Allah Ya Maimaita

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Allah maimaita,

    Allah,

    Don ba mu yi ƙwara ba,

    Allah Allah,

    Shekarau gwamna Kanawa suna ta sonbarka,

    Allah Allah.

    Allah maimaita Allah,

    Don ba mu yi ƙwara ba.

    Allah Allah.

     

    Allah maimaita Allah,

    Dan ba mu yi cuta ba,

    Allah Allah.

     

    Allah maimaita Allah,

    Ba mu zo da zamba ba,

    Allah Allah.

     

    Allah maimaita Allah,

    Ba mu yi manuba ba,

    Allah Allah.

     

    Shekarau Gwamna Kanawa suna ta son barka,

    Allah Allah.

     

    Allah maimaita Allah,

    Dan ba mu yi ƙwara ba,

    Allah Allah.

     

    Shekarau Gwamna Kanawa suna ta son barka,

    Allah Allah.

     

     

     

    Me tajarribin mulki ya ba ka ya ƙara ƙara ma,

    Ya gwanin kyauta mai bayarwa da karawa,

    Allah Allah.

     

    Rabbi mun gode biɗa fa muke na ƙarawa,

    Allah Allah.

     

    Yau Kanon Dabo muna godiya muna barka,

    Allah Allah.

     

    Shekarau Gwamna Kanawa suna ta son barka,

    Allah Allah.

     

    Rabbana Allah salati ka ƙara ƙarawa,

    Allah Allah.

     

    Ga madubin nan mai shiryar da ladabtarwa,

    Allah Allah.

     

    Sayyidil kalƙi Muhammadu ɗan Ƙuraishawa,

    Allah Allah.

     

    Wanda ya yi mulkinsa ba sufani na cutawa,

    Allah Allah.

     

    Women afiyas na kalla zan yi waƙata,

    Allah Allah.

     

    Ƙarƙashin Hajiya Dakta Gaji Ɗantata,

    Allah Allah.

     

    Shugabar mata Hajiya Gaji ÆŠantata,

    Allah Allah.

     

    Zan faÉ—o aikin da Mallam ya yi a daka a daka,

    Allah Allah.

     

    Shekarau Gwamna Kanawa suna ta son barka.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.