7.32 Uwar Iyaye A'isha - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 386)

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Uwar iyaye A'isha Aminu ba za ya bar ki ba,

    Uwar iyayeA'isha Aminu ba za na bar ki ba.

     

    Wanda rana ta sa ya sha, wahala yat taho ya sha,

    Inuwa gun ki A'isha, tarbiya gun ki A'isha,

    A’i mai ban ruwa na sha, na taho don na kuma sha,

    Ya mashaya ta masu sha, ban in shassha A'isha,

    A’i mai ban ruwa na sha, uwar iyaye A'isha.

     

    Inuwa mai kore zuffa Nana, rumfa mai kore rana,

    Nana haske mai kore duhu Nana, uwa abar yabona,

    Nana hanyar sada zamunta Nana, hasken duhun gabana,

    Batu na ƙaunar uwa da ɗanta Nana, kin fi gaban a tona,

    Nana sai dai a zo da koyi Nana, don a yi kwas ganina.

     

    Ba ni mantawa da raino, A'isha da ki kai a guna,

    Har na kai yaye a gunki, ina shagwaɓa da kaina,

    Har na yi ƙuruci dangin hauka na yara ƙanana,

    Ba ki ƙosawa da ni kuma har na yo miki ɓarna,

    Tsokana in na yo gare ki zan gudo na kwana.

     

    Duk tunani na mai tunani ya gaza da sanin laƙanina,

    Laƙanina tarbiya ƙarƙashin koyarwa ga Nana,

    Dafa’ina biyayyar ɗafa ga A’isha Bintu Nana,

    Darajata da martabata kaffa-kaffa uwa a guna,

    Falalata tarairayarta da ba ta haƙƙoƙinta da kaina.

     

    Abin da ƙauna za ta bayar shi biyayya za ta ta bayar,

    Abin da ƙwaƙƙwalwa ta bayar shi tunani za ya bayar,

    Abin da tunnani ya bayar shi fa aiki za shi ya bayar,

    Abin da aiki za shi ya bayar shi ɗabi'a za ta gabatar,

    Abin da halayya ta bayar shi siffofinka za su bayar.

     

    Abin da ruhim mutum ya auno shi gaɓoɓi za su gabatar,

    Abin da son zuciya ya auno shi take son ka ka amayar,

    Aiki da son zuciya mu gano yin sa da na sani ka bayar,

    Aiki a kan hankali mu gano salsalar gaskiya ka bayar.

    Abin da tuntuntuni ka auno shi natijarka za ta bayar.

     

    Wasu na san za su ce wa Aminu kewa baituka hakan nan,

    Ce da su masharar hawaye uwar iyaye Nana ɗin nan,

    Ce da su gatan marayu yara-yara ƙanana ɗin nan,

    Ce da su farar uwan nan A’i Nana muminan nan,

    Ce da su abar ɗafewa a samu Aljannatun nan.

     

    Baki san kukana ko ƙyas haka A’i a kan sanina,

    Ko’ina za ki da ni kike tafiya a dare da rana,

    Nai ƙawa-zuci da ke A'isha uwa Aisha ubana,

    Mutuwa mai gincire shaƙuwar uwa har da so da ƙauna,

    Ga shi na zamo hadimi na uwa a gun wasu a sanina.

     

    Uwar iyaye A'isha, Aminu ba za ya bar ki ba.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.