Ticker

6/recent/ticker-posts

Walle-Walle

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Walle walle,

Kuna ta ɗauki kama karya,

Idan yau mu ne,

Mu gane gobe ba mu ne ba.

 

Da sunan Rabba Ubangiji maƙagin baba,

Gwani makaɗaici mai bin Tabara bai taɓe ba,

Kai ne mai kyauta Allah ka ba ni ban raina ba,

Tsira da aminci Allah daɗawa Manzo babba.

 

Ina roƙon ka ya Rabbi dan isar Manzonka,

Ɗan Abdallah ɗa gun Amina mai kishin ka,

Dukan lamurana albarkacinsa kai zar roƙa,

Ƙaunar Manzo Ilahu sa ba zan taɓe ba.

 

Ina da bayani ya al’uma ku ɗan saurara,

Batun da nake yi idan ka ji ni kana ka lura,

Dukan jagora idan yana da niyyar fara,

Ba za ya amince da gaskiya ta bin shari’a ba.

 

Idan mu ne yau mu gane gobe ba mu ne ba,

Mu daina mugunta domin ba za ta kai mu gaci ba,

Dukan mai mulki idan ba zai yi adalci ba,

Watan wata rana a kwan a tashi ba shi ne ba.

 

Idan ka lura ai wa’adin ka zai ƙare fa,

In bai ƙare ba ka tabbata akwai mutuwa fa,

In kai zalunci a lahirar ka za ka gani fa,

Ka san Walakiri ba za ya ƙyale zalunci ba.

 

Mutum mamugunci bai yi kama da jagora ba,

Idan ya samu ba za ya tausa al’umma ba,

Burinsa kawai shi ya tara arziki dan zamba,

Ya rabba waɗansu da sana’ar su ba kishi ba.

 

Abin haushi ma batunsu gobe kama karya,

Su kama karya su ƙi wa al’umma dan hauka,

Da jagoranci suke ta ci da addininka,

Rabon shan duka ba za ya zama bi Allah ba.

 

Idan burinka kai taƙamarka shuka mugunta,

Idan ka shuka ai dole ne ka je girbe ta,

Ai idan ba ka nan ‘ya’yanka za su je girbe ta,

Abin da ka girba wanan ba za ya zarce guba ba.

 

A kan jagora nake batu ba zan daina ba,

Da dama ta kau gare shi babu sauran zamba,

Idan yai cuta Ubangiji ba zai ƙyale ba,

Jahannama na nan azzalumai ba sa kauce ba.

 

Shugaba mamugunci wannan ba za ya sam rahama ba,

Shugaba marar kirki ba za ya samu alkhairi ba,

Shugaba mai hila ko fajiri ba zai daraja ba,

Shugaba mai ƙarya mai bin sa ma ba zai ƙima ba.

 

Duka mai yin ƙarya da sharri dan ya cuci mutane,

Wanan soko ne ko in kira shi bankaura ne,

Ka ce mugunu ne baƙin azzalimi sauna ne,

Ba za mu amince azzalimi a jagora ba.

 

Shugaba mai kirki burinsa duka adalci ne,

Yai jagoranci ya mai da al’ummassa mutane,

Ya tallafi kowa ya riƙe al’ummassa tukwane,

Ba za ya sake su su tarwatse a kan hanya ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments