Daurin Gwarmi

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Ya ilahuna mai girma, yau abin ba dama,

    Mun gaza da É—aurin kamunga,

    Har da É—aurin gwarmai.

     

    Ya Ubangiji yarda da ni Allah in zamanto jarmai,

    A fagen waƙa in zama sha kwaramniya sha gwarmai,

    Sarki Allah yarda da ni in sunce É—aurin gwarmai,

    Ubangijina Allah abin kamar ya sa in yi amai

     

    Ilahuna sallu alaihi Nabiyu Saiyidussadati,

    Muhammadu Rasulillahi Aminu Kashiful Gummati,

    Har alihi Ahlil baiti haÉ—a har sahabati,

    Maɓuɓɓuga gun sannai ainul ma'ariful jannati,

    Um!! Allah ma'ariful jannati.

     

    Ubangijina har kullum kai nake kaiwa kukana,

    Mai yaye hammi gammi na taho da buƙatuna,

    Abin da an kai a ƙasar nan ya dugunzuma tunani,

    Zan faÉ—i duk dai da an ce da ni in iya bakina.

     

    Guguwa ta sauyin sauyi - Muke nema allah,

    Guguwa ta sauyin sauyi - Kanawa bayinka.

     

    Mai ƙulafuci mai ƙwawa,

    Kana da yawan kuka,

    Mai azarɓaɓi mai tsiwa,

    Ka daina yawan kuka,

    Shugaba na 'yan shabbabu,

    Ka kau da idanunka,

    Ubangida na 'yan Ahbabu,

    Ka zare hannunka,

    ÆŠokacin yawan al'umma,

    Suna da irin taka,

    Ka É—auki hali na ko in kula,

    Kama da maƙwabtanka.

     

    Guguwa ta sauyin sauyi - Muke nema allah,

    Guguwa ta sauyin sauyi - Kanawa bayinka.

     

    Godiya nake wa Allah,

    Da ya horen baiwa,

    In kira da babbar murya,

    A domin faÉ—akarwa,

    In binciko halin alkhairi,

    A don ilmantarwa,

    In warware maƙunshin cutar,

    A gane halin wawa,

    Dole na zamo mai ƙwawa,

    Da kukan kokawa,

    Mai ƙulafuci mai mita,

    Da halin cutarwa.

     

    A ƙasarmu ana noma Allah, abin da ake nema,

    Muna da ƙiragan fatun dabbobi da ake nema,

    Ƙasarmu akwai tama da ƙarafa har robobi ma,

    Akwai mu da ramin man fetur amma ba dama,

     

    Muna da su man angurya har da man gyaÉ—a mai riÉ—i,

    Muna tasirifin man kwakwa ƙasarmu akwai faɗi,

    Muna da kwaranda gwalagwalai kar in ja ka da kauÉ—i,

    Muna tsallen baÉ—ake abin kama da 'ya'yan kwaÉ—i,

     

    Ƙasarmu akwai rana Allah ƙasar wasu ba rana,

    Da za mu yi "sunlight system" ilimin kimiyyar rana,

    Ana madari, sanyi, zafi ni'ima duka a garina,

    Sarkin alfarma ni'ima ta kare a garina,

     

    Ubangijina masifu sun yiyyi mana katutu,

    Masifu na ƙirƙira na neman sa mu mu zazzautu,

    Katankatana ce da handama ta sa muka wahaltu,

    Ya Ubangijin al'umma kai sauyin hutu,

     

    Guguwa ta sauyin sauyi - Muke nema allah,

    Guguwa ta sauyin sauyi - Kanawa bayinka.

     

    Gudun wuya da halin wayyo,

    Ya sa mu cikin wayyo,

    Mahaukata a yau a garin nan,

    An ba su cikin goyo,

    Mu waiwayo ƙananan yara,

    Da ke yin oyoyo,

    Jira-jirai ana yankawa,

    Allah ka yi sakayyo,

    Muƙabira ana tonawa,

    A yaye alawayyo,

    A yanki mamaci da gadara,

    Wayyo Allah wayyo.

     

    Guguwa ta sauyin sauyi - Muke nema allah,

    Guguwa ta sauyin sauyi - Kanawa bayinka.

     

    Na yi mubaya'a gun Ala,

    Mai rushe shirin wawa,

    Mai kira a kan a bi hanya,

    Da ba ta da gantsarwa,

    Mai ragargaza da zalaƙa,

    Na baitocin baiwa,

    Mai bindiga mai tanka,

    Da sautin harbawa,

    Ilahu ka tsare mu da sharri,

    Na duk mai cutarwa,

    Mutum da aljani sarkina,

    Tsare mu da cutarwa.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.