7.29 Sharu Sulaimanu Jadda - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 378)

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    A gaida Sharu Sulaimanu Jadda jinin ma’aiki.

    A gaida Sharu Sulaimanu Jadda jinin ma’aiki.

     

    Allah Ahadin Saraki,

    Lamyalidi a mulki,

    Baida Kini Saraki.

    Allahu Ubangijin Ka’aba Sarkin Saraki,

    Allahu Ubangijin Harramai na haɗa Shabbaki.

     

    Allahu amintakarKa daɗa ta gurin ma’aiki,

    Ƙaribu mafi kusanKa ka mai matsayin ma’aiki,

    Amadu madogarar masu bin Ka gami da aiki,

    Auwal shugaban talikan farko ƙarshe ma’aiki.

     

    Ina zaune wataran cikin shu’uni na aiki,

    Kun san ni da sabgogi gida da waje da aiki,

    Wayoyina wata na amo wata na a baki,

    Wasu ma n ace min agogo uba na aiki.

     

    Na hango Mahiru na ta faman motsa baki,

    Yana ta ahi cikin zaƙƙuwa har ma da ɗoki,

    Ganinsa da nai yana mai bisharar gama aiki,

    Ashe saƙo ya kawo na Jadda jinin ma’aiki.

     

    Ya ce mani ALA inji Sharu jikan ma’aiki,

    Saƙo aka ban in faɗa maka baki da baki,

    In kai ka ka gana ka yi sirri da shi a ɗaki,

    Na ce masa mai yake so in ba shi jinin ma’aiki.

    Mahiru yac ce Allahu a’alam sai ma’aiki,

    Abin da kaɗai na sani in kai ka gurin shaƙiƙi,

    Ina ka yarda mu tafi ƙafarmu ƙanwa ta baki,

    In kai ka gurin Sulaimanu Jadda jinin ma’aiki.

     

     

    Mahirru wayarsa gare ni ta fi faɗi da baki,

    Sannan fa wayassa gare ni ta fi faɗo da baki,

    Muridi ya fusata ya je ga jinin ma’aiki,

    Ya ce da Sharu ka manta da ALA sani aiki.

     

    Ya ce da Sharu idan sarauta ce ka ga sarki,

    Idan a batun muƙami fa Cif Jostis shaƙiƙi,

    Sannan daga nan har Asorok ba a ma shamaki,

    A ƙyale batun daraja jininka jinin ma’aiki.

     

    Idan fa batun waƙa ake da akwai shariƙi,

    Akwai Sadi Musbahu sun fi amonsa zaƙi,

    Akwai su Mudassiru zalaƙa ce a aiki,

    Rabbu da shi maulaya naimi wani shaƙiƙi.

     

    Bara ka ji jikan Annabi da halin ma’aiki,

    Ka san haƙuri babbar ɗabi’a gun ma’aiki,

    Da alƙawari da riƙon amana sai ma’aiki,

    A gaida Sharu Sulaimanu Jadda jinin ma’aiki.

     

    Na sake tarar shi amo kira baki da baki,

    Da Mahiru ko ya saman rabo na gamo na kirki,

    Na je ga Sharu Sulaimanu mai koyin ma’aiki.

     

    Na iske guri danƙam jama’a kowa da ɗoki,

    Sharu a ciki yana bi-da-bi jama’ar ma’aiki,

    Gaba da gabanta aljan ya damƙi wutar lantarki,

    Na sami guri ina zaggwaɗi na ganin shaƙiƙi.

     

    Da kansa Sharu ya tarbe ni mun ka shige a ɗaki,

    Mu kai sirrinmu da shi da ba shi faɗo da baki,

    Na ga abin a faɗa a samu yabo na baki,

    Na ga abin a yaba gare shi jinin ma’aiki.

     

     

     

     

    Sharu ma’abocin kwarjini tamkar saraki,

    Sharu mutafannoni a addinin ma’aiki,

    Sharu mawadacin malami ba cikka baki,

    Baiwa ta Ubangiji ya ajewa jinin ma’aiki.

     

    5 Sharu addu’ar da kake mani baki da baki,

    Ka ban ita in riƙe dafa’an babu miki,

    A yanzu magauta sun tusa ni da soke-soki,

    Ka ban dafa’i na riƙe shi Jadda jinin ma’aiki.

     

    Sharu Ahalan bika ya jinin Fatin ma’aiki,

    Jini na Hasan da Usaini jikokin ma’aiki,

    Ɗiya na Aliyu jarumi hamshaƙin sadauki,

    Mun kama ƙafa da ƙaunarku jinsiyar ma’aiki.

     

    Allah ka tsare mu shiga kadarkon nan na maƙi,

    Ka sanya mahassadana su zamma kama da gunki,

    Fagen fikira ka mai da su tamkar da jaki,

    In zam a samansu kullum suna kuwa da ɗoki.

     

    Allah Ahadin Samadi duk sanda na buɗe baki,

    Sunanka na sa a farko da zan yi yabon shaƙiƙi,

    Na zo ƙarshe murfinta sunanKa Saraki,

    Tamat na rufe da sunanKa Jalla wa Azza Sarki.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.