Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Nasara Burtai

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Mai gayya dole uwar na ƙi mai nasara Burtai,

Makasau dole a sara ma dodon mai zamba.

 

Shimfiɗa

Makasau ka cika aikinka,

Hafsa maza Burtai.

 

Jajirtau ka iya allonka,

Ga tarago Burtai.

 

Gogarma dole na gaisa ka,

Juya maza Burtai.

 

Mai tasau Allah ya kare ka,

Mai da gari kuffai.

 

Jagoran dole a hau doka,

So da ƙiya Burtai.

 

Tilasta massu su hau doka,

Ko da tsiya Burtai.

 

Ya Ahadun mai duka dafa min zan yabi mai gayya,

Assamadu kaurara harshena in faɗi gaskiya,

In yabi ɗan Yusufu gagona an yi kiɗan kurya,

Makasau dole uwar na ƙi mai saka ai zarya.

 

Na yi riƙon tsanin nan nawa annabi mai gayya,

Mai tsarki kuma ɗan tsarkaka babu halin gayya,

Don ƙauna da biyayyarsa sani a kan hanya,

Kar na bi limzamin harshena in yi ɓatan hanya.

 

Na ji gidan sa gudu mai gayya, shi aka nunawa,

Shi ko gidan ƙi gudu ya tashi babu shirin tsaiwa,

Mai takanas Bura uban Maryam je ka mu dafawa,

Babu gudu za mu bi bayanka ba wani gantsarwa.

 

Yau Buratai na saka rigarka inda ake sonka,

Dole a nan za su ji ƙaunata don fa muradinka,

To haka za inda ake ƙin ka na saka rigarka,

To haka za zan ji baƙar gaba na riƙi ƙaunarka.

 

Ni haka nan baya damuna na riƙe hujjata,

Tsahirta bi ni a hankalce don ka ji hujjata,

Ba ni gudun zunɗen mai ƙifce shi zai lalace,

Yay yi ɓatan surkullen bori don ya susuce.

 

Sanya gaba babu batun waige Allah na banka,

Ya hana zub da jinin bayinsa kac cika aikinka,

 Ay yi maza mazza akai ƙarshe ƙarshen aikinka,

Ya rage taku ɗai ingarma, je ka muna bin ka.

 

Wasu sun ɗau rikicin nan gona shi suka nomawa,

Wasu sun ɗau rikicin nan haja shi suka saidawa,

A sanadin zub da jinin bayi wai suka cashewa,

Su yi gida da ɗiyan mataye da kuɗin hutawa.

 

Jajirtau dole uwar na ƙi bar masu talala,

Kai masu anbush su bi shi nawa bar masu talala,

Ka ga tuwon dare ba ya daɗi a ci ana ƙwalla,

Masu raɗa bar ni da su baba zan masu bulala.

 

Sun manta Niger Deltar nan ni ban manta ba,

Sanda ka je gyaran aikin nan ba a ji da daɗi ba,

Yau kuma ga yaƙi ya faru bas su yi sulhun ba,

Jajirtau je ka ka turje su na farau ne ba.

 

 

 

Turawa na inkarinmu sun hana curewa,

Burinsu su haɗa kayinmu mui ta amon garwa,

Don in har mun haɗa kayinmu ba su da cashewa,

Za mu hana su haƙar mayinmu shi suka dubawa.

 

Ka ji dalili dukka Afurka an hana hutawa,

Ko ta ina za ka ji ba sauƙi ba matsugunnawa,

Ga Libya Cairo ga Mali Kyanya a jerawa,

Sauth Africa da Cadinmu na a cikin hurwa.

 

Turawa yau da Afurkawa mun zamto haja,

Don cinikayya ta makamansu mun ka zamo haja,

Ko cuta yanzu su ƙaga ta don mu zamo haja,

Don cinikin magungunnansu mu mu zamo harza.

 

Sun ƙi bari yau a Afrikanmu mu haɗa kayinmu,

Sun haɗa kai tarayyar Turai yuro da ke ƙin mu,

Asiya har latin Amurka mu ko a ware mu,

Har gobe mu ke goyon su mu bayi ne mu.

 

Yau rikici ya game Afirka yanken zauninmu,

Ga Sudan har an datsa ta don raba kayinmu,

Harsashe tun two thausand year za a rabe kanmu,

Kar mu bari ar raba tarayyar Nijeriyyarmu.

 

Makasau mai aikin gayya aikin na gunka,

Ko ka san hujjar zaɓen ka don tauraronka,

Ko ka san hujjar ɗora ka don yaba aikinka,

Ko ka san hujjar nassararka tsarkin niyyarka.

 

Ga kayan aiki nan baba, ba mai toshe ka,

Ga A. A anti air crapt sashen ikonka,

Ga M. Rap motar yaƙin nan anti bom taka,

Ga genaral popuse mechine gun GPMGN ka.

 

Ga shilka amo tanker ce don amo na nan,

G. 16 ga RPG nan rapid gun na nan,

Thirty siɗ angurnet na nan ga AK na nan,

Saggy mota mai kaccar nan sai yaya ke nan?

 

Sojojin Nijeriyyata sai yaya ke nan?

Ga aiki ga kayan aiki sai mene ke nan?

Ko kuma dai mui hijira ne wai in har ba kwa nan?

Me ya rage mu aka saurare ga kowa na nan.

 

Kar ku bari yanzu a datsa mu za mu zamo shara,

Kar ku bari yanzu keta mu za mu zamo saura,

Na ga wasu na haɗa kayansu don tsoron bara,

Ga Tukuro Yisufu mai gayya ba tsoron bara.

 

Natral Counter of Terrorisim Special Forses,

TRA Shool Buniyard Yobe state na nan.

 

Natral Counter of Terrorisim kwamandan baiwa,

Brigadia genaral Folonintro galla maza na nan,

 

Tweenty Two Amo Brigadia, komandan na nan,

Brigadia genaral Bosoya wallah maza na nan.

 

Chief. Instructer Col. Enjike ga ni da waƙa ta,

Co 3 Baterlion L.T Col. Imoke ne.

Lieutenant General Yusuf Tukur Burutai (Nigerian Chief of Army Staff)

 

Lieutenant General Yusuf Tukur Burutai (Nigerian Chief of Army Staff)

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments