Cutar Tabin Hankali

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Cutar taɓin hankali ALA ya kalla,

    Kama da kowacce cuta ikiwana,

    Ina kiran ‘yan uwa ku daina Æ™yama,

    Ga mai taɓin hankali cikin insana.

     

    Allahu sarkin abin nufin buƙata,

    Mai yau da gobe abin a yiwa bauta,

    Na durƙusa don neman buƙata,

    Ka karÉ“i saÆ™on d azan ga ‘yan uwana.

     

    Allah salati ga Sayyidil Wujudi,

    Abin yabawa da koyi Muhamudi,

    Allahu don so da ƙaunar Mahmudi,

    Ƙa’ida saÆ™on da zan ga ‘yan uwana.

     

    Baitukana akan taɓin hankali,

    Da nuna ƙyama ga mai taɓin hankali,

    Rashin kulawa ga mai taɓin hankali,

    Da yazzamo gamma gari cikin garina.

     

    Ya ‘yan uwana gamai taÉ“in hankali,

    A dai na ɗauri ga mai taɓin hankali,

    Idan kuna da masu taɓin hankali,

    Ku je ga docta ƙwararre ikiwana.

     

    Ita lalura ta mai taɓin hankali,

    Sambata yaÉ—o zuwa ga mai hankali,

    Siga ta shaƙar iska cikin hankali,

    Mu’amala ba ta sawa ikiwana.

     

    Mu muna ƙauna ga mai taɓin hankali,

    Mu koya aiki ga mai taɓin hankali,

    Mu ja su jikki da haka su san hankali,

    Allah yana basu lafiya ku tona.

     

    Cutar taɓin hankali yaro da babba,

    Maza da mata cikinsu ban cire ba,

    Jira-jirai ma sukan yi ba ƙahar ba,

    Mu zam kulwa dangi da nuna ƙauna.

     

    Musabbaban cutukan taɓin hankali,

    Suna da yalwa ƙididdigar hankali,

    Idan na zano su ƙarƙashin hankali,

    Ku bini sannu-sannu kan hankali,

    Zaku iske ba tantama aikili,

    Ba wanda yazzarci yai tabiu hankali,

    Ƙiriniyar yara na taɓa hankali,

    Kaya na maye yana taɓa hankali,

    A daina ƙyama ga mai taɓin hankali,

    Mu’amala ba tasda taÉ“in ku tona.

     

    ‘Yan yara-yara suna taÉ“in hankali,

    Manya da tsoffi suna taɓin hankali,

    Rashin na barci yana taɓa hankali,

    Baƙin cikin yana taɓa hankali,

    Mai wasu-wasi yana taɓin hankali,

    Faɗuwar gaba tana taɓa hankali,

    Yawan gajiya yana taɓa hankali,

    Mu daina ƙyama ga mai taɓin hankali.

     

    Kira nake yi ga É—an uwa akili,

    Ga asibitoci ga mai taɓin hankali,

    Gwamnati ta yo ga mai taɓin hankali,

    Inda larura aje a kai su gana.

     

    A Sokoto kwai asibitin hankali,

    Jihar Kano kwai asibitin hankali,

    Kaduna akwai asibitin hankali,

    Maiduguri, Bauchi kwai su babu É“arna.

     

     

    Asibitin Sokoto akwai kirarru,

    Na likkitoci dake horon ƙwararru,

    Na É—alibai masu son su san dabaru,

    Kula da masu taɓi a ilimina.

     

    Babbar cibiya ta masu bincike ne,

    Akwai ƙwararru a fannuka ku tona,

    In dai larurar ƙwaƙwalwa ce sani na,

    FarfaÉ—iya ma, ana wareta gunna.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.