Garkuwa Na Matasa Doktoro Yahaya Adoza

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0. 

    Amshi

    Garkuwa na matasa Doktoro Yahaya Adoza, megida

    Fittilar gwamnoni mai ƙwarjini da niyyar gyaran al'uma.

     

    Za ni birnin Kogi in gai da mashahurin gwamna,

    Mai abin nunawa É—an Bello Yahaya Adozan al'uma.

     

    ShimfiÉ—a

    Sannu bukkar daji ubangida da halin kirki,

    Mallafar gwamnoni É—an Bello wanda ba ya raki,

    Garkuwa na matasa ne ginshiƙi maɗauka daki,

    Mai rabon ai aiki rana fitonki mudun aiki,

    Ba maza a gabanka muddin ka doshi filin aiki,

    Damina alkhairi mai lillimi da taushin aiki,

    Zakaran da Ilahu yai lamuni ya zam hamshaƙi,

    Ko ana ha mata ko ha maza a garken zaki,

    Za ya canyara cara yai fuffuka da ƙarfin Allah.

     

    Mai dare mai rana alhayyu kuma alƙayyumu,

    Ƙadiran maƘaduran mai taimakon mu mai ceton mu,

    Yarda yai daidai ne Allahu ka'imi Kayyumu,

    Zan yabon bawanka mai dogaro da ƙarfin Allah mai sama.

     

    Kan na fara nashida zan gai da MusÉ—afa gatanmu,

    Annabin da ya zamtu shuma gaba da zai cece mu,

    Sayyadul arabiyu wannan da yaz zamo haskenmu,

    Sayyidussadati nurul huda madubin dukkan al'uma.

     

    Zan yabon doktoro É—an Bello Yahaya Adoza,

    Shugaba na matasan gwamnonin ƙasa ka turza,

    Kai ku zaga Afurka ba gwamna kamar Adoza,

    Yahaya Adoza É—an Bello ka zamo buldozan al'uma.

     

     

     

    Kun ga bukkar daji toro da ke kiwo shi shi É—ai,

    Masu suka daidai ka bi su ka baje su da É—aiÉ—ai,

    Dogoronka ilahu mai bada mamlaka a yi É—aiÉ—ai,

    Masu tsoron Allah wa za ya tsorata su a jinsin al'uma.

     

    Dogaronka Ilahu É—an Bello mai hagun mai dama,

    Taka wanda kake so kana da hurrumi ga dama,

    Duk da na san halin É—an Bello ba shi son mazaluma,

    Ba ka ba zalunci ba ka shiri da mai zaluntar al'uma.

     

    Waiwaye aka ce wa ya zam ado ga mai tafiya ne,

    Babu a waigen baya sai dai a waiga tarihi ne,

    Ba a son tuna baya sai dai akan sa tarihi ne,

    Na tuno artabu kafin ka hau ka zam jagoran al'uma.

     

    Ban da baiwar Allah koko in ce saboda karama,

    Sanda kay yi mafarki an ce ka je ka zamma hukuma,

    Inda kag ga ishara za ka zamo uban al'uma,

    Ga shi nan an karɓa Allah riƙa wa Bello ya koma yak kuma.

     

    An yi tataburza ranar da kaf fito contesting,

    Jam'iyu na adawa dominka sun shiga regrating,

    Haka ‘yan jam'iyya dominka sun kusa safareting

    An buga an ƙare ka bar su yau kana kan mulkin al'uma.

     

    Lokacin da akay yo zaɓen furamare ellection,

    Ka zamo na biyu ne loton furamare ellection,

    An yi har an ƙare ka wattsake a halin tension,

    Sai fa Rabbu ya juya Sattaru Wahidul Ƙahharu mai sama.

     

    Muttuwa sababi ce duk wanda ya yi rai zai É—ana,

    Muttuwa riga ce duk wanda ya saka zai É—ana,

    Mutuwar ga guda ce amma fa sabbabinta a tona,

    Sababin mutuwa ne É—an Bello kaz zamo goga raba gardama.

     

     

     

    Addu'a ta mahaifa in suka yi ta babu mushakka,

    Ba kama da ta ummi in har ta yi ta ba wani shakka,

    Bibiya ta iyaye É—an Bello ka zame masu zakka,

    Ba su gane sahunka ɗan Hauwa kai fice hamshaƙin al'uma.

     

    Ko cikin tarihin maza waÉ—anda sun ka yi zarce,

    Sun riƙo da iyaye shi ne ya sa su sun ka yi zarce,

    Tausayi na iyaye da taimakon su ke sa zarce,

    Kun ga baban Hauwa É—an Hauwa kuma autan Hauwa É—an umma.

     

    Ka ga jajirtacce zaƙaƙuri da zatin soja,

    Ni fa in an bar ni da sai na ce da kai ma soja,

    Don rashin tsoronka da kwarjini da zatin soja,

    Ga shi hafsan soja to uban maza na son ka É—an umma.

     

    Ko a halin yanzu É—an Hauwa zan karanto lakca,

    Ko cikin gwamnoni É—an Hauwa ka É—are su da fiyuca,

    Nacaral bay neca koko shiga zubin nan kalca,

    Ni mafarkina yau ko gobe za ka ja linzamin al'uma.

     

    Duniya ta canza don yanzu taswira ta juya,

    Masu mulki yanzu zaga a da'irar duniyya,

    Yau mafi rinjaye kintaci talifin duniya,

    Duk matasa ne ke kan raggama ta jagororin al'uma.

     

    Na janar PMB mai ƙoƙarin cire mu a ƙunci,

    Maganin zalunci Buhari mai dashen adalci,

    Mu muna bayanka ƙarya ta mai shirin makirci,

    Kai da Yahaya Bello za ku gama kalau kuma sannan ku kuma.

     

    Gaisuwar first lady A’isha yar mutanen kirki,

    Ga yabo na musamman don A’isha Buharin kirki,

    Gaisuwar Yahaya ce ALA yake isarwa gunki,

    Allah ƙara zumunci ƙauna ta sami zangon maimai ak kuma.

     

     

     

    Gaisuwa ga amini chief of staff na daman gwamna,

    Edward Onoja babban aboki jigon gwamna,

    Edward Onoja chief of staff na damar gwamna,

    Ga yabonka na girma Allah ya ƙara danƙon ƙauna a kuma.

     

    Sai accountant gernaral JB abin yabon al'uma,

    Gaisuwar ban girma gun Jibbirilla Momoh shi ma,

    Sanadin Yahaya ne Alan Kano maso al'uma,

    Ke yabon ƙaunarku Allah ya ƙara danƙon ƙaunar al'uma.

     

    Sa domestic KB Kabiru na sara ma,

    Ko gurin mai girma an san ka ne a hannun dama,

    Jinjinarka da hannu sannan da baki ma na yi ma,

    Darajar mai girma ubangidanmu jagoran gun al'uma.

     

    Ba ni manta mazaje sashen jigajigan al'uma,

    Luitanant Gen. TY mai kare martabar al'uma,

    Burutai sha fama dodo na mai kisan al'uma,

    Sahibin Yahaya ne ɗan Bello haziƙi goga raba gardama.

     

    Gaisuwar Nsa nation scurity adɓiser,

    Ga yabo na yabawa gun national scurity adɓiser,

    Gaisuwa daga bakin yankan wuƙa da yafi na reza,

    Mai yabon al'uma Alan Kano maso gwamna raba gardama.

     

    Sai yabon inspector gernaral fa a sashen police,

    Gun tsaron al'uma ai dole a yaba wa police,

    Maigida Ibrahim K. Idris uban duka police,

    Sanadin Yahaya ne na miƙa gaisuwar ban girma na kuma.

     

    Gaisuwa gun Sultan mai martaba na birnin Shehu,

    Shugaba na Musulmi Sultan Sa'ad magajin Shehu,

    Sannu hizbullahi mai runduna ta gadon Shehu,

    Allah ja kwananka Allah ya ƙara soyayyarka da al'uma.

     

     

     

    Emir of Kano amir Kano Sanusin Dabo,

    Magajin Ado É—an Bayero na birnin Dabo,

    Ina gaishe ka É—awisu mai ado ba bobo,

    Allah ya riƙa ma mai taimako da kishin haƙƙin al'uma.

     

    Gaisuwar mai Zazzau É—an Sambo Allah ja kwananka,

    Sannu sarkin Zazzau mai kwarjinin da za ai shakka,

    Adalin al'uma É—an Idirisu ga caffarka,

    Mai yabon ka da waƙa Alan Kano madubi ne gun al'uma.

     

    Maƙiya gun gwamna na tabbata da duk an san su,

    Ban faÉ—in sunansu don an riga da duk an san su,

    Za su É—au kashinsu a hannu duk su kama gabansu,

    Dogaronmu Ilahu mai magani na makirci ko an yi ma.

     

    Zan rufe waƙar nan da jinjina gurin ADC,

    Shugaba takarimi da ke da matsayin ADC,

    Kwanci tashi tana nan Allah ya ja da rai ADC,

    Don ina harsashe Allah ya ƙaddara harsashen yai sama.

     

    Ga yabon DSP supoul Aminu ƙusar yaƙi,

    Maganin ‘yan banga da masu so su kai farmaÆ™i,

    Addu'ata kullum Allah tsare ku kar kui miki,

    Kui zama na lumana a kan tsare amanar gwamna ya kuma.

    Daga Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA) 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.