Kalmar So

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Ba Kalmar so ke da wuyar faÉ—i ba,

    Haƙiƙar so ke da wuyar rabewa.

     

    Kalmar so na da wuyar rabewa Ala,

    Nazarin so mai ruɗar da ƙwaƙwalwa Ala.

     

    Harƙar so taka sannu a sannu Ala,

    Fuji’ar so cira-cirye ta figa Ala.

     

    Allahu ka zammana gani da jina,

    Allahu ka zamma ni zaɓi a guna,

    Zaɓin da kammun fa Ubangijina,

    Duk yanda ka so ba ni da zaɓi sona.

     

    Barcina makaho ba ka iya rabewa,

    Mace da ciki Allah ne ke iya rabewa,

    Saƙar zuci Allah ne ke saniwa,

    Halaiyar É—an Adam ba a iyawa.

     

     Harshen baki da shi ake tsarawa,

    Da laɓɓan nan da su ake harbawa,

    Su haÉ—u su ba da sautukan isarwa,

    Da sigar nan gobe suke sauyawa.

     

    Hannun karɓa da shi ake ƙwacewa,

    Idan duba da shi ake ritsewa,

    Kunnen nan dai da shi ake jiyowa,

    Kazalika dai da shi ake bonewa.

     

    Haƙoran nan da su ake darawa,

    Haƙoran nan da su ake cizawa,

    Zukatan da su ke farantatawa,

    Zukatan yanzu sai fa ƙuntatawa.

     

     

    Da kare da are gwanda kare fa baba,

    Don ka ga kare bai rasa fa’ida ba,

    Shi ka ga are bai rasa za’ida ba,

    Da are da aradu ni ba zan rabewa.

     

    Masonin lammari a nai da so ne,

    A ƙarshensa ya birkice da ƙi ne,

    Ka so mai son ka saise-saise gane,

    Watan wataran a dawa za ku gane.

     

    Duk wata cuta da shimfiÉ—ar ta so ne,

    Makidar ta ta zarce masu aune,

    Dukkan zamba da shimfiÉ—ar ta so ne,

    Jalalarta ya zarce kalga ne É—an uwa.

     

    Mafi girman kaba’ira da zamba,

    Mafi tsananin balahira ku duba,

    Ku nutsu da kyau da so a kai turba,

    Jalalar so ta zarce masu duba.

     

    Komai ka nufa za ka iya shi baba,

    Komai tsauri da gagararsa baba,

    Dabba aljan an mallake su baba,

    Amma ba dai halina É—an Adam ba.

     

    ÆŠan Adam ne a zizziga shi,

    Ka iske gobe-gobe ya tire shi,

    Ana ga shi a yanzu-yanzu yashi,

    Ya rikiÉ—e ya rasa inda za shi.

     

    Gangar-gangar a ziga ka ga shi,

    Tiryan-tiryan a gobe ba ka ba shi,

    Lami-lami harka kuke a da shi,

    Hannun riga kuke a gobe da shi.

     

    Allah kenan mai sanya so da ƙauna,

    Da kun juya ya zama so da É“arna,

    Kalaman so a da ku nai wa juna,

    Su koma ƙi da muzgunawa juna.

     

    Allah ga ka a yanzu ga ni ga su,

    Allah ka san abin dake a ransu,

    Allahu ka mai da sharrukaina mai su,

    Raba mu da su irin na kalbisu.

     

    Iska da ruwa mai sha’awar kaÉ—awa,

    Curin hadari mai sha’awar ganowa,

    Da taurari adon gani ga kowa,

    Koren ganye abin É—ebe kewa.

     

    Da kare da are gwanda kare fa baba,

    Don ka ga kare bai wuce fa’ida ba,

    Shi ka ga are bai wuce za’ida ba,

    Da are da aradu ni bazan rabewa.

     

    Dalilan so akwai yawan sabubbai,

    Gurbin so akwai yawa ya dubbai,

    Ku bi ni a sannu kar ku zo a bai-bai,

    Zan zo da su in fasale su É—ai-bai.

     

    Abin É—oki ya zam abin soyewa,

    Abin nema ya zam abin gujewa,

    Abin marari ya zo da gundurarwa,

    Da son kwaÉ—ayi haka take zamowa.

     

    Abin fahari ya zam abin kawarwa,

    Abin ƙauna ya zam abu na yarwa,

    Abu na lale ya zam abin kawarwa,

    Da son sha’awa haka take zamowa.

     

    Mu saurara ku bi ni ba gazawa,

    In zo da batuna so abin rabewa,

    Lura baya da tsakuwa rabewa,

    Makkhon so ya kau ya zam dishewa.

     

    Alan al’umma É—an jahar Kanawa,

    Ke saƙona hikima ga kowa,

    Ba dan kushe da É“ata rai ga kowa,

    Domin faÉ—aka da so hallakarwa.

     

    Da kare da are gwanda kare fa baba,

    Don ka ga kare bai wuce fa’ida ba,

    Shi ka ga are bai wuce za’ida ba,

    Da are da aradu ni bazan rabewa.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.