Jabbama Marafa Abubakar

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    ShimfiÉ—a

    Allah ya riƙa maka,

    Allah ya taya maka,

    Jaɓɓama na ce maka,

    Turmi ka ke sha daka,

    Tirmin luguden daka,

    Hatsi sha sussuka,

    Gamji sha sassaƙa,

    Bai'a aka ma duka,

    Ba wanda ya ja maka,

    Yau ga ni da baituka,

    Marafa a kai maka.

    Marafa Abubakar Allah ya yi maka É—aukaka.

     

    Amshi

    Marafa abubakar na zo nake yi wa tambura,

    Jaɓɓama Abubakar Habu Marafa garin Kano.

     

    Rabbun nasi mai duka wajenka nika zuwa bara,

    Mai ba ni a duniya shi ne zai ba ni a lahira,

    Mulkinsa daban yake Allahn da na yi wa kabbara,

    Allahu abin riƙo wajensa ne muka tattara.

     

    Allah daÉ—a darraja wajen Habibu madogara,

    Wannan da mu kai riƙo da sunna tai muka dogara,

    ÆŠan Abdu majingina ga tsani gunsa na tokara,

    Ƙauna ta zamar mani hujja ranar tsayuwar jira.

     

    A yau tuna baya zan yabon ubanmu a nan Kano,

    Allah ya jiƙan maza Allah jiƙan Marafan Kano,

    Allah ya riƙan Habu wanne? Na yau Marafan Kano,

    Gurbin na ubanmu ne Habu a kanka ta mirgino.

     

     

     

     

    Mafara a nan Kano na fari sai Sule Minjibir,

    Marafa garin Kano na biyu É—an Sule Minjibir,

    Bara in yi waiwaye ado na mai tafiya zubur,

    In waiwayi talifin Marafa É—an Sule Munjibir.

     

    Marafa sarautaka a Sokkoto aka yo aro,

    Marafa a Sokoto ba a naÉ—a ta ga makkwaro,

    Marafa sarautaka ba a naÉ—a wa madankaro,

    Sai É—an babban gida ake naÉ—a masa kwarkwaro.

     

    Shekaru casa'in da bakwai akai Marafa a Sokoto,

    Tun alif da É—ari tara ashirin Marafa a Sokoto,

    Mu alif da É—ari tara da sittin ta zo daga Sokoto,

    Shekaru hamsin da huÉ—u a nan Kano daga Sokoto.

     

    Habu Sule Minjibir da naj ji za a naÉ—i Kano,

    Cikin rukunin naÉ—i cikinsu har Marafan Kano,

    Sai nai kasaƙe na ji wa an ka ba Marafan Kano,

    Domin na yi binciken hujjar naÉ—in Marafan Kano.

     

    Habu Sule Minjibir ta faÉ—a kan Marafan Kano,

    Da naj ji batun haka sai nai caffa ga uban Kano,

    Sara ya yi kan gaɓa Habu Sule Marafan Kano,

    Dukkan rukunai cicif sun hau Habu Marafan Kano.

     

    Sai É—an babban gida ake yi wa Marafan Kano,

    Sai mai tsarkin hali ake yi wa Marafan Kano,

    Sannan ƙasurgumi ake bai wa Marafan Kano,

    Mai tausan jamma'a yake zama Marafan Kano,

     

    Mai tanyon jamma’a ake saka Marafan Kano,

    Jajirtaccen maza yake zama Marafan Kano.

    Gawurtaccen maza ake yiwa Marafan Kano,

    Habu Sule Minjibir ka cancanta Marafan Kano.

     

     

     

    Farko daga assali Habu ka kai maƙurar yabo,

    Jini na sarautakar sarkin Fulani abin yabo,

    Ayuba uban maza kakan Abu Sule sha yabo,

    Sarki Sulemanu ne ya ba shi kun ji abin yabo.

     

    Marafa Abubakar fannin sanin ilimi kuma,

    Jaɓɓama Abubakar harɗo ka zarci fa gardama,

    Harɓard uniɓasity ka je ka sami wajen zama,

    Dakta aka ba ka can fannin sanin sana'u kuma.

     

    Landon da su Jamani ka je ƙarin ilimi kuma,

    Ka sam gindin zama gogayya ka yi ta haƙƙima,

    Oil, and gass a can ka san makamarsu kuma,

    Harkar inÉ“estment hada-hadar jalli kuma.

     

    Kafin haka nan a Rimi City yay yi furamare,

    Barewa Kwaleji can Habu ya yi ta ya ƙarƙare,

    BUK nan Kano Habu ya yi ta ya ƙarƙare,

    Sannan uniÉ“ersity Abuja ya yi ya Æ™arÆ™are.

     

    School of Managment Kellogg Habu ya yi ya dire,

    Chikago America Habu ya je shi fa ya ƙware,

    Oɗford Uniɓasity London Marafa ya ƙarƙare,

    Ya san ilimin hagun ya san na dama badagire.

     

    Fagen hidimar ƙasa Abu Marafa fa ya ƙure,

    Zango na mu'amilla Habu Marafa ba tsambare,

    Aikinsa fa bai faÉ—o yawan ya kai na ruwan dare,

    San nan gaba za ni zo da ayyukansa a yo kure.

     

    Allah ya jiƙan maza Sule Marafa na gun Habu,

    Allah ya jiƙan maza wakili Abba na gun Habu,

    Yaya a gurin Habu wakili Abba maso Habu,

    Allah daÉ—a rahhama a kabbarinsu jinin Habu.

     

     

    Na gai da uban ƙasa limami mai malafar Kano,

    Sarkin mai taguwa sanusi na biyu mai Kano,

    NaÉ—in da ka wa Habu wannan naÉ—i Marafan Kano,

    Allah ya daɗo maku ƙauna da son jama'ar Kano.

     

    Zan gai da shaƙiƙanai na gu Habu Marafan Kano,

    Baaba darman sahu na fari ni fa na zayyano,

    Baaba darman a yau Habu shi ne Marafan Kano,

    Murna na taya ku ni Aminu ALA garin Kano.

     

    Da É—an Isan Kano cikin sahu Marafan Kano,

    Cikinsu abokanai nasa É—an Isa na nan Kano,

    Murna na taho maku Habu shi ne Marafan Kano,

    Allah ya riƙa masa Allah ya armasa ɗanɗano.

     

    Captain Ado na sa Ado karaye a yabo,

    Captain pilot ina taya ku murna da yo yabo,

    Malam Nasir Gumel ALA ne ke baitin yabo,

    Murna ta Abubakar Abu Marafa abin yabo.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.