Manjo Janar Mustafa 1

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Sun buga sun bari manjo janar Mustafa,

    Masaba ƙarfen tama ba sa ga ƙarshenka ba.

    Ƙarfen tama kwangiri gamji ma sha sassabe,

    Manjo janar Mustafa ba sa ga ƙarshenka ba.

     

    Sunan abin dogaro Allahu Alƙadiri,

    Allahu Alƙadiri mai arzikin haƙƙuri,

    Mai sarrafar nan da can cikin dawa ko gari,

    Mubaya'ata duka ga annabi shugaba.

     

    Allah abin ambato a É“oye ko sarrari,

    Ƙaro aminci duka ga sayyidul bashari

    Abin yabon baÉ—ini abin yabon zahiri,

    Mai son mijin A’isha ba a ga Æ™arshensa ba.

     

    Rana idan ta fito sheda ta wayar gari,

    Da an fa waye gari sai dabdalar ‘yan gari,

    Fiton da kome nata ba mai hanawa gari,

    Ranar idan ta fito ba a hana a gan ta ba.

     

    Zubar ruwan maddari Buwayi Alƙadiri,

    Dukkan sha'an lammari yana kasan Ƙadiri,

    Komai nisan zamani yana gurin Ƙadiri.

    Abin da ya ƙaddara ba a ƙi a gan shi ba.

     

    Ga mai dashen kainuwa ta zam cikin bahari,

    In kun biye wa bado kwa sha ruwan bahari.

    Cin dudduge sa ƙwafa ba ya hanin zikkiri,

    Muna biÉ—ar taimako ba gun wanin Rabbu ba.

     

    Allah abin dogaro roƙo yake sha'iri,

    Ka san nufin zuciya da ƙuddurin sha'iri,

    Allah mafarkin da nai sanya ya zam nagari,

    Ka san nufin zuciya ba za mu É“oye ka ba.

     

    ÆŠoÉ—e ganin magauta da dukkanin fajiri,

    Allah kai masa kasshafi ya tsallake haÉ—ari,

    Tarkon haƙon magauta ya zamma ba tasiri,

    Da sun nufin za'ida ba za ta kai gunmu ba.

     

    Ka san dukan lamarin É“oyenmu har zahiri,

    Kasan ciki har waje da baÉ—ini zahiri,

    Babu abu na ɓoye akauni Alƙadiri,

    Sani na al'amari ba za mu ja makka ba.

     

    WaÉ—ansu sun É—au kube suna shirin bidiri,

    Gamji yawan sassaƙa ba ya hana ka tsiri,

    Jumrau mijin Fatima gwarzo abin fahari,

    Takubbunan akwasa ba za mu tsorata ba.

     

    Wanda ya kama Allah Buwayi Alƙadiri,

    Komai ya taso maka gaya wa Alƙadiri,

    Muddin hakan za ka yi ka kewaye haÉ—ari

    Kwaron gizago ba zai sanya ka tsoratta ba.

     

    Yabo nake Mustafa da gwargwadon hankali,

    Ba mai fahimtar abin sai ya zamo akili,

    Mai gwargwadon hankali da ya zamo adali,

    Shi za ya min uzzurin yabonka ba aibi ba.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.