Marainiya

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Duniya mai yayi mai abin ban tsoro,

    Haihuwar guzuma É—a uwa a kwance,

    Habawa ai idan yau mu ne gobe ba mu ne ba,

    Gobe ba mu ne ba,

    Gobe ba mu ne ba.

     

    Duba duba Aminu,

    Alan waƙa,

    Abin ban tausai,

    Gidan marayun yara.

     

    Kaliƙin talikkai,

    Rabbi sarkin tausai,

    Sarki na sarakai,

    Rabbu sarkin jin ƙai,

    Wanda jiji da kai,

    Yake a gunsa maji ƙai,

    Nai nufin waƙa tallafe ni kar nai kwaɓa.

     

    Rabbana yi salati addadi su fi dubbai,

    Gun mai girman al’umma da ke da sahabbai,

    Sayyadin gwanin karkato mabauta baibai,

    ÆŠan Amina abin ambato da ba aibi ba.

     

    Yau akala na karkata ga rainon yara,

    Lokacinda na je ni ziyara domin yara,

    Da abin ban tausai jiki ya kama kyarkyara,

    Tsarraba zan ko za a tausaya wa yara.

     

    Abin ban tausai gidan marayun yara,

    Abin ai kaico hawaye sui ta darara,

    Abin tsuma rai dagwai-dagwai ‘yan yara,

    Wasu haÉ—arin mota akay yi suka zama rara,

    Wasu ko tsinto su a kai a cikkin shara,

    Wasu ko masu taɓin hankali ka haifa yara,

    Sababi na haÉ—akarsu ba shi irgo yara,

    Wasu ‘yan jarirai a kan gadonsu na yara,

    Wasu na tatata da rarrafe ‘yan yara,

    Wasu na makarantar karatun firamara,

    Wasu an kakkai can sakandare don kara,

    Ba uwa babu uba haÉ—in gamayyar yara,

    Komi É—aya amma kamarsu bamban yara,

    Wani na zaluntar na ƙasa da shi dan ƙwara,

    Wani jarumta wanni shaggwaÉ“a ‘yan yara,

    Wani ba Æ™oshin lafiya cikin ‘yan yara,

    Wasu ko ƙoshin lafiya kamar tattabara,

    Abinci idan za a ba su tamkar fara,

    Jerin gwano suke kamar masu bara,

    Gidansu matsattse sai ka ce tattabara,

    Gidansu guda É—aya jal ku je ku yi duba.

     

    Sai naj ji hawaye yana É—osowa dodo,

    Da irin maƙudan kuɗinda ba kirdado,

    Na ji raina ya tirniƙe ina fargaba.

     

    Na tino filin ƙwallon ƙafa na tamola,

    Na tino maƙudan kuɗinda anka malala,

    Na tuno kuÉ—aÉ—en jama’a da ke zuba wa tamola,

    Zuciyata ta harziƙe kamar ba ni ba.

     

    Na tuno makaranta ta nakkasassun bayi,

    Inda kurma ko gurgu a can duka kan yi,

    Gaɓo har masu tawwaya duka kan yi,

    Ilimin zamani a gun fa sai ka duba.

     

    Makaranta tilo guda É—aya jal duba,

    Sai naj ji takaici na kama duba-duba,

    Sai nay yi aniyar za ni in yi duba-duba,

    Da wainar toya waÉ—ansu ya saba ba.

     

     

     

    Tun da na je ni gidan marayu an yo duba,

    Kuma na je ni gidan mahaukata na duba,

    Na je assibitin Kaduna duba,

    Kuma za ni gidan ‘yan siyasa in yo duba.

     

    Yau tsarabar duk abinda ni na nazarta,

    Ku yo nazarin hankali ku zo a kwatanta,

    Sa’an nan ma san abinda zai zam mafita,

    Allahu ka ban izzini na yo ba zamba.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.