Your Excellency Sir

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi: Your eɗcellency sir,

    Mai ka rage a Arewa?

     

    Mafarin bayanina Ilahu gwanin suturtawa,

    Makarin masharranta waɗanda suke tsiraitawa,

    Ka tsare mu karewa daga sharri na dubawa,

    Ka shira mu shiryawa katari da watsewa.

     

    Your eɗcellency sir,

    Mai ka rage a Arewa?

     

    Your eɗcellency sir,

    Mai ya saura a Arewa?

     

    Your eɗcellency sir,

    Mai ka bar mana Arewa?

     

    Ka shirye mu shiryarwa kai manna tsari da watsewa,

    Ka tsare mu karewa da sharri na ji da nunawa,

    Mafarin bayanina Ilahu gwanin suturtawa,

    Makarin masharranta waɗanda suke tsiraitawa,

     

    Makwafa mafuskanta Ubaidu makwaikwayar kowa,

    Sayyadi madubina abin a bi ag ga dacewa,

    Na riƙe ka tsanina da so da biya in dacewa,

    Mahamudu mai bin ka wallahi fa ba shi taɓewa.

     

     

     

    Sanadi na harshena na tsinci dami ina kala,

    Na zamo abin koyi abin a kwafa a ma kalla,

    Na zamo fa sha suka yabo da hali na madalla,

    Wasu na ta Allah wadai waɗansu nata madalla.

     

    Arewa garin noma ba na ɗan waiwaya baya,

    Muna da tufar saƙa ta auduga tun a can baya,

    Muna da tsubin dala don gyaɗa zahiri zurya,

    Da su aka gina ƙasar uwa ubana ta Nijeriya.

     

    In yi waiwayen baya a kan ilimi na Arewa,

    Kafin zuwan Turai muna da abin karantawa,

    Mun san rubutawa kana mun san karantawa,

    Rubutu muna Ajami da Hausa muke fasaltawa.

     

    A har yau a can baya Arewa muna ƙasan doka,

    Ko’ina akwai sarki da masu izo a hau doka,

    Tare-tar tarwai muke hulɗa kasan doka,

    A yau mu ake suka a ƙwance a ƙas a tattaka.

     

    Karatunmu fannoni muna da sani da al’arabi,

    Ilimi da aikinsa yake isowa cikin ƙalbi,

    Kwanci da tashinka kana da abin faɗi Arabi,

    Iliminmu shakundum da babu ta inda ba ya bi.

     

    Da zuwa na Turawa suka dushe illimin Arabi,

    Suka sa na zamani a kan iliminmu na Arabi,

    Suka sanya yin mulki da aiki sai idan ka bi,

    Suka sanya ƙasƙanci ga masu ulumu Al’arabi.

     

    Suka fara kai ilimi Kudu kafin a Arewa,

    Suka ginna jami’u a Kudu da kwaleji Arewa,

    Aka samu farfesa a Kudu ko ɗai a Arewa,

    Suka miƙa ‘yancin kai a wurin leaders na Arewa.

     

     

     

    Arzikin ƙasa wancan loton na nan a Arewa,

    Mu muke da shanu fabbobi fatu a Arewa,

    Ga ƙasa a shimfiɗe don noma birjik a Arewa,

    Da dalar gyaɗa da kuɗin kaɗa aka tona man yalwa.

     

    A yau fa an wayi gari babu tana a Arewa,

    A fannin sanin ilimi fa kale ake a Arewa,

    A fannin gine-gine kufai ka kirayi Arewa,

    A fannin sana’o’i lebura mukke Arewa.

     

    A yau fa mun wayi gari ba mu gyaɗa da nomawa,

    Ba ma rini saƙar bare fa a je majemawa,

    Ba a batun ƙira da fawa fage na rinjawa,

    Kuma iggiyar mulkin Arewa ta fa suɓcewa.

     

    A haka nau’ukan daraja babu guda a Arewa,

    Arzikin ruwan teku babu ɗigo a Arewa,

    Ga wuta ta lantarki diɗum muke mu a Arewa,

    Da industries centers kwaram muke mu a Arewa.

     

    Ba rijiyar fetur guda a kakaf a Arewa,

    Kai babu ta ƙare a inda muke a Arewa,

    Ba zuciyar nema da masu kishi a Arewa,

    Your eɗcellency sir ga tambaya ka amsawa.

     

    A da can a can baya ba mu batun ƙabilanci,

    Akwai yaruka da yawa ba mu faɗan ƙabilanci,

    Muna nan da addinai ba mu kisa na minanci,

    A yanzu mun wayi gari Arewa ciki na muzanci.

     

    Baya an kashe leaders na fari da suka mulkawa,

    Loton su Sardauna Tafawa Ɓalewa Arwewa,

    Haka aka wa Janar na Ramatu Murtala nawa,

    Zuwa Sani mai rasuwa Ummar ɗa na ‘Yar’aduwa.

     

     

     

    Tuni an yi tababa a Zangon Kataf a can baya,

    Ka ɗan waiwaya baya Kaduna fa ma a can baya,

    Cikin shekara wannan a Zanko ma fa an gayya,

    Plateu da Maiduguri cikin rikici ake zurya.

     

    An rasa rayukka da sun fi gaban a ƙidaya,

    Marayu bila adadin da babu uba bare yaya,

    Your eɗcellency sir kai a zatonka sai yaya?

    Su taso cikin tsauri za ko a wanye lafiya?

     

    Iya wanda sunka gaza da kai ‘ya’ya makarantu,

    Da wanda aka hana shiga gurbi na karatu,

    Haɗa har da masu riƙe da kwalaye na karatu,

    Your eɗcellency sir bar su hakan ko ya kyautu?

     

    Kwatancinsu shuka ce da anka haƙa akai bunne,

    Ana nan ana zaune tsiro ya fito fa ba aune,

    Your eɗcellency sir kun bi Arewa kun bunne,

    Bunntayan bunne za ko ya tashi ba aune.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.