4.22 Mu Kaɗe Kumfar Ruwan Kogi - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 178)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Mu kaɗe kumfar ruwan kogi,

Bana ba ma sha da gwuiba ba.

Naɗin da kai akwai lauje,

Mun ɗebo kara da kwarkwasa.

 

Allah masanin cikin ɓoye,

Allah masanin cikin sirrai.

 

Komai ka yi ba mu ma bore,

Kai ke da tasarrafin tsirrai.

 

Kai ke da sanin abin haifa,

Macce da ciki na jarirai.

 

Allah masani na gaibiyya,

Ba ma bautarka don wasa.

 

Tsira da dubun amincinka,

A gun ragamar su limamai.

 

 Ɗan Abdullahi bawanka,

Da yaz zama tinjimi jarmai.

 

Fagen matsayi da bautarka,

Ka sa shi ya kere muƙƙamai.

 

Liwarul hamdi bawanka,

Bauta muka yi da ƙaunarsa.

 

Yau ga hannunka mai sanda,

Ba wai sanda ta duka ba.

 

Wannan sandar ishara ce,

Mai nuni ba da gaba ba.

 

Ba nuni don nifaka ba,

Ba don zambo da zamba ba.

 

Don warware makiran ɓoye

Kitso da akai da kwarkwasa.

 

In za a tuna a can baya,

Nai harsashe da ba zamba.

 

Da nak kaɗa guguwar sauyi,

Da nuni in a kai duba.

 

Kamar kumfar gaɓar kogi,

A yaryaɗe saman gwiba.

 

A yau komai yana sarari,

Mun deɓi kara da kwarkwasa.

 

Yaƙi fa ake da cin hanci,

Ɗauke zakara abin duba.

 

In ban da janar uban tafiya,

Wa ke aiki abin duba?

 

A 'ya’yan jam'iyar alade,

Ciki wanne ne abin zaɓa?

 

A 'yayan jam'iyar jaka,

Ina ne babu kwarkwasa?

 

Ko da, da na zaɓi ji 'yan bi,

Ban zaɓi tumu da yamma ba.

 

Hujjar da ta sa na zaɓe shi,

Har yau ban kai ga kuka ba.

 

Zaton da nake a kan Mamman,

Janar bai ba ni kunya ba.

 

Amma kuma guguwar sauyi,

Ta zo da kara da kwarkwasa.

 

Nama na kare da alhanzir,

Wanne ciki ba haramun ba?

 

Nama na tsaka zuwa jaɓa,

Wanne ciki ba ƙazanta ba?

 

Zatonmu wuta a maƙƙera,

Wutar ba ta tashi, tashi ba.

 

Sai ga ta kwatsam cikin kogi,

Tana bara da kai lasa.

 

Ina da karen da ba bare ba,

Tsakanin durwa har danda.

 

Ruwa ya cinye malammai,

Kadoji har da karkanda.

 

Illa dai ‘yan kaɗan baba,

A masu riƙo da alkida.

 

 

Riga aka yi da ma wando,

Kuɗin rashawa kamar wasa.

 

Tattalin arzikinmu ya karye,

Dalilin makiran zamba.

 

Halayya tamu ta ɓaci,

Dalilin shubbuha duba.

 

Kowa rashawa da cin hanci,

Ba ƙauye ba a birnin ba.

 

Ba ofis kasuwanni ba,

Kowa fa kawai a warwasa.

 

Kaɗai don an rufe boda,

Saboda tsaro da horarwa.

 

Domin samun zaƙaƙurci,

Da toshe kafa ta dambarwa.

 

Sai 'yan safarar makamanmu,

'Yan togaciya da kasuwwa.

 

Wannan da ka loda shinkafa,

Ya sa a ciki da kwarkwasa.

 

Idan har ba mu manta ba,

Muna a ciki na yaƙi ne,

 

Idan ba dai ta bodar ba,

Ta ya za ay yi yaƙin ne?

 

Shigo da makami ko kaska,

Mu gane ai ta bodar ne.

 

 

Da sa hannun ɗiyan kuka,

Ake yaryaɗa kwarkwasa.

 

Ina muka kai dabarunmu?

Ina muka kai tunaninmu?

 

Waɗanda ruwa ya sha kansu,

Ake neman fitar ranmu.

 

Mu lura gidanmu ba shinge,

Bare ƙofa ta kare mu.

 

Allahu ya amsa roƙonmu,

Ya ba mu uban da ba wasa.

 

A ɗazu muna hawaye ne,

Saboda zubar jinanenmu.

 

Muna kuka muna hurwa,

Da ƙone kasuwanninmu

 

Tashoshi har gidajenmu,

An ƙona gurin ibadarmu.

 

A keta har iyalanmu,

Muna barci kamar kasa.

 

A yau har an wuce wannan,

Muna kuka na yunwa ne.

 

Jihohi in da karrega,

A ce ai shugabancin ne.

 

Ana ƙaryar buhariyya,

Ana shukar ƙiyayya ne.

 

 

Ana daɗa maƙare talaƙa,

Kamar kura ta 'yan wasa.

 

A yau kan mage ya waye,

Mun gane naɗin akwai lauje.

 

Siyasa yau firi falo,

Mu zaɓa dai mu daddarje.

 

Mu bar kura da kirginta,

Mu doka kiɗa kiɗan jauje.

 

Mu zaɓi mutum nagartacce,

Mu ƙyale kara da kwarkwasa.

 

Rashin kunya kamar baya,

A bin ya zam kamar wasa.

 

A zaɓe mun yi in gausa,

Ciki da gara da kwarkwasa.

 

Da kako har kukus leaders,

Gara da zago da kwarkwasa.

 

Da tsatson nan gwanin selfee,

Da 'yan mata iyalinsa.

 

Ya tiki rawar tiri dandada,

Anan ya zubar da ɗa'arsa.

 

Cikinsu da mai halin taure,

Abar hidima tsaraicinsa.

 

Bai gaji rufin asiri ba,

Bindin akuya gwanin wasa.

 

 

Ƙuda kwadɗyinsa zai ja mai,

Silar kubcewa mulkinsa.

 

Iyalan zanzaro ko su-

Suke tafiyar da mulkinsa.

 

Talalabo yana barci,

Zai wayi gari a mar yasa.

 

Farar kura uwar tsoro,

Mai kadibiri da bakinsa.

 

Alu ja kullu yaumin shi,

Yana sama tsam a ra'insa.

 

Isasshe shi kaɗai ne shi,

Kowa a ƙasa yake gunsa.

 

Da son girma kamar gyambo,

Musamman ma ana susa.

 

Makasau ka take su,

Ana suka da kai kusa.

 

Su alhudahuda addini,

Yake rumfa a Shemarsa.

 

Ana jele wajen sauka,

Musabikka ta ‘yan gasa.

 

Hagunsa haɗa da damansa,

Adon gemu ka bikonsa.

 

Ai huhulahu kirarinsa,

Har in da riya a aikinsa.

 

 

Tsoron Allah abin so ne,

Allah ya san nifaƙarsa.

 

Da gyare mai yawan kuka,

Halin kuturu ɗabi'arsa.

 

Hakan take ko a hannunsa,

Na ‘yan dambe kirarinsa.

 

A can ɓarin ko ɗan kuka,

Da ke sa jefe umminsa.

 

Na dama icen giginya ne,

A nesa yake lumanarsa.

 

Ko kaska ba ta raɓarsa,

Don babu jini a fatarsa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments