Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
Malam Amadu mai Rauhani,
Malam Amadu mai Rauhani.
Kun ji gamon ALA mai waƙa,
Da malam Amadu mai Rauhani.
Na naimi tsari gun Sarki Allah,
Da a kai ni shaiɗani zamani.
Tsare ni tsarewa Ya Allahu,
Raba ni na fi ƙarfin duk shaiɗani.
Ka ba ni wadatar zuci Allah,
Ka sa na fi ƙarfin duk shaiɗani.
Ya Allahu Ya Ƙayyumu,
Na yi tawassili da Ƙur’ani.
Malam Amadu mai Rauhani,
Malam Amadu mai Rauhani.
Kun ji gamon ALA mai waƙa,
Da malam Amadu mai Rauhani.
Ka ƙara daɗin tsira Ya Allah,
Ga Amadu Mamudu bawan Allah.
Manzon baiwa ɗan Abdullah,
Muhammadu mai kwana yin sallah.
Tsira da aminci ya Allah,
Da ALA yai masa bawan Allah.
Haɗa asahabi ya Allah,
Abin koyin bayinKa Allah.
Ranar Juma’a bayan almuru,
Ina Hikima Midiya al’uma.
Sai ga mota ta alfarma,
Yai fakin da direba mai kima.
Ya zo shi siyan kaset a Hikkima,
Ya ce wai ina Alan al’umma.
Na ce masa ni ne Alan waƙa,
Yai mamaki kirar hamma.
Malam Amadu mai Rauhani,
Malam Amadu mai Rauhani.
Kun ji gamon ALA mai waƙa,
Da malam Amadu mai Rauhani.
Ya ce mini ALA ka birge ni,
Da kai waƙar sarki mai girma.
Sarki Ado ɗan Bayero,
Mai taimako gurin al’umma.
Ya ɗauko alkhairi ya ba ni,
Ya ce tukuici don alfarma.
Albarkacin Ado Bayero,
Da kaw wasa shi cikin al’umma.
Mu kai canjin lambar waya,
Mu kai bankwana da mai Rauhani.
Washegari da sanyin safe,
Za shi Abuja mai Raunahi.
Malam Amadu mai Rauhani,
Malam Amadu mai Rauhani.
Kun ji gamon ALA mai waƙa,
Da malam Amadu mai Rauhani.
Ya zo muka tattauna ni da shi,
Na ce masa mai ma’anar Rauhani.
Ya ce mini aiki ne ya saka,
Ake mini inkiya Rauhani.
Ni na ga abin ai ban mamaki,
Da malam Amadu mai Rauhani.
Na ga abin zam ban al’ajab,
Da malam Amadu mai Rauhani.
Kuma na ga karamar wannan ƙarni,
Da malam Amadu mai Rauhani.
Ya ƙasaita ya gawurta,
Ya tumbatsa mai Rauhani.
Ya ba ni du’a’i ya lazumta,
Ya ce dafa’an mai Rauhani.
Ya ce mani sharrin ɗan Adam,
Da aljan ka kere a zamani.
Ya ce mani kar kai hassada,
Ga kowa ko ƙyashi a zamani.
Ashe malam babban gwarzo ne,
A fanning karatun Alƙur’ani.
Malam Amadu mai Rauhani,
Malam Amadu mai Rauhani.
Kun ji gamon ALA mai waƙa,
Da malam Amadu mai Rauhani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.