Allah Kada Guguwar Sauyi

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi: Baƙar malafa baƙar jaraba mai shanye jinin jikin talaka,

    Allah kaÉ—a guguwar sauyi Buhari Janar karab da gari,


    Allah kaɗa guguwar sauyi Buhari janar ya karɓi ƙasa,


    Ku aje kube sauyi ya zo,

    Ku aje kube sauyi ya zo,

    Ku aje kibau sauyi ya zo,

    Ku aje kibau sauyi ya zo,

    Masu sanduna sauyi ya zo,

    Mai barandami sauyi ya zo,

    Bana kurri’a za ka aje mana fa,

    Bana kurri’a za ka aje mana fa,


    Sai godiya hamdullahi,

    Allah alhamdullahi,

    Allah alhamdullahi,


    Baƙar malafa baƙar jaraba mai shanye jinin jikin talaka,

    Allah kaÉ—a guguwar sauyi Buhari Janar karab da gari,


    Ya karɓi gari,

    Mutum na gari,

    Mu zam na gari,

    Mu bar sikari,

    Mu sam ma gari,

    Abin sabari,

    Sahibus sabari,

    ÆŠa na gari,

    Maras haÉ—ari,




    Subahanaka Rabbu mun gode mu jaddada godiya gun ka,

    Allah alhamdu gwanin Sarki kinin bauta ba ma yi maka,

    Duk yadda ka so da bayinka ba mai tuhuma a mulkinka,

    Muna tuba ga aibunmu ka yafe mana laifukka,

    Allahu ka dubi bayinka, an tashi hana mu bautarka.


    Masifu sun buwaye mu ka sauƙar manna jin ƙanka,

    Baƙin mulki na zalunci ake a ƙasarmu ba shakka,

    BaÆ™ar jam’iyya mai malafa tana son Æ™are bayinka,

    Muƙami in da adalci yana yiwuwa da yardarka,

    Ana ce ko da kafirci kana yarda ya É—aukakka.


    Muƙami in da zalunci kana rusa shi ba shakka,

    Akan ce ko da Musulunci kana hana yay yi albarka,

    Muƙamin nan da zalunci da kafirci na saɓonka,

    Muƙamin nan da zub da jini ana halakar da bayinka,

    Ƙabilanci da ninanci da bambanci ake shuka.


    Area ƙasarmu ya Allah ta zamma kufai kamar bukka,

    Ana ta bugu a kan taiki shi ko jaki yana harka,

    Ana ta kisa kamar fari ba wanda ake ganin shakka,

    DattaÉ“ai ‘yan arewarmu ciki ba wanda ke shakka,

    An karkashe maluma namu sarakar ma ana É—auka.


    Siyasar yau da cin zarafi da muzanci da cin fuska,

    Da zarar an ji sunanka Musulmi ka shige sarƙa,

    Yau taken Musulminmu ta’addanci yake É—auka,

    Ruɓewa taz zukatanmu ta sa ba wanda ke shakka,

    A sa sawu a taka mu da baubayi da mai shirka.


    A sa riga ta Islamu a yo wauta ƙazantakka,

    Sannan fa a jingina kanmu wakilai babu mai tanka,

    Burin muttuwa bayi idan mun take alhaƙƙa,

    Tutur atafau ba za mu yi ba saboda abun da mun shuka,

    Mun bar Allah maƙaginmu mafi girma da ɗaukakka.



    Mun doga yau ga wayonmu a toka yau muke shuka,

    Ba a ma ai fara komai ba har sai ka gyara bautarka,

    Mu dubi arewa lardinmu irin gawa muke shuka,

    Abin kaico da ‘ya’yanmu ake marakar kisan hauka,

    Mu yunƙura gyara kayanmu mu zaɓi Buhari mu dukka.


    Arewar babu mai tari suna tsoron gidan sarƙa,

    Sun zamto damisar kwali hayagaga a hotonka,

    Kyanwar Lami cikin É—aki ba cizo babu bautarka,

    Ruɓaɓɓu a ciki namu suna kuma ci da bautarka,

    Suna inuwa ta addini suna cutar da bayinka.


    Suna miƙa wulayarmu ga mai ƙi ay yi bautarka,

    Kamar dabba suke jan mu da zalunci muna kuka,

    An ƙona wajen karatunmu ana kishin mu ɗaukakka,

    An ƙone kasuwancinmu a yau baƙi suna shakka,

    Ba mai sha’awa ya zo gunmu da hulÉ—ar kasuwa barka.


    An zaɓi ruɓa-ruɓa namu da sunan wai wakiltakka,

    A ba su kuɗi su miƙa mu hannu ƙwarya hanu bakka,

    Tunaninsu iyalinsu su tara abin da ba tamka,

    Suna tsoron talaucewa suna shakkar zama talaka,

    Sun zaɓi zama talakkawa a ranar komuwa gunka.



    Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya a shekarar 2015, Muhammadu Buhari GCFR (General mai ritaya)


    Sun maishe mu kamar kaji a ba ka hatsi ka sa bakka,

    Da an buga tambarin zaɓe mutane babu tsoronka,

    Su sa riga su sa hula su É—au hoto suna ba ka,

    Su ce ma je ka mammanna a É—au na abinci ab ba ka,

    Da sun hau karragar mulki da ƙyar sug gane sunanka.


    Du wanda ya hau kujerar nan abun ƙinsa a ce sauka,

    Ya É—au É—amara na shiryawa da zango ya yi zai sauka,

    A hau fasali da tsarawa ana son sabuwar doka,

    Ana wai za a sabunta a yo doka da bakinka,

    Kundi na gudanuwar mulki su tsarmo sabuwar doka.





    Su daidaita da son ransu kawai don kar a ce sauka,

    Cikin demokaraÉ—iya ake son rai ake hauka,

    A mulkin nan na al’umma na zaÉ“en ra’ayin sonka,

    Mulki daga al’uma aka ce cikin zaÉ“i na son ranka,

    Ana yi don mutane ne misali ba ka ‘yancinka.


    Amma kuma ko mulukiya ba ta yi kamar haka hauka,

    Ko tsarin gurguzu malam bai kai haka ba a tauye ka,

    Jari hujja ake yi mana muƙami na saman doka,

    Da masu kuÉ—i da mai mulki sai yanda su kai a kan doka,

    An yunÆ™ura mai da mu bayi kana bauta da ‘yancinka.


    ‘Yanci na faÉ—i da bakinka a yau in ka yi kai kuka,

    Sai ka yi sa’a a Æ™yale ka da numfashi a É—aure ka,

    Idan suka so su bautar ka ka rayu kamar taɓin hauka,

    Koko É—auri na talala kana raye kamar ba ka,

    Ana raba hankula namu kamar ƙwallo a taka ka.


    Ya taka sai ya ba wancan da ya taka ya miƙa ka,

    Suna ruÉ—in tunaninmu suna hila da kuri’arka,

    Suna ƙarya ta alkawari suna raba kawunan talaka,

    A yau kowa ya É—au wifon makamin kurri’a taka,

    Mu zaÉ“i Buhari al’umma ya gyara Æ™asarmu ba shakka.


    Jininmu da martaba tamu ya zam fansa a mulkinka,

    A yau kan mage ya waye talakka ka san matakanka,

    Ka gane kurri’a taka muhallinta makaminka,

    Makamin yanke zalunci ga duk mai kai wulayarka,

    Wakilai har da dattijai ku zaɓo masu ƙaunar ka.


    Matakin kansila har kan President zaɓi mai son ka,

    Ku lura da kyau talakkawa muna zangon tsaka tsakka,

    Muna dama ta ƙarshe ne gaba ɗaya ba ragin ɗakka,

    Ƙwayaye ƙwarƙwata tamu a yo zaɓi a fisshe ka,

    Da kunne ya ji mun tsira zalunci na ‘yan iska.



    Ka lura Janar cikin tafiya akwai kaska da ke bin ka,

    Waɗannan masu bibiko su raɓe a inuwarka,

    Waɗansunsu mazalunta suna tafiya a ƙurarka,

    Su sam dama su yo mulki su cuci talakawanka,

    Allahu ka yo mana magana ka tsittsince É—iyan iska.


    Ka yi mana kariya Allah da dangina masoyanka,

    Masoya masu bin waƙa bisa lura da son barka,

    Allah ga Janaral namu ka karɓi nufinsa bawanka,

    Ya yo sanadi na cetonmu ta hanyar ba shi mulkinka,

    Ya share manna kukanmu mu bar ƙangin jinin kaska.


    Allahu ka amsa roƙonmu muna kuka da roƙon ka,

    Masifu sun buwaye mu muna kwaÉ—ayi na tanyenka,

    A nan zan sa É—igon aya a kan nusar da bayinka,

    Ka sa waƙar da nats tsara ta zam ƙaimi ga bayinka,

    Ala mai waÆ™e al’umma, masoyin sahibi naka.

    4.1 Allah Kaɗa Guguwar Sauyi- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 116)


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.