Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsohuwa Ta Illaila

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Illaila, Illaila zan koma, Illaila zan komaa,

Illaila zan koma, Illaila zan koma.

 

Tsohuwa ta Illaila fara sannu-sannu,

Rabbi kai ni Illaila in gaida uwata.


Rabbu mai gamin so da jini da masoyi,

So gamon jini ke haɗuwa da masoyi,

Ainaka na Allahu ka bar ni masoyi,

Ka tsare ni Allahu zuwo na bulayi,

Ka tsare ni Allahu da so na macuta.

 

Rabbuna salati ga Habibu ruɓanya,

Shugaba tafarkin da ya sa mu a hanya,

Shugaba da arna ka yabo da gaskiya,

Shugaba madubinmu na samu a hanya,

Sayyadil arafina uban Nana Binta.

 

Tsohuwa ta Illaila tukuf a kamanni,

Tsohuwa da sassafe ta zo ta ishe ni,

Tai wajen maya biyu ta kasa ishe ni,

Tsohuwa muradinta kaɗai ta ishe ni,

Mui tozali ɗa da uwa, ta ga ɗanta.

 

A gida ta bar 'ya'yanta da ta haifa,

Wai garin masoyi ba nisa ta ce fa,

Gurin biyan buƙata rai ya zama jarfa,

Tiƙis-tiƙis ta zo ga rauni mai tsufa,

A gida ta iske ni ya zam gani ga ta.

 

Sai na zo na iske ta da uwar iyaye,

Hajiya uwata da ta sharen hawaye,

Tsohuwa ta dube ni ta zub da hawaye,

Ta ɗago tac ce mini fa ba ɓoye-ɓoye,

Yau ganinka na ida cikar manufata.

 

Ta kuma ta dube ni ta ce tambayata,

Ya gwagwarmayar nan da kake da magauta?
Na ji faɗi-tashin da kake da magauta,

Rabbana ya kare ka da kaidin magauta,

Mu fa sonka ya samu guri a zukata.

 

Nai jagwab na kalle ta kamar na yi ƙwalla,

Sai ka ce galaula auta daga gaula,

Ita kam bayaninta take babu hila,

Na taho da soyayya ɗai babu hila,

Na biyo kalamanka na keta zukata.

 

Ta yi ɗan kas kaɗan da jikinta na tsufa,

Ta yi ɗan ƙwahol-ƙwahol tarinta na tsufa,

Na baro fa Illaila na zo ga fa tsufa,

Ita 'yar mutanen Gwadabawar nan ne fa,

Babu sofanen cutarka a zukata.

 

Tsaraba ta kawo da ta zo ga masoyi,

Tsarabar dabino da aya ga masoyi,

Ba ni cin abinci a waje don shayi,

Ni da tsohuwa soyayya babu shayi,

Nai caraf na karɓe ta cike da buƙata.

 

Wasu da zumuncinsu yana a sulalla,

Wasu kuma zumuntarsu tana a salula,

Wasu kuma sayyadarsu ka sa su su ƙulla,

Gyatuma ko ta zam sha-kundum in ka kula,

Don ko Dije ta kere sa'a a zumunta.

 

Tsohuwa takan sada zumunci da sulalla,

Gyatuma tana sada zumunci da salulu,

Tsohuwa takan je da ƙafarta ta ƙulla,

Dije dai mutanen dauri ce a kula,

Dije samfurin ai dagalo a kwatanta.

 

Rabbi ka sani inda na je da muryata,

Babu yadda za ay yi in je da ƙafata,

Tsohuwa ga saƙon so na muryata,

Zai iso gare ku ko na yi wafata,

Tsohuwa ki yafe ni Kadija uwata.

 

Rabbu garkuwan nan da kake yi wa bayi,

Rabbu kattarin nan da kake yi wa bayi,

Rabbu ɗaukakar nan da kake yi wa bayi,

Rabbu fallalar nan da kake yi wa bayi,

Ni da masu sona ka sa mu rabauta.

 

Rabbi kai katanga ta tsari ga magauta,

Tsare su masu saurara ta da magauta,

Tsare su masu yin nazarina da magauta,

Rabbi ban nufin sharri ba manufata,

Ni da masu sona ka tsare mu magauta.

 

Dije 'yar mutan Gwadabawan Illaila,

Za na so na zo Illaila zuwa Gobilla,

Dije don na gaishe ki ki share ƙwalla,

Dije don na goge miki zunɗen mai hila,

Dije don na share miki zunɗen magauta.

 

Tsohuwa ta Illaila fara sannu-sannu,

Rabbi kai ni Illaila in gaida uwata.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments