Ticker

6/recent/ticker-posts

Adali

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Adali, Adali, Sarki adali, Sarki adali.

Amshi

Irin ginin sakarkari, Jami'a gidan wuya,

Rayuwa a duniya, ALA sai kai a hankali.

 

Rayuwa a duniya, Jami'a gidan wuya,

Irin ginin sakarkari, Aminu sai kai a hankali.

Aminu in yau a gaida kai,

Aminu dole a gaida kai,

Wataran a yi babu kai,

Ka bar ji-ji da kai,

A duniya sai a hankali,

Ka zamo mai hankali,

Mai aiki da hankali,

Ka zamto aƙili,

Aminu ko kuma adali.

 

Allahu kula da ni, ka san da ni a arziƙi,

Kar nai ƙarkon kifin ruwa, ko nai samkon bubukuwa,

Kar nai jewar kulklluwa, kula da ni ka san da ni,

Allahu mai zamani, Aminu ALA bawanka ne,

Ala bawanka ne.

 

Allah ke da magani,

Allah kuɓutar da ni,

Allah ka hayar da ni,

Makidar zamani,

Allah ka san da ni,

Alimul zamani,

Yarda na zamto aƙili,

Yanzu ga shi ina waƙa a bisa izza da ƙwarjini,

Gobe sai ka ga wanina ni na shuɗewa zamani,

Yau da gobe karyar Allah Sarki mai cimma mumini,

Allah ka san da ni,

Ka sa ni a taska ta adali,

Tasku na adali.

 

Allah tsare ni da sharrin shaiɗan kar yai ƙawa da ni,

Allah tsare ni don harshena zai halakar da ni,

Harshenka assadunka idan ka sake shi a zamani,

Shi za ya hallaka ka a ƙarshe ka goce zamani,

Ka zama daƙili, balidi ka goce zamani,

 

Alimul zamani,

Sirril zamani,

Allah ne mai zamani,

Kai ne zamani,

Tsare mu da zamani,

Zai sure mana hankali.

 

Alan zamani,

Taka tsantsan da zamani,

Cutar zuciya Allah shi ke da magani,

Ka ƙanƙame Rabbana da bauta ba ji ba gani,

Afuuwu Gafuru ne mai kyauta ba wani bunbuni,

Muna roƙon Ilahu ya ƙarfafi dukkan mumini,

Ya samu ciki na ceton Manzo sarki adali,

Sarki adali, Manzo sarki adali,

Sarki adali, sarki adali.

 

Adali, adali, sarki adali.

 

Irin ginin sakarkari, Jami'a gidan wuya,

Rayuwa a duniya, ALA sai kai a hankali.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments