‘Yan Mazan Faman Najeriya

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi 

    Sojojin Nijeriya

     

    Shimfiɗa

    Mun yaba jama'ar Nijeriya,

    Ga amanar ‘yan Nijeriya,

    Kun tsare lardin Nijeriya,

    Ku tsare ‘yancin Nijeriya,

    Da iyakokin Nijeriya,

    Da haƙoƙin ‘yan Nijeriya,

    Rayukan ‘ya’yan Nijeriya,

    Malu wal banuna gaba ɗaya.

     

    Daga amo har infantari ba kama da na ‘yan Nijeriya,

    Atilare mazan Nijeriya ba kwatancin 'yan Nijeriya.

    Daga airfouse har naɓyn ruwa ba kama da na ‘yan Nijeriya.

    Sanin makamar aiki jimmiri ba a kaiku ba ‘yan Nijeriya.

     

    Ko a rawar sojan nan farati kun yi zarce ‘yan Nijeriya.

    Kar aje ga batun atisaye nan ku kai uwa kuma har da makarɓiya.

    Kafatan duk babu ragin daka ba kamarku kakaf Ifirikiya.

    Ga shi taken ‘yan Nijeriya ya fi daɗi kaf Ifirikiya,

     

    Kun zamo giwar namun dawa garkuwar yankin ifirikiya.

    Nasarar yaƙin Laberia sai da sojojin Nijeriya.

    Nasarar yaƙin Saraliyon sai da sa hannun Nijeriya.

    Galabar yaƙin Sumaliya sai da kai ɗokin Nijeriya.

    Hoton sojojin Nijeriya suna fareti

     

    Hoton sojojin Nijeriya suna fareti

     

    Gurguso rikici na cikin gida 'yan Biyafara sun tako ƙaya.

    Waiwaye a wajen mai taffiya, ai ado ne ba ni da tankiya.

    Mun ga yarda a kai zaki biyan, da kisan sojin Nijeriya.

    Mai tatsina da yac ci jihar Kano kan a ƙifta ya zama turɓaya.

     

    Duba Nija Dalta sansanin masu satar mai da akai jiya.

    Buratai na manjo jannaral shi ya daidaita masu taffiya.

    Yanzu laftanal janaral yake kuma hafsan soji mazan jiya.

    Masu ta da ƙaya ta hakurkura sun zamo tsuntsun nan mujiya.

     

    Ba sukuni inda ta zagaya ko a dangi koko a wariya.

    Ga mazan artabu da bindiga ga igwa nan ga kuma nakiya.

    Ga mijin hajiya Najeriya mai nagarta ba shi da karraya.

    Buhari janar lamba ɗaya mai gaba gaɗi zabgai kibbiya.

     

    Ga ko hafsan soja mazan jiya Buratai atafa koko ƙaya?

    Dabaibayi laushi ga cin ƙafa da lalama kake ko da hatsaniya.

    Bi su sannu Tukur baban Tukur ƙarangiya kwat taka ya jiya.

    Ƙasurgumi dodon ‘yan Zariya ina da ƙi gudu sa gudu ya tsaya.

     

    Mun yaba maku soja mazan jiya da addu'a da yabo duka na biya.

    Muna yaba maku soja mazan jiya gami da goyon baya bai ɗaya.

    Cikin birane har da su karkara ana du'a'i kan Nijeriya.

    Allah ka bamu zamanni lafiya cikin gida da wajen Nijeriya.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.