Manjo Almusdafa 2

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Don bikin zuwa na gobe kan tanadin kuÉ—i,

    Ga dami irin na rumbu ga masu hankali.

    Ga yabon abin yabawa manjo AlmusÉ—afa,

    Tuna baya shi nake yi wa baitukan yabo.

     

    ShimfiÉ—a

    Ya wajabta in yaba wa wanda yai abin yabo,

    Gwadabe nake yabawa wanda ba kwazazzabo,

    Baituka kama da marka haka sukka zuzzubo,

    Jaruminmu yanzu sambal yake ba É—igon tabo,

    Mai farin hali kumurci agare su 'yan dabo,

    Maƙiyansa sun buga sun gaza yi masa tabo,

    Manufarsa kan matasa ba jidon É—ari kwabo,

    Kwarjininsa dagga Allah yake ba shi na dabo,

    Masanin sani na sannai rukuni tsubo-tsubo.

    Ilimi na dama ga hauni mai farin halin yabo,

    Rabbu amsa addu'ata a gare shi sha yabo.

     

    Wahidun abin yabo na yammaci da safiya,

    Tsarkake ka wajibina yammaci da safiya,

    Rukuni na bautata makka gwani guda É—aya,

    Ya abin kaɗaita bauta Allahu ƙwal! ɗaya.

     

    Ga yabon abin yabawa da riƙo da gaskiya,

    Mahabubu annabina da ya zo da gaskiya,

    Ali na haÉ—a sahabbai duka masu gaskiya,

    A yabon farin masoyi liman na anbiya,

     

    Kalamin na yau yana tsuwwar wasa 'yan maza,

    Godiya na yunƙuro zan yi wa uban maza,

    Da ya yo abin yabawa dole ne na kwarzaza,

    Namiji uban mazajen nan na gidan maza.

     

     

    Ba ni tsara baitukana su wuce ta rariya,

    In daka in tankaÉ—e su rairaya da rariya,

    Duka wanda kibbulata ta nufa da tsinkaya,

    Nutsu tsaf kawai ka kalla za ka tsinci gaskiya.

     

    Lamarin Ubangiji kaf! Ya yi manna izzina,

    Sai mu auna hankali ayoyi ta ko’ina,

    Kana ga dubun misalai ko ta ko ta ko’ina,

    Na abin da yakkasance daga bara har bana.

     

    Hamza yanzu nai nufin in yo wasu baituka,

    Nai nufin dakan daka shekar tsakiyar É—aka,

    Sanadin yabo na ƙauna wacce nake maka,

    Na haɗa gamida dace ƙaimi nake maka.

     

    Haihuwar garin Nguru Yobe state a nahiya,

    Hamza Mustafa a yau babu kamarsa nahiya,

    Gwargwdon iya sanina ne nikka inkiya,

    Da Arewa har Kudanci jumla gaba É—aya.

     

    Za ni in batu a kan kishin namijin maza,

    Kana in batu a kan ƙwazon zakkar maza,

    Kuma in batu a kan hidimar da ya wa maza,

    Ya'ani sadaukarwarsa a gidan maza.

     

    Da yawa suna yin soja a cikin ƙasa,

    Manufarsu su yi power ne a cikin ƙasa,

    Wasu ko kasa mu raba dukiyar ƙasa,

    Mustafa ko don hidimta wa kulliyar ƙasa.

     

    Ya fito second leutanant a acadamy,

    Ya wuce zuwa jihar Lagos babu ƙyanƙami,

    Hidimar ƙasa yat tafi ba darin gami,

    Rabbu taimaka wa Almustafa yai É—arin gami.

     

     

     

    Head Æ™urter ta interlegence a jihar Iko,

    Ya yi enternal affairs Lagos jihar Iko,

    Ya riƙa kusan sau biyu a jihar Iko,

    Yai a eaghty two diÉ“ision sau biyu a Ikko.

     

    Yai a Army Head Ƙurter hidimar Æ™asa,

    Haka a group security na cikin ƙasa,

    Martabarsa ta shahara har wajen ƙasa,

    Yai a head Æ™urter ta defence hidimar Æ™asa.

     

    Har ministry ta defence ya yi hiddima,

    Sai president hause ya yi hiddima,

    Na kira shi dumfama ja raggama,

    Haziƙi mijin Hafsatu ɗa ga Faɗima.

     

    ÆŠan Fatima ja ragama namijin maza,

    Uban Fatima ki gudu ne a gidan ma,

    Baban jenior sa gudu ne a gidan maza,

    Sannu sannu za mu ishe ƙudurin maza.

     

    Yau a nuna gogarma ɗaya kaf ƙasa,

    Wanda yay yi gogayyar sha'anin ƙasa,

    Ba tabo tabon illar da ya wa ƙasa,

    Sai dubun abin khairi da ya wa ƙasa.

     

    Da na ce damin rumbu Almustafa,

    Manufar a ɓoye take mabuga ƙasa,

    Manufar a shirye muke kishin ƙasa,

    Ma'anar a zaune take babu sa in sa.

     

    Wanda Rabbu yai ƙudurin zai zamo wani,

    Dole a jarabce shi da tsakwankwani,

    Zai ga ja'ibar maƙiya da kuna-kuni,

    Kwanci tashi za ya zamo sha'awar gani.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.