Kara Hakkuri Buratai

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Ƙara haƙƙuri Buratai hassada ta zam taki,

    Ƙara godiyar maiduka ba a fara komai ba.

     

    Lafiya mazan tafiya je ka dai mazan fama,

    Ka zamo masaba ta maza makare al'umma,

    TunkuÉ—a iza ka ake hassadar da kan yi ma,

    HaÉ—ari gusa ka matsa babu shamaki a yi ma,

     

    Korami gidan kaluma sauƙi ga mai nema,

    Bar takubbunan akwasa ba abin da tay yi ma,

    Sassaƙa da saranka ɗaukaka suke ja ma,

    Kainuwa dashen Allah mattsala ta mai koma.

     

    Hadarin ƙasa kabido babu mai iya ya yi ma,

    Bahari ruwan teku ka gaji da al'uma,

    Buratai fagenka kake babu mai ja ma,

    Ɗauki ja baƙi ka fasa mu kawai muna bi ma.

     

    Ga imamu ya nisa mamun suna bi ma,

    Jama'a suna barka addu'a suke yi ma,

    Maƙiya suna kuka ƙazafi suke yi ma,

    Malamai suna adu'a al- kunut suna yi ma.

     

    Maƙiya suna zunɗe hasada suke yi ma,

    Dakata kaÉ—an ka jiya duk abin da yaj ja ma,

    Gaskiya kawai ka riƙe ita ta kai ka taj ja ma,

    Masu ƙin ka don hasada Rabbu za ya kare ma.

     

    Ka yi mantuwa TY Burratai in shaida ma,

    Mattsayin da kat taka É—aukaka yake ja ma,

    Hakkanan uban tafiya takala yake ja ma,

    Duk maƙi ganin nasara hassada yake yi ma.

     

     

    Adamawa ‘yan Mubi tutar mazan fama,

    Adamawa Munchika tutar mazan fama,

    Adamawa Madagali tutar mazan fama,

    Mu matsa jihar Yobe tutar mazan fama,

    Yobe Jajimaji duka tutar mazan fama,

    Yobe garin Macina tutar mazan fama,

    Tuta ta Nijeriya na nan na kaÉ—awa,

     

    Yobe garin Gujiba tutar mazan fama,

    Yobe garin Buniyard tutar su dumfama,

    Yobe a Bunigari tutar su dumfama,

    Yobe a Dammaturu tutar su dumfama,

    Yobe garin Gaidam tutar su dumfama,

    Sai sansanin yaƙin filin mazam fama,

    Tuta ta Nijeriya na nan na kaÉ—awa.

     

    Yanƙin jihar Borno Meduggurin fama,

    Borno a Kwandigga tutar mazan fama,

    Barno cikin Bama tutar mazan fama

    Borno garin Goza tutar mazan fama

    Wulasa da Wulari tutar mazan fama,

    Gambori ga Abadan tutar mazan fama.

     

    Alagarno Alabargi tutar mzan fama,

    Kukawa ga Duguri tutar mazan fama,

    Bagadaza ga Dikwa tutar mazan fama,

    Dogonchukun Kaukini tutar mzan fama,

    Malimbe Madari tutar mazan fama,

    Mari da Marte Shuwa tutar mzan fama.

     

    Gajibo da banki kuma tutar mazan fama,

    Markobina ma Hakaza tutar mazan fama,

    Doron nera hakaza tutar mazan fama,

    Borno garin Maitale tutar mazan fama,

    Har an ci an kare Rikicin mazan fama,

    Yau ya rage kale kuma duk suna koma.

     

    A abin da yai saura rikicin mazan fama,

    Damasak da Alagarno ya rage ake fama,

    A haÉ—a cukon Guzo ya rage fagen fama,

    Tantagarya Sambisa a cikin fagen fama,

    Har an ci an Æ™are Æ™arshe na ‘yan nema,

    Leutanant genar Buratai na kira ka dumfama.

     

    Fildimashal É—an Buratai ya rage Neja Delta,

    Tsittsigen rashin kunya ɓurɓushin Niger Delta,

    'Yan ta da ƙayar baya da suke ta kunna wuta,

    Addu'a muna yi ma nasara ta kasshe wuta.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.