa,

    Komai ya wuce sai dai kwatance, sai ka ce ba a yi ku ba.

     

    Wanda ya yi ƙaryar aure ku gane, ba za ya yi ƙarƙo ba,

    Masu auren dole da tauye haƙƙi, ba zai tasiri ba,

    Kun yi hangen Dala a daf da ku ne, birni ba ku kai shi ba.

     

     

     

    Wanda ya yi aure domin wadata, dukiya fa ya mallaka,

    Ya sau reshe ya kama ganye, dole zai rikito da ka,

    Tsuntsu ya tashi gami da farko, ya bar shi da ja'iba.

     

    Shi asasin aure ilimi ne, garkuwarsa ko taƙawa,

    Nan ake fa sanin haƙƙin na aure, ya zamo ba kokawa,

    Ku yi zamanku cikin daÉ—i lumana, ba za a ji kanku ba.

     

    0. Kar ka zamto sarki a gidanka, ka shigo da barazana,

    Sai ya zamma da sun ji É—uriyarka, hankalinsu ya razana,

    Ba sa nutsuwa ba sa sukuni, sai in ba su gan ka ba.

     

    Ka shigo da fushi kuma inkiyarka, gyaran murya u'um!

    'Ya'yanka su bazama É—akunansu, sai in ce maka u'uhum!

    Mata na kyarma da ganinka, kai ko ba ka damu ba.

     

    Ka shigo da salama su su amsa, kuna ta faran-faran,

    Yara na tsalle don ganinka, yau Baban na garin,

    Matarka tana haiban wa farhan, har tana kyaɓa shagwaɓa.

    In suna aiki ka shigo ka iske, É—an kakkama musu,

    Na ga kun gaji ne fa uwargidana, ka yi barkwanci da su,

    Sai su ce maka mun zama fansarka, maigida ba mu gaji ba.

     

    Hannunka riƙe da taɓa ka lashe, daga kayan marmari,

    Ku ci tare ku zauna ku yi taÉ—i, kuna alfahari,

    Da ƙauna mai ɗangon biyayya, ba irin ta su wane ba.

     

    Lokacin É—inki in har ka É—inka, to ka É—iÉ—É—inka musu,

    Harka ta karatu na wuyanka, ko ka kai ga Mudarrisu,

    In ka yi haka Malam ka rabauta, haka ake son uba.

     

    Godiya a gurin sarkin Adala, da ya sa ni na kattaba,

    Rabbu ka nufi a yi mata jin fahimta, ko a nan gun ko gaba,

    Manufar ALA fa a amfana, ba cin zarafinku ba.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.