Shimfiɗa
Na ɗauki angara angara zan bangwana,
Na yi guzuri da ruwan salka kyawun tafiya mai dawowa,
Gani za ni ba ko waigowa tsarabar du’ai gun kowa,
Sai da mai rabo zan ganawa ranar rabuwa mai motsawa,
Mai motsawa mai motsa zuciyar mai bankwana,
Yau ina yin mai bankwana.
Amshi
Na ɗauki Angara na saƙala za ni-za ni ba zan dawo ba,
Na yi guzzuri da rowan salka za ni-za ni ba zan waigo ba.
Ba zan waigo ba – Ba zan waigo ba.
Wanda yai rashin taguwarsa in har ya hangi tandu zai duba,
Na yi lalube sammai ƙassai ban yi kattari da abin so ba,
Na gama bulayi na dawo na saduda ba don na so ba,
Ban yi kattari ba ina kukan zuciya tana duba – duba.
Wai garin masoyi ba nisa haka naj ji wai ba ƙarya ba,
Na yi yunƙuri har na ƙosa nai ƙulafuci na ban kai ba,
Zuciya kamar ta faso ta fito don ba tai gamo da abin so ba,
Na zub da hawaye har ya zam yanzu ma hawayen ba su zuba.
Raƙumi da akala ko gafiya za ta ja shi ba zai tsauri ba,
Na zamo kamar talalaɓo namijin da ba zai ƙarfi ba,
Jijiyar jikina har da ƙashi jinin jiki ruwa ban ɗauke ba,
Sun zamo kamar na jikin tsoho saffa-saffa ba mai ƙwari ba.
Na ji na gani na mai da gani da jin kamar ba ai ba a guna ba,
Na zamo kamar sabon hauka jinni-jinni ba ma wawa ba,
Na ji na sani inda muryata za ta kai jiki ba zai kai ba,
Rabbi ribato da abin son zuciya ba zai min sauƙi ba.
Na ɗauki Angara na saƙala za ni-za ni ba zan dawo ba,
Na yi guzzuri da rowan salka za ni-za ni ba zan waigo ba.
Ba zan waigo ba – Ba zan waigo ba.
Na ɗauki Angara – Angara zan bankwana,
Sai da mai rabo zan ganawa; ga ni rabuwa mai motsawa,
Mai motsa zuciyar mai bankwana – nai muku bankwana.
Ya rage ni kukan zuciya mai sanya zazzaɓi ba ƙarya ba,
Zuciya kamar ɗan kukkuki don baƙi ba zan muku ƙarya ba,
Ta dushe ganina ga rauni da yas saka ba zan yi kataɓus ba,
Zahirin jikina da baɗini ji nake kamar ba ni ne ba.
Ga ni na zamo mai raunin bauta da ayyukan alkhairi ba,
Ni Aminu mai yalwar saɓo Rabbi Ka sani ba ƙarya ba,
Rabbana Gafurun Arrahamar Rahimina Sarkina Rabba,
Sa ni na zamo daga tsarin masu rabo a ranar nan babba.
Rabbi kai ka san abincin zuciya da ba zan buɗe ba,
Rabbi sa na samu rabo na ganawa da ni da abin duba,
Duk da nasan na yi gamo da katar na so da abin duba,
Ya rage ni kyakkyawan ƙarshe in cika da imani Rabba.
Na ɗauki Angara na saƙala za ni-za ni ba zan dawo ba,
Na yi guzzuri da rowan salka za ni-za ni ba zan waigo ba.
Ba zan waigo ba – Ba zan waigo ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.