Ticker

6/recent/ticker-posts

Baubawan Burmi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:

Baubawan birni kasassaɓar mu ce kan zaɓen jagora iye iye.

 

Allah malikal mulki tutal mulki mantasha’u a kan mulki,

Allah mun yi zaman dirshan tamkar fitila a lokon alkuki,

Sai a ka ɗa mu a rau rayar Allah na mu na buƙatar jagora.

 

Sallu alaika Rasulullah ɗan Amina ma fi tsarkin jagora,

Ahlihi har asahaba masu biya biyar ɗafa gun jagora,

Mai alfarma da agala Ahmadu hamidun fiyayyen jagora.

 

Allah ka san kukana ka san hujjar zubar da hawayena,

Bauta ce ta canza ta ɗauko salo da tsari mummuna,

Mun bar mulkin mallaka kama karya a yau shi muka ɗora.

 

Dole in koka da tsiwa,

Dubi ƙasar nan Arewa,

Ba ilimi talakawa,

Ba mu da aikin taɓawa,

Mun zama jujin zubawa,

Tarkacen tarkatawa.

  

Dangi a duba min hanya da can da muna a mulkin mallaka,

Wahala dai aka ba bawa amma duk tsiya abinci a ba ka,

Yanzu ko gadonmu talauci ai kuɗar sa ta fi dukan ka da gora.

 

 

 

 

Talauci shi muka gado jahilci ko ya zamanto rigarmu,

Ba mu da ikon yin mulki balle mu ciro masharin kukan mu,

Mun ɗore da tumasanci mabarata muke a hannun jagora.

 

Dangi a waiwaya a duba makarantunmu daban ne da na ‘ya’yansu,

La’akari da abincinsu kama har zuwa ruwan da suke sha su,

Kai duba da makwancinsu daga nan za ka gane mungun jagora.

 

Sannan ba sa alkunya daga an doka tamburan nan na siyasa,

Kunya ba tsoron Allah su yi oda ta atamfar nan sosa,

Su mammanna gumakansu su rarraba mu ɗauke su mu ɗora.

 

A zokoto da bawa ƙarar kuka da tsuwa,

Mun shagaltu da yunwa,

Mun dishe da ƙishirwa,

Mun makance da sowa,

Allah kai ke sauyawa.

Suke tarkata yaranmu da makamai suna ta saran junansu,

Inda alamar adalci to me zai hana su cakuɗa ‘ya’yansu,

Kayan maye suka ba su su hau gidan mutum su faɗa shi da sara.

 

Kuɗin abinci ake ba ku an maishe ku sai ka ce dabbar kiwo,

Kuɗi a dumtse su a watsa ku bi kuna ta wawaso har ku ji ciwo,

Ungulu za dai fa a koma gidanki dai na tsamiya daina gadara.

 

Allah wanga kashin mulki ya yi kama guda da kashin dankali,

Na sama ya danne na ƙasa idan ya so numfashi babu dalili,

Jin daɗin su kawunansu alfarmarsu iyalansu na kibira.

 

Allah kai ka ban iko in ƙi abin gudu da fatar bakina,

Allah kai ka ban hikima in yi ragargaza da harshen bakina,

In faɗakar gun al’umma don su ƙyamata ga mulki na gadara.

 

Dangi Aminuddeen ALA na Tudun Murtala na kwanar yan Ghana,

Shugaban yan shangwago mai kulakuci da ƙawa dangina,

Shi ne ke muku adabo sai wataran idan muna da yawan kwana.  

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments