Mu Zauna Lafiya

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Amfanin ilimi aiki da shi gaskiya ce faÉ—É—ake,

    Yau Sa'adu Zungur ke kira da amo mai karsashi.

     

    Zaman lafiya da juna,

    Zama na riƙon amana,

    Da massalaha da juna,

    Da soyayya da juna,

    Dangi mu fahimci juna,

    Mu É—au ilimi mu zauna,

    Mu yi amfani mu nuna,

    A aikace 'yan uwana,

    Ba ƙyama ba kiyana.

     

    Allah Al'raziƙu, kai ka ƙagi sani a cikin mashiyya,

    Ka zamo Al'alimu masanin sirrin sarari da ƙurya,

    Ka sallaÉ—a a yi ma bautar da sani a cikin biyayya,

    Amfanin ilimi aiki da sani bisa tsinkaya.

     

    A gani na Malamai su ya kyautu a baiwa kaso da yawa,

    A fage na gudunmawa ta a zauna lafiya da kowa,

    Haka nan kuma su ya kyautu a É—orawa laifi da yawa,

    Kan tashin tashina da rashin aiki da sani ya zauwa.

     

    Ilimi gun É—an Adam gishiri ne mai armasawa,

    Ilimi gun ɗan Adam tirgaɗar ƙarfe ke zamowa,

    Ilimi kam ginshiƙi ne kacokan gun kowa da kowa,

    Sannan aiki da shi ke fassara halayya ta kowa.

     

    Ilimi aiki da shi, shi yake saka soyayya ga kowa,

    Sai an san ilimi za a san ƙauna da ake ga kowa,

    Sai an san ilimi za a sami shigar hulÉ—a da kowa,

    Kasuwanci ko sana'a sai da sani suka haɓɓakuwa.

     

     

    Haka nan kuma malamai da sani suka ilmantar da kowa,

    Da sani suka haddasa aka sami firaku take fitowa,

    Don hakanga na É—au ra'ayi na malumma su sun fi kowa,

    Damar sadar da saƙon sada zaman lafiya ga kowa.

     

    A san ulama'u na gargarun nan masu halin yawa,

    Ba masu shiga gafaka ta malunta ba suna fakewa,

    Masu shiga inuwar mutanen kirki su laɓewa,

    Suna gwara kayin al'umma, manufarsu suke É—agawa.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.