Uban Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Hizbullahi uban Musulmi,

    Sultan Sa’ad Abubakar ne.

    Mai martaba sarkin Musulmi,

    Allah ya ƙara lafiyarka.

     

    Shimfiɗa

    Mai salsala tsatson muƙami,

    Bango madogarar Musulmi,

    Hanyar da ba ƙaya da rami,

    Adon gani gurin Musulmi,

    Allah ya ƙara ƙara ƙaimi,

    Ya ƙara lafiyar muƙami,

    Allah ya kare duk Musulmi,

    Na duniya su ƙara ƙaimi,

    Mai martabar gidan alimi,

    Ɗan Usumanu Shehu.

     

    Allah bara nake da ƙoƙo gareka don ba ka ƙi ban ba,

    Ka ce da ni idan na roƙa antal Ganiyu kuma Rabba,

    Kai ke rabo na rahhamarka don haka nan ba ka ƙi ban ba,

    Kai ke da zarafin bukatu na gurguso bida gurinka.

     

    Allah dubu-dubun salati ƙara gare shi sahibinka,

    Nurul huda Balaraben nan mai gargaɗi da kama sonka,

    Wasilatu haɗa fadhila ƙara su gun mafi kusanka,

    Haske na shiriya ga bayi tsanin shiga aljanna taka.

     

    Hisbullahi uban marayu wanda na ce uban Musulmi,

    Mabubbuga tsatson sarakai cibi na rundunar Musulmi,

    Lamlamɗo Fulɓe na Musulmi irin jinin gidan alimi,

    Allah hukkumu sa a baba murna na zo nake taya ka.

     

     

     

    Ga jinjinar gidan saɗaukai gidan da ke rabon muƙamai,

    Ga jinjinar gidan fasihai gidan da ke rabon ilummai,

    A ƙarƙashin sani da sannai, shis sa na ce gidan alimai,

    Allah ya kare martabarka sultan Sa’adu ga yabon ka.

     

    Daji da ba ayi wa shinge kwatankwaci na martabarka,

    Iya ganin ka hauni da ma na ƙarƙashi na izzanka,

    Gusun Arewa nahiya kaf! Mulkinsu na a da'irarka,

    Dagga Sokoto har Ilori ikonsu na ƙasan ƙafarka.

     

    Gagari gasa shakundum ni nai kiran ka don yaba ka,

    Idan ana dara akan ce fid da uwa ake a ba ka,

    Da ka ji san ƙasar Musulmi sultan Sa’adu ne iyaka,

    Alan Kano na san Kano ne ke tambarin yabon yaba ka.

     

    Farar uwa uwar maƙera ta ce da ni ALA na waƙa,

    Kana ta shirya baitukanka kana ta wasa masu son ka,

    Ba kai batun uban Musulmi sultan Sa’adu inuwarka,

    Goggon Sokoto tay yi ƙaimi na zaburo da baitukanka.

     

    Da fari sai na kama tsoro mai zani ce uban sarakai,

    Kamar uba gurin Musulmi ya sha gaban dukan sarakai,

    Na ƙare kambamar sarakai me za na ce wa mai sarakai,

    Ni gani ɗalibin mawaƙi dutsen kwatarkwashi na ɗauka.

     

    Ka san yabon uban sarakai sai ka kiyaye laffuzanka,

    Kana yabon uban Musulmi sai ka ƙure dukan saninka,

    Ni ga ni ba yawan sanin ba dutsen kwatarkwashi na ɗauka,

    Allah Buwayi agazanni kai lamuni a wagga waƙa.

     

    Na san a wanga zamanin dai ka ƙarfafe ni ba zuga ba,

    Kai lamuni na hikkimarka baiwa ta fussuha da hubba,

    Ga kau farin jinin mutane uwa da ɗa haɗa da baba,

    Da sun ji furuci na ALA sai zaggwaɗi da sanya barka.

     

     

     

    Na san yawa na masu waƙe garin yabo da bakunansu,

    Waɗansu sun yi sun yi dace fagen yabo da bakunansu,

    Waɗansu kuwwa bakunansu sun kai su har mahallakarsu,

    Dokin hawa na masu baki Allah tsare ni don isarka.

     

    In shirya baituka a tsare ban haura ƙa'idar sani ba.

    In burma dukka kallumana a kan sani da ba ɓata ba.

    Haƙƙin Ubangijinmu Rabba ban bai waninsa ko ɗigo ba,

    In aika saƙunan yabawa gurbinsu a ƙasanta doka.

     

    Angon Nabila na yaba ka murna na zo ni in taya ka.

    Sarauniya gidan sarakai Hajja Nabila kin ji waƙa,

    Waƙar ubangidan sarakai cikin dubu ba ta yi tamka,

    In har Nabilatu ta karɓa ‘ya’yanta za su sanya barka.

     

    Baban Fatima mai sarauta sarki Sa’adu mai Musulmi,

    Baban Amiru Ussumanu Sultan Sa’adu mai muƙami,

    Baban Abubakar Sa’adu Walid Allah ya ƙara ƙaimi,

    Uba gurin amira Maryam da Nana Dija na yaba ka.

     

    Ga salsalar jinin sarakai tun daga Shehu Fodiyo ne,

     

    Tushen sarautakar Fulani Shekh Usumanu Fodiyo ne,

     

    Bayansa Shehu Fodiyon ne sai ɗansa Bello yaɗɗare ne,

     

    Sarkin Musulmi Bello ya hau Sultan na biyu ka'imi ne,

     

    Bayansa ragamar Musulmi sai ɗan Atiku Bubakar ne,

     

    Sultan Abubakar Atiku zaƙaƙuri abin yabo ne.

     

    Sannan Aliyu babba ya hau shi ma jinin sarautakar ne.

     

    Sai ɗan Atiku Amadu kau, ya gaji karragar hakan ne.

     

    Sarki Ahamadu Atiku, mai martabar da ba shi bone.

     

    Sannan muhammadu Atiku, ya gaji karraga a zaune.

     

    Bayansa sai Aliyu sarki Sultan Ali karami shi ne.

     

    Sai ɗan Rufa'i Amadun nan Ahmad Rufa'i shi ya zaune.

     

    Sannan Abubakar na Raba ya gaji karraga a zaune.

     

    Mu'azu Bello na tsuminsa bayansa sai ya hau a zaune.

     

    Ban zamanin Mu'azu Bello sai ummaru Ali a zane.

     

    Sai Abdurrahaman Atiku ya hau gadon sarautakar ne.

     

    Muhammad Attahiru na ɗaya, ya gaji ɗan Atiku zaune.

     

    Muhammad Attahir na biyu ya gaji na ɗaya sukwane.

     

    Daga wajen sai Maiturare Muhammad mai Turare gane.

     

    Ya karɓi ragamar Musulmi, bayansa Tambari a zane.

     

    Muhammad Tambari saraki, ya zauni karraga a zaune.

     

    Sultan Hasan na gun ma'azu, ya karbi martaba a zaune.

     

    Sai sir Abubakar na uku, ya hau ya ja sahun mutane.

     

    Sai Ibrahimu Dasuƙi Sultan ya zam ya ja mutane.

     

    Sultan muhammad Macciɗo, ya karɓi ragga a zane.

     

    Sai jijjige uban Musulmi Mamman Sa’ad jarumi ne.

     

    Rumfar gidan jinin amirai Hizbullahi tugagari ne.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.