Farar Aniya Alamin Nasara

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Nasiru Dano sahibin gernaral shugaban ƙasarmu Buhari.

Farar aniya alamin nasara shugaban ƙasarmu Buhari.

 

Shimfiɗa

Komai nisan jifa ƙasa zai,

Sai in ba a harba kibau ba.

 

Komai tsananin wahala a gaba,

Sauƙi zai zo ba wai ba.

 

Komai nisa na gari a gaba,

Akwai wani sai ba a je ba.

 

Albasa fara ce tun asali,

Sai in ba a jure ɓara ba.

 

Mai sa sauƙi bayan tsanani,

Allhu fa bai manta ba.

 

Ko da da maƙiya sun ji gani,

Ba za su hana mu baza ba.

 

Mai baƙin ciki rintse idanu,

Za ka ga abin ba ka so ba.

 

Wannan tafiya ba ja baya,

Sai dai adaɗe ba a kai ba.

 

Shugaban ƙasa mun mubaya'a

Ba mu yi ƙasar gwuiwa ba.

 

Allah masani mai juya gari mai amsa kiran rarrauna,

Ka share hawayen talakawa mai tsarma dare daga rana,

Komai nisan jifa aka ce zai sauka a ƙasa ya kwana,

Yau zalunci ya zo ƙarshe ko da maƙiya ba su so ba.

 

Na kama ƙafa da biyar Mamman wannan da ba ay yi ya shi ba,

Manzon rahama mai adalci alaye har asahaba.

Mai umarni a game da hani kan adalci ba zamba.

Dodon ƙarya da mazalunta bai ƙyale shirin maƙiya ba.

 

Kayar daƙwara in ta kama taka tsantsan ka cire ta.

Wankin gyambo sai dai haƙuri daga ya warke an huta.

Jama'ar ƙasa in mun gane sauranmu taki na mu huta.

Baƙar aniya da baƙar jarfa ba za a kuma a gari ba.

 

Shi ingirichi sai dabbobi ba za a a bai wa mutum ba.

Idan kasko ya fashe a ƙasa sai ai tsingaro baba.

Duk sanda akai sauyi na kiɗa su masu rawa ba su hau ba.

To ya zama baubawan burmi ba zai yi ado na gani ba.

 

Aikin ga uku da Buhari yake sun isa su gyara ƙasata.

Farin farko kan sakiwrate a samu tsaro a ƙasata.

Abu na biyu hanci rashawa daidaita sahu na macuta.

Sai gyara zaman ɓeran ɗinka ɓarnar da sukai ba ta kau ba.

 

Dukkan lamari in babu tsaro ba a yi rawa da baza ba.

Arzikin ƙasa bai bunƙasa sai in da tsaro da sawaba.

Shi tsaron ƙasa shi ne farko sai dokoki ba su kau ba.

Munai maka fatan alkhairi ba za mu yi ma na zago ba.

 

 

In babu tsaro a ƙasa tamu baki ba za su taho ba.

Inda firgici a ƙasa tamu ba za mu kasa a saya ba.

In ba nutsuwa da sakin fuska ba ma yi rawar hantsi ba.

Kai ja mu mu je fagen fama mun miƙa wuya ba mu kau ba.

 

Sannan rashawa da su cin hanci in har a ƙasa ba su kau ba.

Har yau da rina a ciki na kaba don kau ba a kai ga gamau ba.

An kashe maciji an bar kai me akay yi ba shirme ba.

Duk ɗan rashawa haɗa kayanka ƙasarmu ba ka ga guri ba.

 

Har na ji waɗansu suna ta zuga haƙansu ba tay yi ruwa ba.

Burin kunya suka yi a ƙasa ba za mu bi 'yan hauka ba.

Bore suka so a yi wa gernaral suna ta zuga ba a hau ba.

Komai wahala sai mun jure ɓarnar da ku kai ba ta sha ba.

 

Na shirya bayanai kan rashawa musamman ba da gumi ba.

Na shirya bayanai kansa tsaro kacokan ba da gumi ba.

Nasiru Dano ka yi min ƙaimi in yi don na isar ba a so ba.

A kan gernaral ba ka manko sai in ba a ce kawo ba.

 

Gwamna Badaru Talamizu,

Gwamna a gari na Jigawa.

 

Gwamna Malam elruffa'i,

Gwamna a gari na Kaduna.

 

Hwamna Simon Lalong ne,

Gwamna a gari na Plateou,

 

Aminu Bello Masari ne,

Gwamna a gari na Katsina.

 

Rotimi Amechi minista ne,

A kan sufuri ba wai ba.

 

M.A Abubakar Rt,

Gwamna daga yankin Bauchi.

 

Rotimi Amechi minista ne,

A kan sufuri ba wai ba.

 

Mai Mala Buni ne sakatare,

APC kaf a ƙasata.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments