Mallam Ibrahim Shekarau Allah Ya Maimaita

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    ShimfiÉ—a: 

    Ka ceci Kanon Dabo,

    Ka kare Kanon Dabo,

    Kiyaye Kanon Dabo,

    Ka tsame Kanon Dabo,

    Ka fid da Kanon Dabo,

    Ka kau da halin bobo,

    Ka sa su a masu rabo,

    Ka kau da halin ƙwambo,

    Ka kau da halin aibo,

    Raba mu da mai zambo,

    Ka sanya Shekarau Mallam Jallah ya maimaita.

     

    Amshi: 

    Allah Ubangiji Jallah ka ceci Kanon Dabo,

    Ka sanya Shekarau gwamna Jallah ya maimaita,

    Da Sani ÆŠanlawan Limamun Allah maimaita.

     

    Allahu kai kake yarda ka so sha’anin mulki,

    Ka basuwa ka ƙarawa ai ba mamaki,

    Ubangijin baitil harami har shabbaki,

    Ka sanya Shekarau gwamna Jallah ya maimaita.

     

    Allahu kai dubun tsira har da amincinka,

    Wurin Muhammadu jagora duk bayinka,

    Da alihi da sabihi haÉ—a da waliyanka,

    Waɗanda ba su ƙosawa kan ai ma bauta.

     

    Gwamnanmu Shekarau shi jama’a suk ka zaÉ“a,

    A lokacin takarar da akai da su ɗan kulɓa,

    Ya sanya ɗan maciji tilas ya kwaɓe saɓa,

    Dogaro ga Allah jarin Allah maimaita.


    Abin da yas sa nake waƙar Allah maimaita,

    Kamar kullum na daÉ—e ina yi maku bita,

    Ku É—an tsaya in tsahirta domin na karanta,

    Dogaro da hujjojin Allah ya maimaita.

     

    Gwamnanmu Shekarau ba gurbin da bai taɓa ba,

    Gurin sha’anin ayyuka da akke ba ai ba,

    In kana musu zauna in batso roba,

    A yanzu Alan Kanawa za yai ma bita.

     

    Shi ne da gwamnatin fa da ya taimaki ‘yan fansho,

    A lokaci guda babu ka je ka yi boshosho,

    Dan tsabagen murna da na je na ga ‘yan fansho,

    Suna zubar hawaye wasu na Allah maimaita.

     

    Shi ne da gwamnatin da ya alkinta kuÉ—in taki,

    Domin a samu ingancin noma jan aiki,

    A tallafa wa mai ƙaramin ƙarfi yai aiki,

    Nan ma na ji manoma na Allah maimaita.

     

    Shine da gwamnatin da ta kwashi marasa aiki,

    A jinsinan ‘yan maza mata domin aiki,

    Aka yi musu innifom dan ingancin aiki,

    Suna ta addu’a domin Allah ya maimaita.

     

    Shi ne da gwamnatin da ta gyaggyara firamare,

    A da fa idan ka je za ka tarar fa kamar zaure,

    Babu abin zama ba alli a firamare,

    Har na ji yara suna tsallen Allah maimaita.

     

    Shi ne da gwamnatin kare mataffiya Hajji,

    Ga shi da babban gwarzo na mazowa Hajji,

    Sakattare Sani ÆŠanlawan kuma alhajji,

    A yanzu shi ya zama limamun Allah maimaita.

     

    Shi ne da gwamnatin da take shishshimfiÉ—a kwalta,

    Adon gani adon tafiyar masu hawa mota,

    Adon gari gwanin tsari birnin haihuwata,

    Mu dara muna Allah sa shi ya maimaita.

     

    Shi ne da gwamnatin da ta gyaggyara mana famfo,

    Ta say yi chlorine domin tace ruwan famfo,  

    Ta gyara injina masu tafi da rowan famfo,

    Dan hakka naj ji ‘yan birni na Allah maimaita.

     

    Shi ne da gwamnatin da ta agaji ‘yan NEPA,

    A da fa sai mu yo mako babu wutar NEPA,

    Na tuna ‘yan Fagge Kurna fa a kan NEPA,

    Suna ta addu’a Sarki Jallah ya maimaita.

     

    Shike da gwamnatin zakka har da musabiƙa,

    Ya tarkato malaman zaure a cikin halƙa,

    Ya ware kyautukan ban girma ga musabiƙƙa,

    Dan haka ‘yan Islamiyya na Allah maimaita.

     

     

    Shike da gwamnatin Shari’ar nan ta Musulunci,

    An É—ebi massana shari’a dan su yi adalci,

    Da masu faÉ—É—akarwa dan tsoronsa maceci,

    Ubangiji yana bayanka za ka maimaita.

     

    Shi ne da ‘yan adedeta sahu ‘yan Kanawa,

    Shi ne da Æ™ungiyar ‘yan Hisbar nan ta Kanawa,

    Masu tallafi dan Allah da tausasawa,
    Na ji jama’a na Allah maimaita.

     

    Na je ni tsegumi Kim domin na nazarto su,

    Nan na riƙƙe baki na yam maganaɗisu,

    An kwaikwayon baitul harami Rabbil insu,

    Don koyarwar alhazawa yanda ake bauta.

     

    Na je ga ‘yan fire serÉ“ices dan leÆ™en sirri,

    Gidan masu kisa ga gobara a cikin tsari,

    Nan na gano kalar motoci masu sururi,

    Sai nai suƙul da baki nac ce Allah maimaita.

     

    A daidaita sahu Mallam yai babban aiki,

    Dan ya giggina office gami da kayan aiki,

    Sannan ya gina É—akin bita domin aiki,

    Bala Muhammadu Ladanin Allah maimaita.

     

    Sannan na je jami’a suna Allah san barka,

    Dan na ga É—alibai na mammanna hotonka,

    Dan ka biya scholarship yas sa su su so ka,

    Suna ta sintiri da faÉ—in Allah maimaita.   

     

    Ka je assibiti maternity emergency,

    Ka je har mortuary É—an uwa emergency,

    Ka kallo aiki na Shekarau an kashe sisi,

    Sai ka zub da hawaye za ka ce Allah maimaita.

     

     

     

    Sannan emergency relief and agency,

    Ma’aikatar tallafawa ya ayyuhan nasi,

    Duk mai matsalar al’ammura a cikin insi,

    Can za ya je ya kai kuka don ai mai kyauta.

     

    Je ka gaddar Tamburawa ka sha mamaki,

    Matata ta ruwa Mallam yai mana jan aiki,

    Kwana kaÉ—an masu zauwa sai an mamaki,

    Ta yarda zai kara É—aya birni da kewayenta.

     

    Yaƙi na jiniyo sakandire ɗari da ashirin,

    Da motarsu free É—ari biyar sannan machine,  

    Na dala yalo kaf dubu da ƙari shi machine,

    Kan hakka ‘yan Babura suna Allah maimaita.

     

    Na je ma’aiktar wasanni ta sport council,

    Na samu Kano Pillars domin broadcasting,

    Da ‘yan amacuwan Kano fa ba mai ma council,

    Suna dara suna sowar Allah maimaita.

     

    Allah Ubangiji Jallah ka ceci garin Ado,

    Dan na ga takarar bana har ma da su É—an daudu,

    Da masu rawar yaraye iye carman dudu,

    Da masu gwamnatin kama karya dan cuta.

     

    Shi ne da gwamnatin da take karrama masarauta,

    Kanawa na alfahar da wannan masarauta,

    Ta Alhaji Ado Sarki mai riƙon sarauta,

    Dan hakka naj ji fadawa na Allah maimaita.

     

    Shi ne da gwamnatin da ta wanzar da security,

    Ta kau da harin ‘yan daba da masu tare titi,

    Tun zamanin Buhari Janar mai samu a titi,

    Ba ai kwatankwacin Mallam mai Allah maimaita.

     

     

     

    Dan daÉ—i da godiya a gurin Rabbul izza,

    ‘Yan fansho da kuÉ—insu su sukai tataÉ“urza,

    Sukay yi adashen gata sun hango haza,

    Su kas sayo wa Mallam form É—in Allah maimaita.

     

    ‘Yan Æ™ungiyar Æ™wadago ta Kanawanmu na Dabo,

    Su nag gano suna toroƙo wasu na ƙwambo,

    Suna ta tutiyar Mallam na Kanawan Dabo,

    Suna faÉ—in mai ta Annabi ne zai maimaita.

     

    Can na gano sansani na garasa sun haÉ—a kaya,

    A É“angare guda shi kuma zanzaro a baya,

    A wancan kuiɓin nag ga zago ya taka ƙaya,

    Na ce sakamako na cin amanar mai kyauta.

     

    Aminu É—an jaha ta Kanawa na halaliya,

    Na unguwar tudun Muri mai fatan khairiya,

    Ubangidan matasan shabbabul khairiya,

    Yake ta zakwkwaÉ—i dan É—okin Allah maimaita.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.