6.19 Bakan Dabo - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 264)

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Bakan dabo san kano ɗan baiwa,

    Ɗan Abdallah lafiya takawa.

     

    Ɗan Abdallah san Kano takawa,

    Abin bugun gaban Kano da Kanawa,

    Marmara ƙashin ƙasa ɗan baiwa,

    Bango ne majingina gun bawa,

    Matokara ta masu son tasawa,

    Jeji ka fice gaban shinge wa,

    Hadari sa gabanka ba a hanawa,

    Madubin sarakuna na arewa,

    Sha kallo da armashin dubawa,

    Mai kallonka ba shi nuna gazawa,

    Ɗan Bayero fahari ga Kanawa.

     

    Ɗan Abdallah gaida tilon sarki,

    Ko taron sarakuna da saraki,

    In ka fito cikinsu ba cika baki,

    Komawa suke kamar 'yan tsaki,

    Dagatai sukke in fa ga takawa.

     

    Bakan Dabo na kira shi barade,

    Don aikinsa ne a yau ya karaɗe,

    Ɗan Abdallah hadimi mai lugude,

    Da ayyuka na khairu duk ya karaɗe,

    Birnin Dabo lafiya ɗaukawa.

    Ɗan Bayero kai daban a saraki,

    Dubi shigarka na saka mana ɗoki,

    Sarki mai hawa na ban mamaki,

    Al'amuranka kwai abin mamaki,

    Mai ɗebe hason Kano da Kanawa.

     

     

     

    Na nutsa bincike a harka tawa,

    Na gaza tadda mai sarautar baiwa,

    Mai mulki ya san Kano na Kanawa,

    Mai tsari ya san Kano na kanawa,

    Ban isko ba san Kano ɗan baiwa.

     

    Sarkin nahiyar Kano mai girma,

    Mutan garinka na ganinka da kima,

    Maƙwabtansu na ganinka da kima,

    Baƙi na jahar Kano na yi ma,

    Fatan ƙara lafiya a Kanawa.

     

    Dattijai suna Allah ya tsare ka,

    Mattasa suna Allah kare ka,

    'Yan mata suna Allah sambarka,

    'Yan yara suna Allah kiyaye ka,

    Mai Kano lammarinka sai dai baiwa.

     

    Farin gani abin fahar ga Kanawa,

    Sha waƙe, yabo kirarin baiwa,

    Waƙoƙinka sun wuce ƙirgawa,

    Mai wasa ka sai fa ya dagewa,

    In ko ya ƙiya ya yo dambarwa.

     

    Mai horo abi Allahu buwayi,

    A lafiya toya matsafan bayi,

    A lafiya sadauki marrashin shayi,

    Hadari sa gabanka ba wani shayi,

    Gun haƙuri damo a sanka da sanyi,

    Mahassadanka sun gaza da bulayi,

    Mai taimako gurin Musulmin bayi,

    Ka yi taka ka yi ta ragwayen bayi,

    Sarki Alhaji da shi ka yi koyi,

    Sarki Ussuman da shi ka yi koyi,

    Sarki Innuwa da shi ka yi koyi.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.