Bebejin Zazzau Haji Ahmad

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Bebejin Zazzau Haji Ahmad na gaishe ka.

    Ka zama tauraro da ya kere tsara albarka.

     

    ShimfiÉ—a

    Na ga ana taro har da bubuwa fa ƙudan doki.

    Na ga irin kaska rabi mai jini kuma hamshaƙi,

    Na ga uban zari masu gangami da uban aiki,

    Na ga farar saƙa ƙudan zuma ki tashi ana bin ki.

    Biki na uban gayya mai da raƙumi kuma mai doki.

    Biki na uban tafiya mai hagun da dama kare doki,

    Mai da'awar kirki É—an gidan tsatso asalin kirki.

    Mai goden jama'a ba shi bora mowa cikin É—aki,

    Sadauki hamshaƙi haji Amadu kuma garnaƙaƙi,

    Ina baitin ungo magani na mai kwauron baki,

    Bebejin Zazzau ga fa jinjinar sautin baki,

    Don ka zama tauraron da ya kere tsara sanbarka.

     

    Mai abin kyauta Allah, ba ka gyangyaɗi ko misƙala,

    Godiya ta cancanta gun matabbacin Sarki Allah,

    Ga yabo Sarki Allah da kaÉ—aitakar Jalla Jalala,

    Rabbu alhamdullahi ba ni yin kini fa a bautarka.

     

    Rabbu sanda ka ban kyauta ba sani na kowa mai ungo,

    Da na gode kai ƙari kai daɗi na kyauta shirgogo,

    Mai tulin kyauta barki wanda ya aran nisan zango.

    Godiyar nan na ƙara Rabbu ƙara narkon albarka.

     

     

    Ga yabon angon ai mai madogara da yabon Allah,

    Annabi kuma limamin masu gaskiya da riƙon sallah,

    Na yi tsanin ƙaunarka mursali maso mai son Allah,

    Duk abin da na tunkara Rabbu ƙaddara yai albarka.

     

    Maƙasudin baitocin da na kattaba wannan waƙa,

    Zan yi baitin hamshaƙi mai halin yabo da na sanbarka,

    Ahamad kuma Bebeji da akai naɗinsa nake waƙa,

    Godiya a gurin Allah da naÉ—inga Allah sanbarka.

     

    Hujjar waƙen nan an naɗin saraki hamshaƙi,

    Wanda hagun dama É—an kabar tsaka yake ba miki,

    Hagunsa jinin sarki kana kuma dama jinin sarki,

    Zan maku tabbihi ku ji talifin É—an albarka.

     

    Bebejin Zazzau mai halin yabo da na cancanta,

    Bebejin da akai babu tantama ka cancanta,

    Gado ko asali koko illimi ko ƙasaita,

    Ko kyawun hali ciki babu wanda ka zarce ka.

     

    Ya yi primary Gwale wacce ke a Kanon Dabo,

    Ya yi Barewa kwaleji ta Zaria birnin Sambo,

    Ya yi degree Scince Sociology ba ya gwanbo,

    Yai stractagy and scurity admin. Barka.

     

    Jikan Muhammadu Sani sarki na ƙasar Zazzau,

    Sarki Muhammadu Sani sarki na biyar Zazzau,

    Uwa da uba Ahmad na da salsalar sarkin Zazzau,

    Bara na zubo sarkarsa ta salsala ku ji sambarka.

     

    Gidan Malam Musa da ake kiran sa Yamausa,

    Ya haifo Muhammadu sarki na biyar Malam Musa,

    Ya haifo Dallatu Ummaru jikan Yamusa,

    Dallatu Ummaru ya haifo Malam Sidinsa,

    Shi ko Malam Sidi sarkin yaran Zazzau É—ansa,

    Shi ko Abubakar Abdu Jaji ya zamto É—ansa,

    Shi ko Abdu Jaji Ahmad Jaji ya zam É—ansa,

    Wanda shi nika wa waƙa Ahmad U Bebejin Zazzau na ya ba ka.

     

    Nasaba ta uba ke nan ɗan kabar tsaka ne hamshaƙi,

    Malam Yamusa shi ya haifi Mamman san Zazzau,

    Kana malam Yamusa shi ya haifi Idrisu sarki,

    Idris sarkin Kauru shi ya haifi Haruna sarki,

    Haruna sarkin Kauru shi ya haifi Bubakar sarki,

    Abubakar sarkin Kauru É—ansa kau Sarina sarraki,

    Sarina san Kauru shi ya haifi gimbiya Balki.

    Gimbiya Balki ko ta haifi Bebeji saraki.

    Kun ji jinin sarki da hagun da dama ba miki,

    Bebejin Zazzau haji Ahamad na gaishe ka,

    Ka zama tauraro da ya tsere tsara san barka.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.