Nasiru Dan Dano

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Nasiru É—an Dano dubu jiran É—ai a gayya,

    ÆŠan amana na Dutse yau kake ba hamayya.

     

    ShimfiÉ—a

    Mai bugun ramli ya bugo dariki da rayya,

    Mai dariki farin ciki ya harbo da gayya,

    Shi ko rayya ka san ka na gidan 'yan hamayya,

    Mutuwa ko baƙin ciki gidajen su rayya,

    Nasara na gidan Dano uban tara gayya,

    Ɗan amanar uban ƙasa janar masu gayya,

    Na gurin Buratai uban maza watsa gayya,

    Ɗan gaban goshi gun uban ƙasar Dutse hayya,

    Mai asarki akiza mai gadawur da gayya,

    Ga yabon Nasiru inai ciki ba hamayya.

     

    Nasara dai nake biÉ—a gurin mai rabawa,

    Wanda shi ke rabo na rahama babu kwarwa,

    Gyangyaɗi ba shi riskuwar maƙagi na kowa,

    Ko bare cinkisa da gajjiyawar gazawa.

     

    Khaliƙi godiyarka na yi na jaddawa,

    Falala wacce kay yi min ka zamto daÉ—awa,

    Nasarori suna zuwa a huce da baiwa,

    Ba barin martaba da tumbuÉ—i na kwakwalwa.

     

    Gaisuwa gun Muhammadul Aminu na kowa,

    Shugaban mursalai da annabawa na baiwa,

    Mai sahabbai kwatankwacinsu ba a kumawa,

    A nagarta zuwa riƙon amana da baiwa.

     

    Yau yabon godiya na gurguso don yabawa,

    Ga ubanmu majingina madafar fakewa,

    Masani akili cikin sarkan Arewa,

    Nuhu Mamman Sanusi Allah kareka yalwa.

     

    A sarautu na hakimai da dama Arewa,

    Daga jin ɗan amana an riga an ƙurewa,

    Daga ji É—an halaliya ake bai wa baiwa,

    Daga ji ai sarautakar ga 'ya'ya akewa.

     

    Wanda duk an ka ce wa ɗan amana ƙurewa,

    A aminci kusan ya kai magaryar tuƙewa,

    A kusanci kusan ya kai makwarwar kusurwa,

    Da aminci ake amintuwa ai daÉ—ewa.

     

    Nasiru Haladu Dano ina sabbahawa,

    ÆŠan amana na dutse tamburan sallamawa,

    Mai nagarta na gun janar na gwamnan Jigawa,

    EÉ—celency badar riÆ™on amanar Jigawa.

     

    Jinjimi ƙwai da damina ake karkaɗowa,

    Gamji sara da sassaƙa na mai sassaƙowa,

    Bai kisanka kana ba shi hana ka fitowa,

    Taka sannu ubangida da halin yabawa.

     

    Duniya an yi makka godewa tai ragewa,

    Arzikin duniya gida da mota akewa,

    Kana sannan da lafiya da masu rakawa,

    'Yan baranda gida da dawwa na tuttuÉ—owa.

     

    Sanadan nan uku da kan saka ai naÉ—awa,

    Jarumta da assali da gadon naÉ—awa,

    Ko hidimtawa jamma'a da halin yabawa,

    A rukunnen ga babu wanda ka É—ungushewa.

     

    Yau uban Dije É—an Khadija ke baitukan nan,

    Tambarina tsakar dare nake walwalar nan,

    Saƙe-saƙe da ƙulle-ƙulle har warwarar nan,

    Da kaÉ—aici nake rawar bazata a sannan.

     

     

    Ko ka ce min Alan mutan Kano É—an Kanawa,

    Gungurun gagarau ga masu son mirginawa,

    Goɗiya ta wajabta gun maƙagi na kowa,

    A yabon Nasiru Dano fa na kammalawa.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.