Rayuwa A Duniya Tana Ban Tsoro

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi:

    Rayuwa a duniya tana ban tsoro,

    Lamarin duniya rawan ‘yanmata,

     

    Da farko ka tashi ne kana É—an yaro,

    Duk wani motsinka za ta yi masa wairo,

    Sai a yi maka tarbiya cikakken gwauro,

    Ka gane abinda duk da kai da kyau dana tsoro,

    Ka tashi da ƙarfin ƙuriciya ɗan yaro,

    Ba aikin ƙwarai bare ka wahalta.

     

    Larurarka gaba É—aya ake É—aukar ta,

    Ba ka abinci da sutura ka tufata,

    A É—ora ka a turbar sani makaranta,

    In ba ka da lafiya a kai ka ga likita,

    Muhallin kwancinka ya zamo mai tsabta,

    A ba ka kulawa mafi nagartar tsabta.

     

    Watan watara a tashi bakai ne ba,

    An sami waninka yanzu shi aka duba,

    Ba a mararinka yanzu sai É—an baba,

    Ka kama tudun hawa uba É—an baba,

    Ka zama mai yunƙurin zamowa baba,

    Sha’anin duniya rawar ‘yan mata.

     

    Da ka taka munzali na isa aure,

    A É—an Æ™uÆ™uta da ‘yan uwanka a daure,

    A sama maka ‘yar budurwarka ta aure,

    Aure fa sha’aninsa sai an daddaure,

    Sai an jure riƙe amanar aure,

    A bar ka da yau da gobe É—an tatata.

     

     

     

     

    Daga nan sai tsufa ta fara shiga ba ciwo,

    Abinda da kake yi a yanzu bashi yiwo,

    Baka tafiya ta nesa balle yawo,

    Da kai tafiya ‘yar kaÉ—an jiki yai ciwo,

    Babu kataɓus a gunka ka zama wauro,

    Ka zama sai dai ka ci abinci ka kwanta.

     

    Fuskarka buzu-buzu da gashin girma,

    Kana nan sai furfura ta bayyana ita ma,

    Ko tsayuwa in ka yo jiki na kyarma,

    Zama kwance tsayuwarka duk ba dama,

    Fata ta jikinka ta sake ga rama,

    Ruwan É“argon jikinka ya nakasata.

     

    Anan lafiya yau ta gobe da dama,

    A yau ciwo a hagun ka gobe a dama,

    Kallon nesa gunka yanzu ba dama,

    Zance in an yi sai a maimaita ma,

    Abinci cikin hikima ka É—an laluma,

    Sannan ka haÉ—iye ka É—an kikkifta.

     

    A sannu zuwa hankali komai sai an ma,

    Abinda ke wa jinjiri yanzu ake ma,

    Ya zam ko kashi ka yi sai an wankema,

    Jimɓintar lamuranka har su da zama,

    Mai ƙarfi da ƙuriciya ya koma,

    Rarrauna mar rashin lago na buƙata.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.